ME YA FARU A KARBALA? 3 (Dr mansur sokoto)

ME YA FARU A
KARBALA? 3
Rikicin mawallafa a
game da YAZIDU
Yana da wahala kwarai
ka samu mutum a tarihi
wanda aka yi ta takin
saka a kansa, ruwayoyi
kuma suka rinka cin
karo da juna a kan sa
kamar YAZIDU. Yawan
masoyansa masu
yabon sa, da makiyansa
masu sukar sa na
sanya mai karatun tarihi
a cikin rudani ba na
wasa ba. Zan bada
wasu ‘yan misalai don
mu gane wannan.
Misali na Daya: A yayin
da Ibnu Abdi Rabbihi ya
ruwaito cewa, YAZIDU
ya damu da nadin da
aka yi masa a matsayin
kwamanda wajen yakin
Qustantiniyah kuma har
ya zargi babansa da son
halaka shi. Kai har ma
wai zambo ya yi ma
baban nasa! (Duba Al
Iqdul Farid na Ibnu Abdi
Rabbihi 4/367)
Shi kuma Ibnu Tolon
cewa ya yi YAZIDUn ne
ya nemi a ba shi
wannan mukami.
Saurari ruwayarsa
kamar haka:
Watarana Fakhitah
matar Mu’awiyah ta
zagi YAZIDU a gabansa
sai ya ce mata, ai
YAZIDU ya fi danki
Abdullahi. Da ta
gardamta ma sa sai ya
aika aka kira Abdullahi a
gaban ta don ya nuna
mata banbancin su. Da
Abdullahi ya zo sai ya
tambaye shi in yana da
wata bukata. Abdullahi
sai ya kada baki ya ce,
baba jaki nake so ka
saya min! Mu’awiyah ya
ce, to, kin ga irinta! Ai
kai ma jaki ne. Tashi ka
ba ni wuri. Nan take ya
aika aka kira masu
YAZIDU, sai ya yi masa
irin tayin da ya yi ma
dan uwansa. YAZIDU
sai ya fadi ya yi sujada
don godiya ga Allah. Da
ya daga kansa sai ya
taya babansa murna da
Allah ya nuna masa
wannan rana da ya
amince ma dan cikinsa.
Sannan ya ce masa,
bukatocin dan sarkin
musulmi su ne kamar
haka:
1. Ka shugabantar da ni
a wajen Jihadi
2. Idan kwarewata ta
bayyana sai ka yi mini
Amirul hajji
3. Ka fada ma jama’a na
nemi ayi masu karin
albashi kuma ka aminta
4. Ka yanka ma marayu
sabon tsarin albashi
5. Daga baya sai ka
ayyana ni a matsayin
yariman da zai gaje ka
(Duba littafin Qaidus
Sharid Min Akhbari Yazid
na Ibnu Tolon, shafi na
25-26).
Duda irin banbancin da
ke tsakanin wadannan
ruwayoyi guda biyu. A
ta farkon an nuna
YAZIDU a matsayin
wani wawa da bai san
ciwon kansa ba, har
zambo yake ma
mahaifinsa a kan tura
shi yaki. A ta biyun
kuma sai ya fito wani
sadauki, jarumi, mai
tarin basira da hankali,
ga nazari da iya siyasa.
To, wace riwaya zamu
dauka?
Zamu ci gaba da kawo
misalai irin wadannan
don mu tabbatar da
yadda marubuta suka
sha banban wajen
bayyana wannan dan
taliki sannan daga bisani
mu fadi ra’ayinmu a kan
sa. Bayan haka sai mu
koma maganar siyasa,
ina nufin nadinsa da
Abubuwan da suka
haifu bayan sa.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out / Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out / Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out / Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out / Change )

Connecting to %s