ME YA FARU A KARBALA? 2

ME YA FARU A
KARBALA? 2
Wane ne YAZIDU?
Sunansa YAZIDU Dan
Mu’awiyah Dan Sakhr
(Abu Sufyan) Dan Harb
Dan Umayyah Al
Umawy Al Qurashie.
Ana yi masa alkunya da
Baban Khalid.
Mahaifiyarsa ita ce
Maisun ‘yar Bahdal daga
kabilar Kalbu, daya daga
cikin kabilun Kuraishawa
masu karfi a wancan
lokaci. Ta rabu da
mahaifinsa tana dauke
da cikinsa, sai ta yi
mafarkin wata ya fito
daga jikinta. Masu
Fassara suka ce mata in
har mafarkinki ya
tabbata za ki haifi sarki.
Hakan kuwa aka yi.
An haifi YAZIDU a
shekara ta 26H a
zamanin halifancin
sayyidina Usmanu Dan
Affan. YAZIDU ya tashi
a gidan sarauta, domin
ko da aka haife shi
mahaifinsa yana
gwamnan Sham. Ya
samu tarbiyyar jihadi
domin tun yana matashi
dan shekaru 24 ya
jagoranci runduna mafi
girma da ta fatattaki
Rumawa kuma ta
kwace hedikwatarsu
“Qustantiniyah”. Daga
nan ne kuma sunan
YAZIDU ya fara fitowa
har ya yi tashe a
tsakanin matasa. A nan
ne kuma ya samu tasa
daraja daga Hadisin
Ummu Haram bint
Malhan Matar sayyidina
Ubada bin As Samit
wacce ta ce ta ji
Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wa Alihi Wasallam
na cewa “Rundunar
farko da zasu yi yaki a
teku daga cikin
al’ummata Allah ya
gafarta masu”. Ta ce,
Manzon Allah ina cikin
su? Ya ce, eh. Kina
cikinsu. Sannan ya ce
“Rundunar farko da
zasu ci birnin Qaisar
daga cikin al’ummata su
ma Allah ya gafarta
masu”. Ta ce, Manzon
Allah ina cikin su? Ya ce,
a’a. (Sahihul Bukhari,
Hadisi na 2924).
Wannan Hadisi ya hada
falalar YAZIDU da
babansa gaba daya.
Domin kuwa babansa
Mu’awiyah ne ya fara
jagorantar Rundunar
farko da ta yi jihadi da
Rumawa a teku,
zamanin sarki Usmanu
a shekara ta 27H. A
cikin rundunarsa kuwa
har da irin su Miqdadu
Dan Amru da Shaddadu
Dan Ausu da Abu Dharril
Gifari da Ubada Dan
Samit tare da wannan
matar da ta gamu da
ajalinta kai tsaye bayan
gama yakin.
Shi kuma YAZIDU shi ne
ya ci babban birnin
Qustantiniyah a shekara
ta 52H. Qustantiniyah
kuwa ita ce birnin Qaisar
a zamanin Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wa Alihi
Wasallam. A cikin sojojin
wannan runduna tasa
kuwa har da wasu
fitattun sahabbai irin su
Ibnu Umar da Ibnuz
Zubair da Ibnu Abbas da
Abu Ayyub al Al Ansari,
mai masaukin Manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wa
Alihi Wasallam, Wanda
kuma ya cika kafin
kammala yakin.
(Duba Fathul Bari na Al
Hafizh Ibnu Hajar 6/120
da kuma Al Bidayah
Wan Nihaya na Ibnu
Kathir 6/249).
Kafin haka YAZIDU ya yi
Amirul Hajji na musulmi
baki daya a shekara ta
50H.
Ba zamu yi mamaki ba
idan muka ga
mahaifinsa ya zabe shi
a matsayin Yarima. To,
amma ko mene ne ya
sa aka zabe shi alhalin
akwai wadanda suka fi
shi irin su HUSAINI jikan
Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wa Alihi
Wasallam?
Wannan ita ce
tambayar da zamu
amsa a nan gaba
Sa’annan mu dawo ma
rikicin mawallafa da
takin sakar su a kan
wannan dan taliki
YAZIDU kafin mu
fantasia cikin maganar
rikicin da ya hada shi da
YAZIDU Wanda a
sanadiyyarsa Allah ya
ba shi shahada.
Allah ya kai mu gobe

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s