RAYUWA DA MUTUWA MALAMAI UKU NA SUNNAH – (1) SHEIKH ABUBAKAR MAHMUD GUMI, SHEIKH JAFAR MAHMUD ADAM DA SHEIKH MUHAMMAD AUWAL ALBANI ZARIYA (ALLAH YA KARBI SHAHADARSU AMIN

DARASI NA DAYA (1) Na ga yadda mutane dubunnai suka yi dafifi a wurin jana’izar Sheikh Albani Zaria amma cikin ikon Allah mutane ba wanda ya ke fadin wata magana ta karama ko mafarkin ya ganshi yana gyara wurin da zai sauki manzon Allah. Duk da shedawar da jama’a suka yi na kalmar Shaha da wadannan malamai suka yi a bayyane ba bu wanda ya ba daya daga cikinsu
da aka baiwa wasika ya ce ya kai wa Allah, domin Ahalussunnah ba su san ana haka ba. Abin da zai baka sha’awa a wurin jana’izarsu, babu wanda ya je da gudu ya ce bari ya shafi tabarraki na wannna bawa Allah ballantana wanda ya shafi gawarsa shima a taba shi. Ka duba irin littatafi masu yawa da ko su kansu wadannan malamai ba za su iya fada maka adadinsu ba da suka karantar tun daga bango zuwa bango amma kuma hakan bai sa an zo ana karanta wani baiti ko waka ba a bakin kabarinsu. Mutane ne daga ko’ina su ke ta turowa daga wurare daban-daban domin har zuwa wannan lokaci da muke ciki baki sai shigowa suke yi domin su sami yi masa sallah, da zarar mutum ya zo ya ji ance an gama yi masa sallah wasu su yi addu’a wasu kuma ku je bakin kabarin su
yi ta su addu’ar. Wannan shi ne karantarwa da Sheikh Abubakar Mahmud Gumi da Sheikh Jafar Mahmud Adam da Malam Albani suka tafi a a kanta, kuma ita ce tafiyar da manyam malam sunnan su ke kanta. Duk wani mutum da ya mutu a malaman Sunnah ana ambatonsa ne kawai a irin ayyuka da ya yi. Tun daga lokacin da aka ce Sheikh Abubakar Mahmud Gumi ya rasu, babu wata rana da zata fito ta koma face anyi masa addu’a kuma an kwankwadi ilimi, ya mutu kamar bai mutu ba. A kowane lokaci da safe da rana da yamma idan a wancan garin ba aji karatunsa ba, to za dauki littafansa a karanta. Amma duk da wannan irin gudunmuwa da Malam ya bada babu wani daga cikin ahlussunnah da ya taba yin ikrari cewar Malam yana al’jannah sai dai kullum mu na masa fatan yana aljannah. Wani abin jin dadi ma shi ne ba wanda ya taba tunanin ya ce dole sai ya ziyarci kabarinsa ballantana ya nemi ya bashi wani abu na karama, ko neman gafara daga gare shi. Da za ka tambayi wani ahlussunnah a ina kabarin Shiekh Abubakar Mahmud Gumi ya ke zaka sa mu kasha 75% ba su sani ba. Sheikh Abubakar Mahmud Gumi bai taba nunawa wani darajarsa ba, bai taba cewar wani ya bishi ba, bai taba nunuwa wani cewar shi waliyi ba ne, amma kuma ka duba yadda Allah ya tabbatar da daukakarsa da darajarsa da kuma girmansa, wanda yaran da aka haife su a shekarar da Malam ya rasu yanzu wasu daga cikinsu suna jami’a. Amma da yawansu za su ce maka suna ganin yana raye bai mutu ba. Mene ne dalilinsu saboda suna tare da iliminsa da koyarwarsa a kowane lokaci. Yadda za ka ga ne cewar Allah ya daukaka darajar malam, shi ne darajar iliminsa da Allah ya daukaka, a lokacin da malam ya ke da rai bai taba nuna ya fi kowa ilimi ba, hasalima ya kan nuna wadansu malamai ya nuna cewar su masu ilimi ne. Hakan ya sanya wadansu da suke jin yana fadin cewar su malamai ne su ke ganin cewar sun fishi ilimi. Tawadi’unsa da kuma komawarsa zuwa ga Allah ya sanya Allah yayi wa ilimisa albarka, ya
kasance akwai malamai da suka yi zamani da shi, wadanda suka ma koyar da shi, da wadanda suke ta yi karaji a masallatai idan watan ramala ya tsaya amma kamar anyi ruwa an dauke. Wasu daga cikinsu ma suna nan a raye amma kuma kamar sun mutu. Shi yasa Khalifan Manzon Allah SAW Umar dan Kaddab ya ce “Mu wadansu mutane ne da Allah ya daukaka mu da musulunci, duk lokacin da muka ne mi wata daukaka ba ta wannan hanyarba Allah zai kaskantar da mu da ita”. Malam bai ne mi daukaka a wurin kowa sai Allah, ya daraja Sahabai da Iyalan manzon Allah, ya ba su hakkinsu kamar yadda shi manzon Allah ya ba su, bai yi shisshigi ba bai yi jafa’i ba. Duk abin da ka ji daga wurin Sheikh Abubakar Mahmud Gumi ya na nan a cikin littafai na farko. Allah ya gafarta masa ya kautata na mu

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s