MENENE MANUFAR GWABNATIN NIGERIA KARKASHIN JAM’IYAR APC?

MENENE MANUFAR GWABNATIN NIGERIA KARKASHIN JAM'IYAR APC?

Nasan xaka iya cewa meyasa nayi wannan tambayar saboda 'yan nigeria muna kyautata xaton cewa #apc gyara sukaxo aiki zasuyi wa kasa ba sace dukiyar kasaba, ba kuma sharholiya sukazoba sai dai kuma alamu nanu cewa akwai matsala, don me nace haka biyoni xuwa karken rubutuna.
A dai-dai wannan lokacin kasarmu #NIGERIA na cikin wani wadanda sukamata gwabnatin ta duba kuma tayi nazari akansu misali.
A. Ragargar da yan boko haram sakayi na kashe al'umma babu dalili.
B. Halin da 'yan gudun hijira ke ciki duk da cewa babu iyalan shugaban kasa, gwaba ko wani dan majissar dattawa ko na wakilai.
C. Barnar da gwannatin baya tayi a wawure asusun kasar.
D. Tsadar man fetur da har yanxu ba'a gama warke daga cikinsaba.
E. Durkushewar tattalin arzikin kasa.
F. Matsanancin talauci.
G. Sannan ga uwa uba, rashin aikinyi ga al'ummar kasar.

Amma kash wai muna cikin wannan yanayin kwatsam sai naji a kafar yada labarai cewa taro da ake gudanarwa a kaduna na bikin #makada #mawaka #yan_duniya wanda aka shirya domin #sharholiya bayan kiranda malamai sukayi kamar haka:-

Shugaban majalisar
Sheik Usman Abubakar
Baban Tune shi ya yi
wannan Allah wadai,
lokacin da yake gabatar
da hudubar juma'a a
Masallacin NNPC Kaduna.
Sheik Baban Tune ya
kara da cewar, El Rufa'i
ya tozarta kuri'un
jama'ar jihar Kaduna,
wadanda suka zabe shi
kwai da kwarkwarta,
maimakon su samu
kyakkyawar sakayya
daga gare shi, sai ya
buge da gayyato
mawaka wadanda za'a
kashe sama da Naira
Miliyan 290 akan
harkarsu, yayin da ya
gaza wajen biyan
ma'aikata albashi.
Sheik Baban Tune ya
kuma gabatar da Al
kunuti a cikin sallar
juma'ar, inda ya bukaci
taimakon Allah akan
halin fitina dake
fuskanto jihar ta
Kaduna.@rariya.
A nasa bangare shima sanata shehu sani yi tir da wannan taron kamar yarda jaridan rariya ta rawaita inda yake cewa:-
-Sanata Shehu Sani
Sanata mai wakiltar
Kaduna ta Arewa a
Jiyhar Kaduna, Sanata
Shehu Sani, ya yi tir da
taron ruguntsimin
mawakan kasar nan da
aka shirya yi a Kaduna.
Shehu Sani ya ce
wannan la’anannen taro
ne, kuma bai yi daidai da
dabi’un mazabar da
yake wakilta ba, da
jihar Kaduna da ma
Arewa baki daya.
Bugu da kari, ya ce abin
haushi da takaici ne a ce
za a shirya wannan
taro a Kaduna a daidai
lokacin da arewa ke
zaman makoki da
kuncin ragargaza yankin
da Boko Haram ta yi,
inda ya ce an kashe
mutane sama da dubu
ashirin da biyar, ga
milyoyin da suka rasa
gidaje sannan kuma ga
dubban wadanda aka
arce da su aka yi
garkuwa da su.
Sanatan, wanda ba ya
iya gani ya yi shiru, ya
ce irin kaifin matsalar
tattalin arzikin da ake
fama da ita kawai ta
isa duk mai hankali kada
ma ya yi tunanin kada
ma ya tara jama’a a yi
wannan sharholiya. Ya
ce ma’aikata da masu
karbar fansho na fama
da kiki-kakar biyan su
hakkinsu, don me wani
zai kafci kudi ya shirya
taron sharholiya?
A karshe ya yi kira ga
Shugaba Muhammadu
Buhari da ya nisanta
kansa daga taron ta
hanyar kin amsa
gayyatar da aka yi
masa.
Amma duk da haka wai sai gashi ana sanarda cewa taron yasamu halastan manyan jam'iyar #apc cikuwa harda shugaban kasa #muhammadu_buhari da wasu gwabnonin kasarnan balle mai gayya mai aiki #gwabna_nasir_elrufai.

Anya kuwa ba an mana angulu da kan xabo bane?

¤Abubakar nuhu koso
12/12/2015.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s