Kyauta da kyauta- yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi; Daga jaridar aminiya

Kyauta da kyauta-
yi don Allah ba ta
rage dukiyar
Musulmi
Category: Rayuwar
musulmi Published on
Friday, 11 December
2015 15:05 Written by
AHMAD MUHAMMAD
Hits: 155
Da sunan Allah, Mai
rahama, Mai jinkai.
Dukkan yabo da godiya
na Allah ne, Ubagijin
halittu, Wanda da
ni’imarSa kyawawan
abubuwa suke cika,
kuma Ya sanya yin
kyauta da kyauta-yi
cikin kyawawan dabi’un
Musulmi. Tsira da
Amincin Allah su kara
tabbata ga mafificin
halittu, Annabi
Muhammadu dan
Abdullahi, (Sallallahu
Alaihi Wasallam), wanda
Allah Ya aiko shi, ya
kasance jinkai ga talikai,
kuma ya koyar da cewa
kyauta da kyauta-yi ba
ta rage dukiya; Amincin
Allah ya tabbata ga
alayensa da
sahabbansa, sannan da
duk wadanda suka bi
gurabunsu cikin
kyautatawa har zuwa
Ranar karshe.
Lallai, mafi kyawun cikar
zance shi ne Littafin
Allah (Alkur’ani), kuma
mafi alherin shiriya ita
ce ta Annabi
Muhammadu, (Sallallahu
Alaihi Wasallam). Mafi
sharrin al’amari shi ne
wanda aka kirkire shi
cikin addini; duk abin da
aka kirkira cikin addini
bata ne, wanda kuma
karshensa wuta. Allah
Ya kare mu daga gare
ta. Amin.
Bayan haka, yau, kamar
yadda kanun mukala ya
nuna, za mu duba
dabi’ar kyauta da
kyauta-yi ne, kamar
yadda bayanin haka ya
zo a cikin littafin
Shakhsiyyatul Muslim
Kama Yasughuhal Islam
Fiy Alkitab Wassunnah
na Dokta Muhammad Ali
al-Hashimi, tare da
wasu bayanai daban.
Allah Ya ba mu dacewa
wajen bi da kuma
aiwatar da wannan
dabi’a, wadda ba ta sa
talauci, don mu samu
rabauta duniyarmu da
lahirarmu.
Malam ya ce: Babu
shakka duk Musulmi na
gaskiya, wanda yake da
yakinin bin karantarwar
addininsa, zai kasance
mai kyauta ne shi, mai
kyauta-yi ta yadda zai
ta bibiyar hanyoyin da
zai ga ya kyautata wa
al’ummar da ke kewaye
da shi, a kowane yanayi
da lokaci, wato yana
cikin wadata ne ko
rashi.
A duk lokacin da
wannan Musulmi ya yi
kyauta don Allah, to
yakan bayar ne da dadin
zuciya, alhali yana sane
da cewa ba asara ya yi
ba, kuma ba barna ya yi
ba, domin yana sane da
cewa Allah, Wanda Yake
sane da komai, Ya
tanada masa abin a
wajenSa. Allah Ta’ala Ya
ce, “…. Kuma duk abin da
kuka ciyar daga alheri,
to lallai Allah, gare shi
(abin da kuka ciyar din),
Masani ne.” Surar
Bakarah, aya ta 273.
Haka nan ya yi imanin
cewa duk abin da ya
kashe a cikin kyauta-yi
(saboda Allah), abin zai
komo gare shi, kuma za
a nunnunka masa shi,
Allah Ya ribanya masa
lada, a nan duniya da
kuma Lahira, kamar
yadda Allah Ya ce,
“Misalin wadanda suke
ciyar da dukiyoyinsu don
yada kalmar Allah,
kamar misalin kwaya
daya ce, sai ta fitar da
zangarniya guda
bakwai, kowace
zangarniya kuma a
cikinta (aka samu)
kwaya dari. Kuma Allah
Yana ninkawa ga wanda
Ya ga dama, kuma
Allah, Mai yalwa
(yalwata wa kowa) ne,
Masani ne.” Surar
Bakarah, aya ta 261.
A cikin littafin Tarjama
da Sharhin Ma’anonin
Alkur’ani Mai Girma, a
shafi na 230, Shaikh
Ja’afar Mahmud Adam
ya ce, “Abin nufi, misalin
wadanda suke ciyar da
dukiyoyinsu don yada
kalmar Allah, don
taimakon addinin
Musulunci, …kamar
misalin kwaya daya ce…
da aka shuka ta a cikin
kasa…sai ta fitar da
zangarniya guda
bakwai, kowace
zangarniya kuma a
cikinta… aka samu
kwaya dari, ka ga za a
ninka wa mutum har
sau dari bakwai ke nan.
Ubangiji Ta’ala Ya ce, “…
Yana ninkawa ga wanda
Ya ga dama…”
gwargwadon
kyakkyawar niyyar
mutum lokacin da zai
ciyar da dukiya din,
kuma Shi (Allah), Mai
yalwa ne, kuma Masani
ne.
“Hadisi ya tabbata a
cikin Sahihi Muslim
[na1151], Manzon Allah
(Sallallahu Alaihi
Wasallam), ya nuna
yadda Allah Yake
ninninka wa mutum aiki
nagari. Kowane aiki,
kyakkyawan aiki daya,
za a iya ninninka wa
mutum sau goma; ba
ma sau goma ba, za a
ninka wa mutum har
sau dari bakwai. Wani
Hadisi ya sake tabbata
a cikin Sahihi Muslim (na
1892), Manzon Allah
(Sallallahu Alaihi
Wasallam), zai tafi wani
jihadi, sai wani Balarabe
ya kawo taimakon
taguwa guda daya tare
da akalarta a daure da
ita. Da Manzon Allah
(Sallallahu Alaihi
Wasallam), ya karba, sai
ya ce, “A ranar tashin
Alkiyama Ubangiji Ta’ala
Zai maye maka gurbi,
sakamakon wannan
guda daya da taguwa
guda dari bakwai
kowace da akalarta.”
Abin nufi, wannan
kinaya ce zuwa ga lada
da za a ninninka wa
mutum a ranar tashin
kiyama.”
Allah Yana sane kuma
Yana musanyawa: Allah
Ya ce, “….Kuma abin da
kuka ciyar daga wani
abu, to, Shi (Allah) ne
Zai musanya shi…” Surar
Saba’i, aya ta 39.
Haka nan Allah Ya ce,
“….Kuma duk abin da
kuka ciyar na alheri, to
domin kawunanku ne,
kuma ba fa za ku ciyar
ba, sai don neman
yardar Allah, kuma duk
abin da kuka ciyar na
alheri, za a cika muku
(ladarsa), alhali da dai,
ba za a zalunce ku ba.”
Surar Bakarah, aya ta
272.
Musulmi na gaskiya
yana bayar da dukiyarsa
ne alhali yana da yakinin
Allah Zai maye masa
gurbinta ta fuskar
sanya wa abin da ta
baro (sauran) albarka,
ga kuma ninki na lada a
wajenSa. Kuma idan ya
makale ta (dukiyar), ya
yi rowa, ya ki bayarwa
(saboda tsoron talauci),
to sai Allah Ya tauye ta,
Ya saka masa asara,
kamar yadda Manzon
Allah (Sallallahu Alaihi
Wasallam), ya fadi
cewa, “Duk safiya, idan
bayin Allah suka tashi,
sai wasu Mala’iku biyu
su sauko. daya yana
addu’a cewa, “Ya Allah,
Ka musanya wa wanda
ya yi kyauta da
dukiyarsa;” dayan kuma
yana cewa, “Ya Allah,
Ka sanya asara ga mai
rowa.” Buhari da Muslim
ne suka ruwaito shi.
A wani Hadisin kudusi,
Allah Yana cewa, “Ciyar
(bayar; yi kyauta) da
dukiyarka, ya kai dan
Adam, Ni kuma in ciyar
da kai (in ba ka, in yi
maka kyautar) dukiya.”
Buhari da Muslim ne
suka ruwaito shi.
Musulmin da ya yarda
da Allah, ba ya wata
shakka a cikin
zuciyarsa, in ya bayar
(ya yi kyauta) saboda
Allah, cewa dukiyarsa
ta ragu don ya yi haka,
sai ma dai karuwa take
yi, kamar yadda Hadisin
da Muslim ya ruwaito ya
nuna, cewa, Manzon
Allah, (Sallallahu Alaihi
Wasallam), ya ce,
“Sadaka (kyauta ko
ciyarwa saboda Allah,
ko fitar da zakka ta
farilla, misali) ba ta rage
dukiya….”
Ladar da ake samu a
dukiyar da aka kyautar
saboda Allah tana da
yawa domin Allah Yana
nunnunkata ninkin-ba-
ninkin, kamar yadda
bayani ya gabata). Shi
ya sa ma Manzon Allah
(Sallallahu Alaihi
Wasallam), yakan ce,
“Dukiyar da take
taskance ita ce wadda
aka bayar da ita saboda
Allah.” A’isha (Allah Ya
yarda da ita), ta ba da
labarin wata tunkiya da
aka yanka, aka yi ta
rabon namanta, har sai
lokacin da Manzon Allah
(Sallallahu Alaihi
Wasallam), ya tambayi
ko me ya rage a cikinta,
sai aka ce masa,
“Karfata daya.” Sai ya
ce, “An taskance komai
na tunkiya, sai karfata
daya kadai.” Imamu
Tirmiziy ne ya ruwaito
shi kuma ya ce Hadisi ne
mai kyau, ingantacce.
Wato manufa, an
taskance ladar kowane
sashi na tunkiyar ban da
karfata daya, wadda
suka ci. Shi ya sa
Bahaushe ma kan ce,
“Abin da ka bayar, shi
ne naka, abin da ka ci
kuwa na salga (masai)
ne.”
Allah Ya ba mu dacewa
da abin da yake alheri.
Nan za mu dakata, sai
makon gobe, in Allah Ya
kai mu.
Wassalamu alaikum
warahmatullah!
Mu nazarci wasu
sinadaran kyautata
rayuwa (3)(1)
Tare da Sheikh Yunus
Is’hak Almashgool,
Bauchi(11)
Shin kana cikin ’yan
gatan Allah a Ranar
kiyama?(1)
Kyauta da kyauta – yi
don Allah ba ta rage
dukiyar musulmi (2)
Mu nazarci wasu
sinadaran kyautata
rayuwa (4)
Tare da Sheikh Yunus
Is’hak Almashgool,
Bauchi (1)
Illar cin mutuncin
mutane (2)
Kyauta da kyauta-yi don
Allah ba ta rage dukiyar
Musulmi
Mu nazarci wasu
sinadaran kyautata
rayuwa(5)
Tare da Sheikh Yunus
Is’hak Almashgool,
Bauchi (7)
Illar cin mutuncin
mutane (1)
Manuniya kan ladubban
yin addu’a (3)
Yadda ya kamata mu
kasance a rayuwarmu
ta yau da kullum(1)
are da Sheikh Yunus
Is’hak Almashgool,
Bauchi
Musulmi da farfagandar
makiya(1)

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s