ME AKE NUFI DA SUNNAH? DAGA ZAUREN SUNNAH DA TAMBAYOYI.

DAGA ZAUREN SUNNAH
DA TAMBAYOYI:
ME AKE NUFI DA
SUNNAH?
Kalmar SUNNAH tana da
ma'anoni masu yawa
duba da yadda malamai
sukayi bayaninta a
fannonin ilmi daban-
daban.
Ga wasu daga cikin
ma'anoninta:
1- Sunnah a wurin
malaman Lugah(wato
malaman harshen
larabci): Shine hanya ko
turba.
2- Sunnah a wurin
malaman hadisi: Shine
abunda aka samo ko
aka jingina ga Manzon
Allaah sallallaahu alaihi
wa alihi wasallam na
magana ko aiki ko
tabbatarwa(ma'ana
abunda akayi a
gabanshi ko a
zamaninsa yayi shiru
baiyi inkarinsa ba) ko
sifa na halitta da
dabi'unsa.
3- Sunnah a wurin
malaman usulul- fiqh:
Shine abunda aka samo
daga Manzon Allaah
(s.a.w) na magana ko
aiki ko tabbatarwa
wanda zai iya
kasancewa dalili a
shar'ance.
4- Sunnah a wurin
malaman fiqhu: Shine
abunda idan musulmi ya
aikatashi za'a bashi
lada, idan kuma
yabarshi baza'ayi mishi
u'kubah ko rubuta mishi
zunubi ba. Misali kamar
karanta sura bayan
fatihah a cikin sallaah.
Sai dai ba'a kiran abu
sunnah sai idan ya
inganta daga Manzon
Allaah(s.a.w), a
karkashin haka ba
daidai bane mutum
yace: wannan sunnar
bata inganta ba, sai dai
yace wannan hadisin bai
inganta ba, amma
shima sai idan yakai
matsayin fadin hakan,
domin inganta hadisi ko
raunatashi ba da molon
kai akeyi ba; da ilmi
akeyi. Idan kuma
mutum bashi da ilmin
dazai iya gano inganci
ko rashin ingancin hadisi
to sai ya dogara da
ingantawar wani daga
cikin malaman hadisi
kwararru wadanda
sukayi nutso a cikin
ilmin, kamar: Al-imam
Malik, Al-imam As-
shafi'iy, Al-imam
Ahmad bn Hanbal, Masu
alkutubus-Sittah, Aliyu
bnul Madiniy, Ad-
daraqu'dniy, Al-kha'dibul
Baghdaadiy, Azh-
zahabiy, Ibn Rajab, Ibn
Hajr, Ahmda Shaakir,
Muhammad Nasiruddenil
Albaniy, d.s.
Kuma ita sunnah
wajibine abita a kuma yi
aiki da ita, babu
banbanci tsakanin farilla
da sunnah(a wurin
malaman fiqhu) da
mustahabbi, domin
karkasa abunda ya
tabbata a shari'ah
zuwa farilla ko sunnah
ko mustahabbi
anyishine domin idan
akasamu matsala ko
tangarda a cikin ibadah
asan yadda za'a
gyarata. Ba an
karkasasu bane domin
ayi aiki da wani abar
wani ba.
Kuma ita sunnah ba a
baki bane kadai ko a
rubuce ba; a'a dole sai
anhada da aiki, domin
shi imani da Manzon
Allaah(s.a.w) baya
tabbata sai idan ka
yarda da sunnarsa,
sannan ka furta,
sannan kuma kayi aiki
da ita.
Muna rokon Allaah ya
rayamu akan sunnah,
yadauki ranmu akan
sunnah, ya tashemu
ranar Alkiyamah tareda
Ahlussunnah, yakuma
hadamu da maigidan
sunnar bakidaya a
Aljannar Firdausi.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s