DAGA MIMBARIN JIBWIS SOCIAL MEDIA NIGERIA. Sakon Sarkin Saudiyya Ga Shugaban Nigeria Buhari: Mukurkushe ‘yan Shia da Akai a Zaria, Yaki ne da ta’addanci.

Sakon Sarkin Saudiyya
Ga Shugaban Nigeria
Buhari: Mukurkushe 'yan
Shia da Akai a Zaria,
Yaki ne da ta'addanci.
Jibwis Nigeria ta leka
kasar saudiyya, Inda na
ruwaito wannan labari,
kamar yadda Kuka sani
Wannan shine karo na
farko da Sarki salman
yayi jawabi tun bayan
murkurkushe 'yan shi'a
a kwanakinnan. A
tattaunawarsa da
shugaba Buhari ta
hanyar wayar salula,
sarki Salman ya ambaci
cewa kashe daruruwan
yan Shia a birnin zaria
shima yaki ne da
ta'addanci , kamar
yadda hukumar yada
labarai ta kasar Iran ta
shaida.
Kafar watsa labarai ta
Ahlul Bayt ta ruwaito
cewa shugaban Nigeria
Muhammadu Buhari yayi
tattaunawa ta wayar
tangaraho ta
takwaransa na Saudi
Arabia, Salman bin
Abdul Aziz Al Saud.
A yayin tattaunawar,
dukkan shugabannin
guda biyu sun mayar da
hankali ne kan
muhimman alamura da
suka shafi alaka
tsakanin kasa-da-kasa,
gami da harkokin da ke
faruwa a fadin
kasashen guda biyu.
Wannan de yazamto
karona farko bayan
afkawa yan Shi'a da
akayi a zaria da
saudiyya tayi jawabi ta
hanyar jagoran kasar a
kwanaki biyu dasuka
gabata. A wannan
tattaunawa ne de
sarkin ya tabbatar da
cewa kashe daruruwan
yan Shi'a da akayi a
zaria, shima yaki ne da
ta'addanci. Kamar yadda
Kafar yada labarai ta
FARS ta tabbatar.
Harwa yau, sarki
Salman ya bayyana
cikakken goyon bayan
gwamnatin saudiyyah
kan yaki da ta'addanci
da kasar Nigeria ke yi a
halin yanzu. Sarkin
yakuma kara da cewa
Saudi Arabia zata
marawa Nigeria dake
Afirka baya, biyo bayan
jerangiyar ta'addancin
dake aukuwa a kasar.
Sarki Salman bai gushe
ba yana nanata cewa
ayyukan ash-sha kamar
ta'ddanci ba koyarwar
addinin islama bane.
Haka zalika yakara da
cewa saudiyyah bazata
yadda ta shiga sahun
masu katsalandan wa
Nigeria ba, domin hakan
ka iya zama barazana
ga tsaro da cigaban
kasar.
Daga bisani shugaban
Nigeria muhammdu
Buhari ya bayyana
godiyarsa da
jinjinawarsa ga sarki
Salman bisa kuduri da
aniyar da gwamnatin
kasarsa ta dauka na
hada hanu da Nigeria
domin magance
barazanar tsaro da yaki
da ta'addanci. Shugaban
na Nigeria Muhammadu
Buhari ya dauki
alwashin ziyartar kasar
ta saudiyyah a kwana
kwanan nan.
Jibwis Nigeria

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out / Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out / Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out / Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out / Change )

Connecting to %s