Kyauta da kyauta – yi don Allah ba ta rage dukiyar musulmi (2); Daga jaridar aminiya

Kyauta da kyauta
– yi don Allah ba ta
rage dukiyar
musulmi (2)
Category: Rayuwar
musulmi Published on
Friday, 18 December
2015 15:23 Written by
AHMAD MUHAMMAD
Hits: 113
Da sunan Allah, Mai
rahama, Mai jinkai.
Dukkan yabo da godiya
na Allah ne, Ubagijin
halittu, Wanda da
ni’imarSa kyawawan
abubuwa suke cika,
kuma Ya sanya yin
kyauta da kyauta-yi
cikin kyawawan dabi’un
Musulmi. Tsira da
Amincin Allah su kara
tabbata ga mafificin
halittu, Annabi
Muhammadu dan
Abdullahi (Sallallahu
Alaihi Wasallam), wanda
Allah Ya aiko shi, ya
kasance jinkai ga talikai,
kuma ya koyar da cewa
kyauta da kyauta-yi ba
ta rage dukiya; Amincin
Allah ya tabbata ga
alayensa da
sahabbansa, sannan da
duk wadanda suka bi
gurabunsu cikin
kyautatawa har zuwa
Ranar karshe.
Lallai, mafi kyawun cikar
zance shi ne Littafin
Allah (Alkur’ani), kuma
mafi alherin shiriya ita
ce ta Annabi
Muhammadu (Sallallahu
Alaihi Wasallam). Mafi
sharrin al’amari shi ne
wanda aka kirkire shi
cikin addini; duk abin da
aka kirkira cikin addini
bata ne, wanda kuma
karshensa wuta. Allah
Ya kare mu daga gare
ta. Amin.
Bayan haka, mun
kwana bayan mun koro
bayani a karkashin
kanun, “Allah Yana sane
kuma ana
musanyawa,” har muka
kai daidai inda Manzon
Allah (Sallallahu Alaihi
Wasallam), ya ce,
“Dukiyar da take
taskance ita ce wadda
aka bayar da ita saboda
Allah.” A’isha (Allah Ya
yarda da ita), ta ba da
labarin wata tunkiya da
aka yanka, aka yi ta
rabon namanta, har sai
lokacin da Manzon Allah
(Sallallahu Alaihi
Wasallam), ya tambayi
ko me ya rage a cikinta,
sai aka ce masa,
“Karfata daya.” Sai ya
ce, “An taskance komai
na tunkiya, sai karfata
daya kadai.” Imamu
Tirmiziy ne ya ruwaito
shi kuma ya ce Hadisi ne
mai kyau, ingantacce.
Ga ci gaba:
A kan irin wannan
garabasar ladar ce
Manzon Allah (Sallallahu
Alaihi Wasallam), ya rika
karsasa Musulmi wajen
yin kishi (gabda -kishin
da ma ina da irin abin da
wane ya samu, sai in yi
kamarsa ko in fi shi) ga
mutum biyu, inda ya ce,
“Ba hasada (gabda-
takara), sai dai a kan
mutum biyu: (1)
Mutumin da Allah Ya
wadata shi da dukiya
kuma Ya azurta shi da
ciyar da ita a cikin abin
da yake na gaskiya
(wato saboda Allah); da
kuma (2) Mutumin da
Allah Ya ba shi ilimi da
basira, yana aiki da shi
kuma yana karantar da
mutane.” Buhari da
Muslim ne suka ruwaito
Hadisin.
Dukiya dai ita ce kashin
bayan sinadarin gudanar
da al’amurran rayuwa a
tsakanin al’umma,
musamman idan aka
dace da mai ita yana
bayarwa don Allah
kuma cikin abin da yake
na gaskiya, don amfanin
kowa da kowa; sai
kuma wanda yake da
ilimi da basira, kuma
yana amfani da su
wajen shiryar da
al’umma wajen bin abin
da yake daidai. Babu
shakka idan aka samu
haduwar wadannan
mutum biyu a tsakanin
al’umma, za a ga
kyakkyawar al’umma,
wadda sai dai a yi
kamarta, amma ba a
wuce ta da komai ba.
Saboda haka shi
Musulmi na gaskiya
yana bayar da dukiyarsa
tare da sanin cewa za
ta komo gare shi ta
fuskar lada da
kyautatuwar abin da ta
baro tun farko. Wannan
dalili ya sa yake bayar
da dukiyar, alhalin ba ya
jin ya wuce wuri ko
kuma yana takura wa
magadansa, balle ya
hana musu samu daga
gare ta, shi ya sa ba za
a ga wata alamar rowa
a cikin gudanarwarsa
ba. Haka dai za a same
shi mai tafiyar da
al’amurransa a tsaka-
tsakin yanayi domin
yana lura da abin da
shari’a ta gindaya masa
a rayuwa.
Hasali ma dai za a iske
cewa abin da ya bayar
na dukiyarsa saboda
Allah ya fiye masa dadi
a ransa, saboda ita ce
tasa, a kan wadda ya
taskance ta don
magada, wadda da
zarar ya mutu, za a
raba ta a tsakaninsu.
Wannan ne ma ya sa
Manzon Allah (Sallallahu
Alaihi Wasallam), ya ce
wa sahabbai, “Wane ne
ya fi son dukiyar (da zai
bar wa) magadansa a
kan dukiyarsa.” Sai suka
ce, “Ya Manzon Allah, ba
wanda yake son dukiyar
magadansa a kan
dukiyarsa.” Sai ya ce,
“Dukiyar (mutum ta)
gaskiya, ita ce wadda
ya bayar (saboda Allah);
amma dukiyar
magadansa, ita ce
wadda ya (mutu ya) bar
musu.” Buhari ne ya
ruwaito Hadisin.
Ita kyauta da kyauta-yi,
daya ce daga cikin
kyawawan dabi’un
Musulunci da kuma
Musulmi. Shi ya sa ma a
yayin da wani mutum
ya zo ya tambayi
Ma’aiki (Sallallahu Alaihi
Wasallam), “Wane
(aikin) Musulunci ne ya
fi?” Sai Manzon Allah
(Sallallahu Alaihi
Wasallam), ya ce, “Ciyar
da mutane da yin
sallama ga wanda ka
sani da wanda ba ka
sani ba.” Buhari da
Muslim suka ruwaito
Hadisin.
Ba a bude hannu duka:
Kada wajen zumudin
samun lada mutum ya
kwashe dukiyarsa gaba
daya ya rabe ta, ya bar
magadansa ba su da
komai. Ba a bude hannu
duka. Kowane irin
al’amari na rayuwa,
Musulunci ya tsara
yadda ya kamata a
gudanar da shi, sai dai
mutum ya lura, kada ya
kasa kuma kada ya
wuce wuri. Kamar
yadda bayar da dukiya
saboda Allah yake da
muhimmanci, haka ma
tsare mutuncin
magada, don kada a bari
su koma mabarata a
tsakanin jama’a.
Wannan kuwa ya dace
da abin da ya gudana
tsakanin sahabi Sa’adu
dan Abu Wakkas da
Annabi, lokacin da rashin
lafiya ta tsananta gare
shi, ya kai gargara.
Yayin da Manzon Allah
(Sallallahu Alaihi
Wasallam), ya ziyarci
Sa’ad (Allah Ya yarda da
shi), don ya duba shi
game da rashin
lafiyarsa, sai ya ce
masa, “Ya Manzon
Allah, ina da dukiya mai
yawa kuma ’ya’ya
mata biyu kadai gare ni
(da za su gaje ni), shin
in bayar da kashi biyu
cikin ukun dukiyata
sadaka?” Manzon Allah
(Sallallahu Alaihi
Wasallam), ya ce, “A’a.”
Sai ya ce, “To, in ba da
rabi?” Manzon Allah
(Sallallahu Alaihi
Wasallam), ya ce, “A’a.”
Sai ya ce, “To, kashi
daya cikin uku fa?”
Manzon Allah (Sallallahu
Alaihi Wasallam), ya ce,
“Ka bayar da kashi daya
cikin ukun, amma dai shi
ma yana da yawa!”
Daga nan ne sai Manzon
Allah (Sallallahu Alaihi
Wasallam), ya yi
bayanin cewa, “Ka bar
’ya’yanka cikin wadata,
ya fi ka bar su cikin
talauci, su koma suna
bara (ko rokon mutane).
Kuma ka sani, ba abin
da za ka bayar (kyauta
ko sadaka), ba tare da
an ba ka ladarsa ba, ko
da loma ce da ka dauka
ka sanya a cikin bakin
matarka.” Buhari ne ya
fitar da Hadisin.
Manzon Allah, Sarkin
Kyauta!!
Manzon Allah (Sallallahu
Alaihi Wasallam), shi ne
sarkin kyauta, madubi
na gaskiya abin koyi
dangane da kyauta da
kyauta-yi. Ba a taba
samun wani nakasu
daga wajen Manzon
Allah (Sallallahu Alaihi
Wasallam), dangane da
kyauta ba, kuma bai
taba hana mabukacin da
ya roke shi wani abu
ba. In yana da abin da
zai bayar, ba ya jinkiri; in
kuma babu abin
bayarwa a wannan
lokacin, yakan hakurtar
da mabukaci, ya saurari
abin da za a ba shi.
Sahabi Jabir (Allah Ya
yarda da shi), ya ce, “Ba
a taba tambayar
Manzon Allah (Sallallahu
Alaihi Wasallam), wani
abu ya ce, ‘A’a’ ba.”
Buhari da Muslim suka
fitar da wannan Hadisi.
Allah Ya taimake mu
wajen yin kyauta domin
neman yardarSa, amin.
Mu kwana nan, sai
makon gobe, in Allah Ya
kai mu. Wassalamu
alaikum warahmatullahi
wabarakatuh!
Mu nazarci wasu
sinadaran kyautata
rayuwa (3)(1)
Tare da Sheikh Yunus
Is’hak Almashgool,
Bauchi(11)
Shin kana cikin ’yan
gatan Allah a Ranar
kiyama?(1)
Kyauta da kyauta – yi
don Allah ba ta rage
dukiyar musulmi (2)
Mu nazarci wasu
sinadaran kyautata
rayuwa (4)
Tare da Sheikh Yunus
Is’hak Almashgool,
Bauchi (1)
Illar cin mutuncin
mutane (2)
Kyauta da kyauta-yi don
Allah ba ta rage dukiyar
Musulmi
Mu nazarci wasu
sinadaran kyautata
rayuwa(5)
Tare da Sheikh Yunus
Is’hak Almashgool,
Bauchi (7)
Illar cin mutuncin
mutane (1)
Manuniya kan ladubban
yin addu’a (3)
Yadda ya kamata mu
kasance a rayuwarmu
ta yau da kullum(1)
are da Sheikh Yunus
Is’hak Almashgool,
Bauchi
Musulmi da farfagandar
makiya(1)

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s