ME YA FARU A KARBALA? 6 (Dr mansur sokoto)

ME YA FARU A
KARBALA? 6
Matsayin Sayyidina
Hussaini game da
gwamnatin Yazid
Kafin mu je can, yana da
kyau muyi waiwaye
game da gwamnatin da
ta kawo shi mulki, ina
nufin gwamnatin
babansa Mu’awiyah.
Abinda aka sani ne
cewa, har zuwa lokacin
wafatin sayyidina Ali ba
wani nadadden sarkin
musulmi in ba shi ba.
Babu kuma wanda yake
da’awar son ya karbi
wannan mukami daga
wurinsa. Amma bayan
da sayyidina Ali ya
samu shahada ta
hannun Abdurrahman
bin Muljam (daya daga
cikin ‘yan Khawarij
wadanda suka yi
tawaye daga
rundunarsa – Shi’arsa),
sai mutanen Iraq suka
nada dansa AlHasan, a
yayin da mutanen Sham
suka nada gwamnansu
Mu’awiyah. Ba kuma
wani bangaren da ya
tuntubi wani a wajen
aiwatar da muradinsa.
Wannan shi ne karo na
farko a tarihin
musulunci da aka samu
sarkin musulmi biyu a
lokaci guda. Don
warware wannan
takaddama ne Al Hasan
Radiyallahu Anhu ya
gayyaci Mu’awiyah da
kansa don su sasanta,
daga karshe kuma ya
sauka ya gabatar da
Mu’awiyah, ya kuma
sanya mutanen Iraqi yin
haka. Wannan shi ya
tabbatar da busharar da
Manzon rahama ya yi a
kansa cewa, jikan nan
nawa zai zama
shugaba, kuma Allah zai
kawo karshen wata
tarzoma da zata barke
a tsakanin manyan
bangarori biyu na
musulmi. Sahihul Bukhari
(7/74) da Al Jami’ na
Tirmidhi, hadisi na 3775.
HUSAINI Radiyallahu
Anhu ya Lizimci kawaici
game da abinda wansa
ya yi amma a zuciyarsa
bai ji dadi ba kamar
yadda akasarin
mutanen Iraqi ba haka
suka so ba amma dai ya
daure ya yi mubaya’a
tare da sauran jama’a.
Ba wani rahoto da ya
nuna ko sau daya ya
taba nuna ma
Mu’awiyah rashin goyon
bayansa ga
gwamnatinsa kamar
yadda shi ma Al Hassan
din ya yi. Sukan karbi
kyautarsa, suna
mutunta shi tare da bin
umurninsa. Kusan ma
duk yakokan jihadi da
aka yi a zamaninsa tare
da su aka yi. HUSAINI
ma yana cikin rundunar
Yazidu wadda ta ci
Qustantiniyah. Shekaru
goma ne Al Hasan ya yi
a karkashin mulkin
sayyidina Mu’awiyah,
Husaini kuma ya kara
wasu goma bayan haka.
A cikin wasiyyar da Al
Hasan ya bar ma
kaninsa HUSAINI ya
gargade shi da kada ya
rudu da mutanen Iraqi.
Ya ce masa ka san
wahalar da mahaifinmu
ya sha a hannunsu,
kuma ni ka ga irin
tozartawar da na gani
hannunsu wadda ta sa
na yada mangoro na
huta da kuda. Don haka,
kada ka yarda su sake
janka cikin wannan
lamari. Ga dukkan alamu
Allah ba zai hada
Annabta da halifanci a
gidanmu ba. Al Imam At
Tabari ya kawo wannan
wasiyyar a tarihinsa.
To, ko sayyidina Husaini
ya rike wasicin
yayansa? Amsa ita ce
eh, ya rike wasicinsa
amma sai dai akwai
wasu abubuwa da suka
biyo baya. Sai a ci gaba
da biyo mu domin jin
abinda ya faru.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s