DAGA MIMBARIN SALAFIYYAH NETWORK NIGERIA KUNDIN TARIHIN KWAMANDOJIN SALAFIYYAH KASHI NA ‘DAYA (PART 1)

DAGA MIMBARIN
SALAFIYYAH NETWORK
NIGERIA
KUNDIN TARIHIN
KWAMANDOJIN
SALAFIYYAH KASHI NA
'DAYA (PART 1)
.
Wannan Shine Ash-
Sheikh Abu Abdullahi,
Muhammad 'dan Saalih
'dan Muhammadu 'dann
Uthaymeen at-Tamimi.
.
Al-Uthaymeen kamar
yadda aka sani
mutumin 'kasar
Saudiyyah ne wanda ya
fito daga cikin 'kabilar
Banu Tamim.
.
An haife shi ne a ranar
ashirin ga watan
Ramadan hijiriyya ta
dubu 'daya da 'dari uku
da arba'in da bakwai
(1347) a garin Unayzah.
Yayi karatun shi a
hannun manya manyan
malaman duniya irin su
Ash-Sheikh 'Abd ar-
Rahman ibn Naasir as-
Saa'di, Muhammad Amin
ash-Shanqeeti da kuma
Ash-Sheikh AbdulAzeez
Bin Baz.
Uthaymeen ya kwashe
sama da shekaru talatin
da biyar yana
karantarwa a
masallacin Harami dake
garin Makka. Kafin
rasuwarshi, Malami ne a
tsangayar Shari'a dake
jami'ar musulunci na
Imam Muhammad ibn
Saud. Har ila yau memba
ne na majalisar malamai
na duniya, sannan kuma
Shine babban limamin
Masallacin Unayza.
.
Kadan daga cikin
ayyukan da yayi ma
duniyar musulunci sun
kasance kamar haka;
.
Rubuta littafin Sifatu
Salatin Nabiy, Sharh al-
Aqeedat Al-
Hamawiyyah, Sharh
Usool al-Iman, Sharh
Usool al-Thalaathah,
Sharh Hadeeth Jibra'eel.
.
Allahu Akbar Kabiran!
Komai yayi farko zai yi
'karshi. Ash-Sheikh
Uthaymeen ya rasu a
ranar laraba sha-biyar
ga watan Shawwal,
hijira na da shekara
dubu 'daya da 'dari hudu
da ashirin da 'daya
(1421 AH). Ya bar duniya
yana da shekara saba'in
da biyar, sannan anyi
jana'izar shi a garin
Makka Saudi Arabia.
.
Duniyar musuluncin
Nigeria baza ta taba
mantawa da Ash-
Sheikh Uthaimin ba
domin ya karantar da
manya-manyan
malaman Sunnan
'kasarnan irin su Ash-
Sheikh Abdulwahhab
Abdallah Kano da kuma
Ash-Sheikh Muhammad
Auwal Adam Albaniy
zaria (Rahimahullah) a
'karkashin tsarin koyon
karatun irin na zaure.
.
Allah (SWT) muke roko
da ya jikan Ash-Sheikh
Uthaimin. Allah (SWT)
muke roko da ya kai
haske 'kabarinsa.
.
SOURCE:
http://www.uthaimin.com

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s