ME YA FARU A KARBALA? 5 (Dr mansur sokoto)

MEYA FARU A
KARBALA? 5
Har yanzu dai a kan
Yazid
Mun riga mun fadi cewa,
akwai rikici mai yawa a
tsakanin mawallafa
game da sha’anin
Yazidu har mun soma
bada wasu ‘yan misalai
a kan haka.
Daga cikin abin da ke
nuna haka zamu ga
zancen wasiyyar da
Mu’awiyah ya yi masa
Dinawari da Ibnu Abdi
Rabbihi duk sun ruwaito
ta. Amma Dinawari
cewa ya yi Mu’awiyah
ya yi masa wannan
wasici ne baka da baka,
amma shi Ibnu Abdi
Rabbihi sai ya ce
Mu’awiyah ya rubuta ta
ne a yayin da Yazidu
yake can yana farauta
da wasanni kuma bai
dawo ba sai bayan
mutuwar uban nasa.
Duba Al Iqdul Farid na
Ibnu Abdi Rabbihi
(4/372) da kuma Al
Akhbarut Tiwal na
Dinawari, shafi na 225.
To, wace ruwaya ce ta
gaskiya a cikin
wadannan?
Game da zancen kashe
HUSAINI ma riwayoyin
mutanen Kufa (Iraq)
sun karkata ga zargin
Yazidu da bada umurnin
a yi wannan danyen aiki.
Wasu riwayoyin kuma
cewa suke ya barrantar
da kansa har da
rantsuwa cewa bai ce a
kashe shi ba, ya dai ce a
dakatar da shi ne daga
yunkurinsa na juyin
mulki.
Haka ma game da
iyalansa, an ce ya
wulakanta su, an kuma
ce ya girmama su.
Akwai ma riwayoyin
Abu mikhnaf da ire-
irensa masu cewa ya
dauki karen gamba ya
rinka sokawa a cikin
hancin Husaini lokacin da
aka zo masa da kansa.
Yana wulakanta shi
yana Jin dadi. Alhali
akwai riwayoyi da suka
ce kuka ya rinka yi har
da la’antar gwamnan
Kufa, yana cewa bai
mutunta Manzon Allah
ba ga iyalansa. Kuma
duk wadannan akwai su
a littafan tarihi irin na su
Tabari da Ibnu Sa’ad da
makamantansu. Zamu
dawo ga wannan
maganar idan mun zo
zancen Karbala.
Amma kafin mu
karkare magana kan
Yazidu yana da kyau a
san abubuwan da
Ahlussunna ke la’akari
da su wajen yanke
hukunci a kan kowane
mutum.
1. Musulmi duk yana da
alfarmar da ya kamata
a kiyaye masa. Ba ya
halasta a shiga rigar
mutuncinsa sai da dalili
tabbatacce.
2. Kuskure a wajen
kyautata ma musulmi
zato ya fi alheri bisa yin
daidai wajen cin
zarafinsa. Domin a na
farkon, Allah na iya yi
ma uzuri, amma a na
biyun mai alhaki zai ja
alhakinsa.
3. Wanda bai gani da
idonsa ba, ko ya ji da
kunnensa, to idan ya ba
da sheda, shedarsa ba
kammalalliya ba ce,
domin ba ta ginu a kan
ilmi ba. Kamar yadda
Allah ya ce: ﺍﻻ ﻣﻦ ﺷﻬﺪ
ﺑﺎﻟﺤﻖ ﻭﻫﻢ ﻳﻌﻠﻤﻮﻥ. ﺳﻮﺭﺓ
ﺍﻟﺰﺧﺮﻑ: ٨٦
“Sai dai wadanda suka
yi shaida da gaskiya,
kuma suna sane (da
abin da suka yi sheda a
kansa).
4. Maganar abokin gaba
ba a karas da ita sai an
tabbatar da tsarkin
zuciyarsa da gaskiyar
harshensa. Amma
abokin gaba da aka san
shi da shara ta to sai
anyi nazari an duba
sauran ruwayoyi
sannan a yanke hukunci.
5. A kan kowane
mutum akwai abinda
yake yuwa a jingina
masa. Ko a cikin
abokanenka da zaran an
ce wane ya yi kaza,
zaka yi fararat ka ce
a’a. Ba dai wane ba.
Wani kuma da zaran an
fada zaka ce karamin
aikinsa ne. Wannan fa
tun baka bincika ba
kenan, to ina ga ka
tambaye shi ya karyata
zargi? Wannan shi ya sa
yake da kyau mu san
cikakken tarihin mutum
kafin mu dau matsayi a
kan duk wani labari da
aka jingina masa. Kuma
wannan shi ya sa masu
hankali ke sanya nazari
kan almajiran Annabi
Sallallahu Alaihi Wa Alihi
Wasallam la’akari da
dinbin yabon su da
muke ta karantawa
kullum a cikin maganar
Allah. Wanda Allah ya
saukar da
dawwamammen littafi
ana karantawa a kan
yabon sa, zai yiwu ya
zama shi ne abin zargi?
6. Mutum ya kan iya yin
laifi kome girmansa
amma ya kasance ya
tuba daga bisani ko ya
gamu da wani hukuncin
Allah a nan duniya
wanda zai shafe
laifinsa, ko ladarsa ta
rinjayi zunubinsa, ko ya
samu gamon katar da
ceton Manzon Allah, ko
Allah ya dubi tsarkin
zuciyarsa ya yafe
kurensa ko ya yafe
masa laifinsa. Don haka
ya sa Ahlussunna ba su
zagi, ba su la’anta
domin ba su son shiga
tsakanin mutum da
mahaliccinsa.
Wadannan ka’idoji ne da
suka shafi Kowa da
Kowa. Ba ina nufin
Yazidu ba. Amma
maganar Yazidun da
nasa laifi tana nan tafe.
Ku kara biyo mu.
Ma’assalam.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s