Illar cin mutuncin mutane (1) @aminiyya

Illar cin mutuncin
mutane (1)
Category: Mumbarin
musulunci Published on
Friday, 04 December
2015 14:58 Written by
Hudubar Sheikh
Abdurrahma As-Sudais
Babban Limamin
Masallacin Ka’aba Hits:
193
Gabatarwa: Bayan haka,
ya ku bayin Allah! Ku bi
Allah Madaukaki da
takawa a cikin magana
da aiki. Ku yi maSa
takawa bisa tawali’u da
bin umarninSa safe da
maraice, kuna masu
tabbatar da girma da
daukaka da fiffiko da
kamalarSa. “Kuma
wanda ya bi Allah da
takawa, Allah zai
kankare masa munanan
ayyukansa, kuma Ya
girmama masa
sakamako.” (k:65:5).
Ya ku Musulmi! A yayin
da duniya ke fama da
fitintinu masu yawa,
jere da juna, take fama
da munanan bala’o’i
marasa iyaka, wadanda
suke girgiza zukata
suka shallake tunani da
hankulan jama’a, sai ga
zamani ya zo da wani
sabon abu da ke bata
tunani ke raunana
tunanin zababbu da
gama-garin jama’a,
yana bijiro da al’umma
zuwa ga rarrabuwa da
rugujewa, yana
kekketawa da yayyaga
hadin kan jama’ar
Musulmi da zaman
lafiyarta. Al’umma ba
ta ji zafi ba, face
saboda aukuwarsa,
jama’a da daidaikun
mutane ba su gushe ba,
face wannan abu yana
kekketa su yana karya
su, yana jefa su cikin
fushin zubar da jini.
Wannan abu – Allah Ya
tsare ku – shi ne cin
mutuncin mutane da
bata martabarsu da
tuhumar barrantattu
daga cikinsu da niyyar
cin zarafinsu. Hakika
wannan abin ki ne,
kuma kaiton yin haka,
Allah wadaran wannan
abin zargi da wawaye
suke riko da shi, hali ne
da ke kaiwa ga watsa
kazafi da kiren-karya da
kalamai masu jawo
fasadi a tsakanin
Musulmi, ya kawo juya
baya ga juna da kaurace
musu. Hakan na lalata
zamantakewa ya jawo
kirkirar karya a kan
mutum ba kunya ba
tsoro, ba don komai ba,
sai don a zubar da
mutuncin wani haka
kawai, kuma a haifar da
cutarwa marar iyaka da
za ta daidaita zaman
jama’a ta girgiza tushen
zaman al’umma.
Saboda wadannan
miyagun abubuwa da
wannan dabi’a ke
jawowa na dagula
al’amura da bata zaman
lafiya, sai gargadi mai
karfi da tattalin narkon
azaba mai tsanani ya zo
a cikin Alkur’ani da
Sunnah kan munin
makomar duk mai kiren-
karya yana watsawa:
“Kuma wadanda suke
cutar muminai maza da
muminai mata, ba da
wani abu da suka aikata
ba, to, lallai sun dauki
kiren-karya da zunubi
bayyananne.” (k:33:58).
Daga Abu Huraira (RA)
ya ce: “Lallai Annabi
(SAW) ya ce: “Riba tana
da matakai ko nau’o’i
har saba’in. Mafi
saukinta shi ne misalin
mutum ya yi zina da
mahaifiyarsa. Kuma lallai
mafi girman riba, shi ne
mutum ya rika cin
mutuncin dan uwansa.”
Bazzaru ya ruwaito shi
a cikin Musnad dinsa sai
Ibn Abu Shaiba a
Musnaf dinsa.
Allahu Akbar! Me ya kai
girman mutuncin
Musulmi? Me ya kai
daukaka da karimcinsa?
Domin haka ne shari’a
ta tsare shi kada a zagi
mutum kada a fada
masa mummunar
magana kada a auka
wa mutincinsa, kada a
soke shi kada a yi masa
kazafi. Kai kiyaye
mutunci, mafi kyan abin
da ake nema ne, kuma
mafi girman manufofin
shari’a kamar yadda
ma’abuta ilimi irin su
Shadabi da wadansu
suka bayyana.
Ya ku muminai! Bin
aibobin mutane da
al’aurorinsu don gano
nakasunsu da
gazawarsu da
kazantarsu mummunar
hanya ce mai
halakarwa. dabi’a ce ta
mutanen da ake zargi
kuma kazanta ce, kuma
ta saba wa shari’ar
Allah Madaukaki da
shiriyar ManzonSa
(SAW) wanda yake
cewa: “Albarka ta
tabbata ga wanda ya
shagaltu da
laifuffukansa daga
laifuffukan mutane.”
Bazzaru ya ruwaito a
Musnad dinsa sai Baihaki
a Shu’ubarsa.
Wani magabaci yana
cewa: “Mun riski
magabatan kwarai ba
su ganin ibada ta
takaita a kan Sallah da
Zakka kawai, a’a suna
ganin ta hada da
kamewa daga taba
mutuncin mutane.”
Kuma Malik bin Dinar
(Allah Ya yi masa
rahama) ya kasance
yana yawan cewa: “Ya
ishi mutum zunubi a ce
bai kasance salihi ba,
saboda yana aukawa ga
cin mutuncin mutane.”
Kuma mafi muni daga
cikin cin mutunci shi ne a
rika kazafi kiri-kiri a soki
mutum a bata shi a ce
ba haka yake nufi ba a
zuciyarsa, a tuhumi
niyyarsa da manufarsa.
A kutsa cikin dukkan
siffofi na gaibi da ke
cikin zuciyarsa a yi
masa kazafin aibubbuka
da barna da babu
wanda ya san
hakikaninsu ban da Allah
Madaukaki. Kuma a yi ta
watsawa da yayata
wadannan abubuwa ta
hanyar kiyayya da rudin
mutane a kawata
kalmomi na karya a
basar da jahilai a watsa
sharruruka. Ina abin da
ya kai wannan zama
abin bakin ciki, tir da
wannan abin bakin ciki!
Kuma karin abin bakin
ciki da ke cikin wannan
muguwar dabi’a ta keta
rigar mutuncin mutane,
shi ne, yadda ire-iren
wadannan karairayi
suke zama tamkar
gaskiya a wurin
mutane. Su zamo su ne
daidai, su ne gaskiya.
Ku ji tsoron Allah! Ku ji
tsoron Allah! Ba yadda
za a yi haka ya zama
gaskiya, wannan ba
wani abu ba ne, face
jahilci da mugun zato da
suke haifar da aibu da
gadar da zunubi. Masu
yin haka Allah Ubangijin
talikai Ya siffanta su da
cewa: “Ba mu zato,
face zato mai rauni,
kuma ba mu zama
masu yakini
ba.” (k:45:32).
Kowane lafazi za a
taskace shi a cikin
littattafan ayyukanmu
domin Ranar Hisabi, a
cikinsa za mu ga aikin
sharrin da muka furta
da bata wani da muka
yi a cikin lafazi da labari
an rubuta su lafazi-
lafazi.
Ya ’yan uwa a cikin
imani! Ana yin haka ne
alhali miyagun abubuwa
suna karuwa, munanan
ayyuka suna dada
yaduwa, cin mutunci ya
zama babban abin ado a
tsakanin al’umma.
Malamanta sun zamo
abin dariya, wanda yake
cin mutuncinsu ya zama
hazaki abin koyi a
tsakanin mutane, ya
zama tauraro, saboda
yana tozarta lamarinsu,
yana bata su ta
kafafen sadarwa na
zamani!
Duk inda ka juya abin da
za ka gani, shi ne suka
da zagi da soki burutsu
da cin dunduniya ta
amfani da alkaluma a
yada dafin mujirimanci
da harsuna masu guba
a ci mutuncin mafifitan
cikin al’umma,
barrantattu da salihai
da masu tsarkinsu,
wandanda suke rayuwa
domin gyara da maganin
cututtukan al’umma!
Hakika mai tsira da
amincin Allah ya fadi a
cikin mashahuriyar
hudubarsa a Ranar Arfa
cewa: “Lallai jininku da
dukiyarku da
mutuncinku haramun ne
(katangaggu ne) a
tsakaninku, kamar
yadda wannan rana
taku take (da martaba)
a wannan gari naku, a
wannan wata naku
(masu alfarma).” Kuma
(SAW) ya ce: “Kowane
Musulmi haramu ne a
kan dan uwansa
Musulmi ya taba jininsa
ko dukiyarsa ko
mutuncinsa.” Muslim ya
ruwaito.
Imam Ahmad (Allah Ya
yi masa rahama) ya ce:
“Ban taba ganin wani
yana magana a cikin
mutane ba (yana cin
mutuncinsu), face
(mutuncinsa) ya zube.”
Shaihul Islam Ibn
Taimiyya (Allah Ya yi
masa rahama) ya ce:
“Magana kan mutane
wajibi ne ta kasance
bisa ilimi da adalci ba da
jahilci da zalunci ba.
Kuma auka wa
mutuncincu ya fi satar
dukiyarsu muni.”
“Ya mai keta mutuncin
mutane mai yanke,
Hanyoyin kauna da
soyayya, za ka rayu ba
abin mutuntawa ba.
Da ka kasance
’yantacce daga tsatso
mai girma,
Ba za ka kasance mai
keta mutuncin Musulmi
ba.”
Don haka ya ku ’yan
uwa a cikin imani! Lallai
mai kutsawa a cikin
mutuncin Musulmi,
kuma mafi muni da
kebantar girman masu
karkata, shi ne mai cin
mutuncin shugabannin
Musulmi da malamai da
masu gyara. Halinsa shi
ne juya wa Allah baya
da bijire maSa, mai
komawa zuwa ga
tsanani, bai san ya yi
godiya da shukura ga
ma’abucin falala ba,
balle ya san kima da
matsayinsa.
Hakika an wayi gari
wadansu mutane
musamman saboda
samuwar sababbin
hanyoyin sadarwa, sun
zamo ba su da sukuni,
ba su da hakuri, face
sun kekketa mutuncin
mutane da munanan
kalamai da zunde da
tuhume-tuhume. Tir da
manufa da burinsu.
Suna rubuta zur da
alkalumansu, suna boye
gaskiya. Da haka
tunaninsu ke umartarsu
domin su samu damar
wargaza hadin kan
al’ummar Musulmi da
muminai ta hanyar
rubuce-rubucen son
zuciya da bin son
rayukan kungiyoyi da
mazhabobinsu, ba su
yin aiki face ga
wadansu kungiyoyin
asiri da burinsu shi ne
wargaza hadin kai da
zaman lafiyar al’ummar
Musulmi.
Ya ku masu keta
mutunci domin ganin
bayan Musulmi da kawo
karshensu! Ku nisanci
wadannan miyagun
abubuwa masu
fusatarwa, ku ciru daga
wadannan abubuwa
masu halakarwa, ku yi
kwadayi zuwa addini ta
hanyar neman tsira da
salama gabanin
aukuwar mutuwa mai
zuwa afke da nadama:
“Kuma ba domin falalar
Allah ba a kanku da
rahamarSa, a cikin
duniya da Lahira. Lallai
ne, da azaba mai girma
ta shafe ku a cikin abin
da kuka kutsa da
magana a
cikinsa.” (k:24:14).
Mu nazarci wasu
sinadaran kyautata
rayuwa (3)(1)
Tare da Sheikh Yunus
Is’hak Almashgool,
Bauchi(11)
Shin kana cikin ’yan
gatan Allah a Ranar
kiyama?(1)
Kyauta da kyauta – yi
don Allah ba ta rage
dukiyar musulmi (2)
Mu nazarci wasu
sinadaran kyautata
rayuwa (4)
Tare da Sheikh Yunus
Is’hak Almashgool,
Bauchi (1)
Illar cin mutuncin
mutane (2)
Kyauta da kyauta-yi don
Allah ba ta rage dukiyar
Musulmi
Mu nazarci wasu
sinadaran kyautata
rayuwa(5)
Tare da Sheikh Yunus
Is’hak Almashgool,
Bauchi (7)
Illar cin mutuncin
mutane (1)
Manuniya kan ladubban
yin addu’a (3)
Yadda ya kamata mu
kasance a rayuwarmu
ta yau da kullum(1)
are da Sheikh Yunus
Is’hak Almashgool,
Bauchi
Musulmi da farfagandar
makiya(1)

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s