*KARYAR KU ‘YAN SHI’I ASIRIN KU YA TONU*

*KARYAR KU ‘YAN SHI’I ASIRIN KU YA
TONU*

Tareda:- *Sheikh Muhammad Kabiru
Haruna Gombe {Hafizahullah}*

Wannan Shine Muhadarar da Malam
Yagabatar Jiya a Masallachin Sultan Bello dake nan Cikin Garin Kaduna.
Danna link dake kasa domin downloading
wannan Karatu

http://darulfikr.com/s/53342

*Domin Samun Video Na Karatun Malam
Sunnah Daban-Daban kuyi
Subscribe din *Channel* Din *Mu* http://www.Youtube.com/SunnahNewsNigeriaTv
KARYAR KU ‘YAN SHI

IZALA KADUNA ZATAYI WA’AZI A GARIN DOKAN TAGWAI, KUBAU LG

*WA’AZI.! WA’AZI.!! WA’AZI.!!!*
A Madadin Kungiyar Jama’atu Izaltil
Bid’ah Wa’iqamatis-Sunnah reshen Jihar
Kaduna Karkashin Jagorancin
Shuwagabannin Kungiyar ta Jiha
– Alhaji Muhammad Tukur Isa (Shugaban Kungiya ta Jiha)
– Sheikh Aliyu Telex
(Shugaban Majlisar Malamai ta Jiha)
– Mallam Adamu Ibrahim
( Daraktan ‘Yan Agaji ta Jiha)
Suke Gayyatar Al’ummar Musulmi Ahlus- sunnah Wal-jama’ah Zuwa Wurin
Gagarumin Wa’azin Kungiyar Izala ta
Jiha Wanda ta shirya zai gudana kamar
haka;
*- Gari; *Dokan Tagwai, Kubau LG,
Kaduna State*
*-Rana;* Asabar/Lahadi 28-29 Rajab 1439, 14-15 April
2018*
*MALAMAI MASU WA’AZI*
Ana Saran Halartan Manyan Malamai Da Alarammomi Da Zasu Yi Wa’azi Kamar Haka;

– Sheikh Aliyu Abdullahi Telex
– Sheikh Dr. Yusuf Ibrahim Kubau – Sheikh Muhammad Jamil Abubakar
Albani
– Sheikh Usman Saleh
– Sheikh Nasiru Yusuf Khidir
– Imam Aminu Ramin Kura
– Imam Khidir Manufa – Mallam Muhammad Kabiru Idris Kauru
– Mallam Isa Nasir Birnin Gwari
– Mallam Muhammad Nura Mujahid
– Mallam Muhammad Nazifi Hashim
– Mallam Musa Ibrahim (Alkali)
– Mallam Muhammad Auwal Adam Kudan – Mallam Salihu Muhammad Adam
– Mallam Bashir Sulaiman Gazara
– Mallam Aminu Kabiru Makarfi
– Mallam Salisu Makarfi
*ALLARAMMOMI*
– Alaramma Salisu Ung. Kanawa – Alaramma Ridwan Pambegua
– Alaramma Shu’aibu Usman Zuntu
– Alaramma Abdullahi Lawal Makarfi
– Alaramma Yusuf Ibrahim Meyere
*MASU GAYYATA*
1- Sheikh Yusuf Ibrahim Kubau (Mataimakin Shugaban Majalissar Malamai Na Jiha)
2- Malam Habib Idris Anchau (Shugaban Jibwis kubau LG)
_*Sanarwa Daga Shugaban Kungiya Izala Na Karamar Hukumar Kubau, Malam Habib Idris Anchau*
_*Abubakar Nuhu Yahya Koso #IbnNuhAssunnee*_
_*V.Chairman Jibwis Social Media Kubau LG*_
*27 Rajab 1439*
*12 April 2018*

007 HUKUNCE – HUKUNCEN JANAZA A SAWQAQE

TAKARDA TA FARKO {1} WANKA DA ABUBUWAN DA KE DA ALAQA
DA SHI DARASI NA UKU {7} YADDA AKE YIN WANKA BIYAR {5} KO
FIYE DA HAKA Idan ya kasance wanka biyar ko bakwai ko
tara za ayi to wanka na biyu {2} wato wankan
magarya shi za aita maimaitawa. Amma dole
ya zama sai ya zama na kafur da turare. MISALIN YADDA ZA AYI WANKAN SAU
BIYAR *1-* Na farko shine na tsarki.
*2-* Na biyu soso da magarya.
*3-* Na uku shima soso da magarya.
*4-* Na hudu shima haka.
*5-* Na biyar kuma sai ayi amfani da kafur da
turare. Allahu a’alam KAMMALAWA Daga karshe muna gode ma Allah daya bamu
ikon gama wannan dan takaitaccen rubutu
akan wankan gawa wanda ba dabarar mu
bace ba don muna da ilimi mai yawa ba.
Amfaninsa shine ko wannenmu ya iya, ta
yadda ko wane gida za su rika yi ma ‘yan uwansu.
Ina rokon Allah ya azurta mu ni da ku
kyakkyawar cikawa. Allah shine mafi sani. Rubutawar:
Yusuf Lawal Yusuf
(Abu Ja’@far) Mai nazari:
Mal. Basheer Lawal Muhammad Zaria.
(Abu Sumayyah) 1st Rabi al-Akhar 1439AH.
19th December, 2017.

006 HUKUNCE – HUKUNCEN JANAZA A SAWQAQE

TAKARDA TA FARKO {1} WANKA DA ABUBUWAN DA KE DA ALAQA
DA SHI DARASI NA UKU {6} YADDA AKE WANKA SAU UKU {3} Da farko idan masu yiwa mamaci wanka sun
zabi suyi masa wanka sau uku, to bayan sun
gama abubuwan sama saisu fara wankan. Da
farko dai zasu tanadi ruwa kashi uku {3} domin
wankan. Ko wani ruwa za ayi wanka daya
dashi. WANKA NA FARKO: Yi masa tsarki:
Ana bukata yayin yi masa tsarki a sa safar
hannu.
Kawar da najasar bayan yi masa tsarki.
Al’wala irin al’walar sallah.
Wanke kai sau uku. Wanke bangaren jiki na dama.
Wanke bangaren jiki na hagu.
Wanke dukkan jikinsa. WANKA NA BIYU: Za a zuba Magarya mai kumfa ko sabulu.
Soso inda bukata.
Wanke dukkan jikinsa da ruwan. WANKA NA UKU: Za a zuba Kafur da turare mai qamshi a cikin
ruwan.
Wanke dukkan jikinsa da ruwan Allah shine mafi sani. Rubutawar:
Yusuf Lawal Yusuf
(Abu Ja’@far) Mai nazari:
Mal. Basheer Lawal Muhammad Zaria.
(Abu Sumayyah) 29th Rabi al-Awwal 1439AH.
18th December, 2017. Daga: ZAUREN MAL. BASHEER LAWAL
MUHAMMAD.

005 HUKUNCE – HUKUNCEN JANAZA A SAWQAQE

TAKARDA TA FARKO {1} WANKA DA ABUBUWAN DA KE DA ALAQA
DA SHI DARASI NA UKU {5} ABUBUWAN DA AKE TANADA DON
WANKAN GAWA:- Kafur.
Turare.
Safar hannu.
Magarya. dakakkiya {garin magarya} ko
sabulu.
Ruwa mai tsarki kuma matsakaici tsakanin sanyi da zafi. YADDA AKE YIN WANKAN GAWA:- Ana yin wankan gawa mara-mara ne misali:
Sau uku {3} ko
Biyar {5} ko
Bakwai {7} ko
Tara {9}. Hakan ya tabbata daga Manzon Allah {S.A.W}
acikin hadisin ummu Adiyyah {R.A} Wadanda
za su yiwa mamaci wanka su zasu yi la’akari
suga wanka nawa ya dace masa. Da farko dai kafin a fara wankan da akwai
abubuwa guda uku {3} da za a fara yi wa
mamacin.
1- A cire masa tufafin da ke jikinsa in ba a riga
an cire ba a lokacin da ya rasu. 2- Matsa cikinsa domin kazantar da ke cikin
cikinsa ya fita. 3- A yi masa tsarki, na bangaren mafita biyu
{bawali da bayan gida}. 4- Idan macece, za a tsefe kitson da yake
kanta, a wanke kan, sannan ayi lallabi uku a
kan {wato kalba guda uku} sai a kwantar da
kalbar tayi bayan kan nata, idan namiji mai
kitso ne sai a warware kitson gaba daya. Allah shine mafi sani. Rubutawar:
Yusuf Lawal Yusuf
(Abu Ja’@far) Mai nazari:
Mal. Basheer Lawal Muhammad Zaria.
(Abu Sumayyah) 28th Rabi al-Awwal 1439AH.
17th December, 2017. Daga: ZAUREN MAL.BASHEER LAWAL
MUHAMMAD.

004 HUKUNCE – HUKUNCEN JANAZA A SAWQAQE

TAKARDA TA FARKO {1} WANKA DA ABUBUWAN DA KE DA ALAQA
DA SHI DARASI NA UKU {4} FALALAR WANKAN GAWA:- Al-Imam Hakim ya ruwaito hadisi wanda
Manzon Allah {S.A.W} yake cewa“Duk wanda
ya wanke mamaci, kuma ya rufa masa asiri,
Allah zai gafarta masa sau arba’in”. Kuma a
wani hadisin Manzon Allah {S.A.W} ya ce “Duk
wanda ya wanke mamaci, kuma ya rufa masa asiri, to Allah zai tufatar da shi daga cikin
tufafin gidan al-jannah. SIFFOFIN MAI WANKAN GAWA:- Daga cikin siffofin mai wankan gawa ya
kasance:- 1- Mai ikhlasi {Yi don Allah}. 2- Daga cikin makusantan sa misali: iyaye,
kanne ko yayye, ‘ya ‘yansa da sauransu, in ya
yuwu. 3- Maza su wanke maza, suma mata su
wanke mata {sai dai miji zai iya wanke
matarsa haka ma mace zata iya wanke
mijinta}. 4- Mai rufa asiri {wato kada ya yada abin da ya
gani mara kyau daga gawa}. Allah shine mafi sani. Rubutawar:
Yusuf Lawal Yusuf
(Abu Ja’@far) Mai nazari:
Mal. Basheer Lawal Muhammad Zaria.
(Abu Sumayyah) 27th Rabi al-Awwal 1439AH.
16th December, 2017. Daga: ZAUREN MAL. BASHEER LAWAL
MUHAMMAD.

003 HUKUNCE – HUKUNCEN JANAZA A SAWQAQE

TAKARDA TA FARKO {1} WANKA DA ABUBUWAN DA KE DA ALAQA
DA SHI DARASI NA UKU {3} HUKUNCIN WANKAN GAWA:- Lallai musulmi idan ya rasu wajibi ne akan
mutane dasu yi gaggawar wankesa saboda
hadisin Manzon Allah (S.A.W) “Ku gaggauta
kai mamaci; domin idan gawar ta gari ce, to ga
alkhairi zaku sadar da ita, idan kuma bata gari
ba ce, to za ku sauke sharri daga wuyayenku”. Bukhari da Muslim Kuma abu ne sananne umurni ana daukarsa a
matsayin wajibi. Amma wajabcin wanka dalili
shine saboda hadisin Manzon Allah (S.A.W)
da yace game da ‘yarsa Zainab (R.A) “Ku
mata wanka sau uku, ko biyar, ko bakwai, ko
sama da haka in kunga haka”. Bukhari da Muslim.
Saboda haka jamhoran malaman fiqhu suka
tafi akan cewa wanke mamaci wajibine a kan
dukkan musulmai har sai an sami wadanda su
kai masa. Allah shine mafi sani. Rubutawar:
Yusuf Lawal Yusuf
(Abu Ja’@far) Mai nazari:
Mal. Basheer Lawal Muhammad Zaria.
(Abu Sumayyah) 26th Rabi al-Awwal 1439AH.
15th December, 2017. Daga: ZAUREN MAL. BASHEER LAWAL
MUHAMMAD.