ME YA FARU A KARBALA?

ME YA FARU A
KARBALA?
Wane ne Husaini?
Shi ne jikan Manzon
Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam HUSAINI Dan
Ali Dan Abu Dalib Dan
Abdulmuttalibi Dan
Hashimu Al Hashimi.
Mahaifiyarsa ita ce
Fatimah Diyar Manzon
Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam.
An haife shi a cikin
watan Sha’aban na
shekara ta hudu bayan
hijira.
(watanni 11 ke tsakanin
sa da wansa Al Hasan).
Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallam ne ya
sanya masa suna, ya
kuma yanka masa rago.
A Lokacin wafatin
Manzon Allah Sallalahu
Alaihi Wasallam
HUSAINI na da shekara
6 da wata 7.
HUSAINI ya fi kowa
kama da Manzon Allah
Sallallahu Alaihi
Wasallam ta kasan
jikinsa. Amma Al Hasan
ya fi shi kama da shi ta
saman jiki.
Sun tashi kamar
tagwaye saboda
kusancin shekarunsu
kuma Manzon Allah
Sallallahu Alaihi
Wasallam ya kasance
yana son su da kaunar
su irin so da kaunar da
ba sa boyuwa. Ya kan
kuma yi musu addua
yana cewa, “Ya Allah!
Hakika ina son su, Ya
Allah kai ma ka so su”.
Wannan ya sa masu
kwarjini da kauna ba na
wasa ba a wurin
Sahabbai wadanda
kaunar da suke ma
Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallam ta sa
suna son duk abinda
yake so kuma yake
kauna.
HUSAINI ya yi tarayya
da Dan uwa sa Al Hasan
a wata falala wadda
suka kebanta da ita, ita
ce kasancewar su
shugabannin matasan
aljanna.
(Al Jami’ na Tirmidhi,
Hadisi na 3768 da Al
Musnad na Ahmad (3/3
da 3/62) da Al
Mustadrak na Hakim
(3/167). Kuma Tirmidhi
ya infanta shi.
Za mu ci gaba in Allah

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s