ME YA FARU A KARBALA? 7 (Dr. Mansur sokoto)

ME YA FARU A
KARBALA? 7
Nadin Yarima Mai
jiran gado
Kamar yadda muka fadi
a baya, HUSAINI
Radiyallahu Anhu ya bi
umurnin wansa Al
Hasan wajen yin
biyayya ga gwamnatin
sayyidina Mu’awiyah har
sanda Allah ya kawo
karshenta a shekara ta
60H. To, amma kafin
haka Mu’awiyah ya
ayyana Yazid a
matsayin Yarima wanda
zai gaje shi idan ajalinsa
ya cim masa. A nan ne
Husaini ya cije ya ce ba
zai bada goyon baya ba.
Husaini ba shi kadai ya
dauki wannan matsayi
ba. Akwai masu
mutane uku da suka
hada da Abdullahi Dan
Umar da Abdurrahman
dan Abubakar da kuma
Abdullahi dan Zubair. Su
hudun basu bada goyon
baya ba, kuma
dukkansu ‘ya’yan
manya ne kamar yadda
muka gani. Ko
wannensu babansa na
cikin mutane goman da
aka yi amanna ‘yan
aljanna ne don
sanarwar da bakin da
ba ya karya ya bayar a
kansu. Amma HUSAINI
ya dara sauran don shi
yana da tasa bushara
ta kashin kansa. Amma
dai duk da haka wannan
lamarin ya ci gaba yadda
aka tsara shi.
Me ya sa sayyidina
Mu’awiyah ya nada
Yarima? Kuma don me
ya zabi dansa YAZIDU?
Amsa ita ce, Sanin gaibu
sai Allah. Amma dai ba
za a rasa dayan
wadannan abubuwa ba
ko dukansu bisa ga
hasashen masu iya
kyautata masa zato a
matsayinsa na
sakataren Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wa Alihi
Wasallam, wadanda ba
su dauke da “Gilli” a
zukatansu dangane da
shi. Ga su:
1. Jin tsoron afkuwar
fitina a tsakanin
musulmi bayan cikawar
Mu’awiyah la’akari da
sabon yanayin da
al’umma take ciki,
musamman bayan an
fadada biranen
musulunci, mutane da
dama sun shigo
wadanda ba su da
kyakkyawar manufa ga
ci gaba da daukakar
addini.
2. Kwarewar da YAZIDU
ya nuna a sha’anin
shugabanci da rikon
jama’a. Musamman da
yake ya yi Amirul Hajji
shekara goma kafin
haka, ya kuma jagoranci
mafi girman rundunar
da ta kwace
hedikwatar babbar
super power ta duniyar
wancan lokaci.
3. Kasancewar Yazidu
shi ne wanda zai fi
samun goyon bayan
mutanen Sham, cibiyar
halifanci ta wancan
lokaci saboda matsayin
mahaifinsa wanda yake
da gagarumin goyon
baya a can tun da ya yi
gwamna tsawon
shekaru ashirin, har
kuma yanzu da ya hau
kujerar sarkin musulmi
wasu tsawon shekaru
goma sha biyar.
Ta bangaren masu
ganin laifinsa kuwa sun
zarge shi ne da nuna
son kai, da sha’awar ya
mayar da mulkin
musulunci gado, abinda
duk magabatansa ba su
yi kokarin yi ba. Shi ma
sayyidina Ali ba shi ya
ce a nada dansa ba,
shawara ce ta gudana a
tsakanin jama’arsa
bayan wafatinsa.
To, ko ya lamarin yake
dai, mutanen Sham sun
bada hadin kai sosai
wajen aiwatar da
wannan muradi. Su
kuma mutane hudu da
basu yi mubaya’a ba, an
kyale su hakanan ba
wata takurawa ko
tsangwama da aka yi
musu.
Wannan duka ya faru ne
Mu’awiyah Radiyallahu
Anhu yana da ransa da
lafiyarsa a shekara ta
55H. Bayan da Allah ya
yi masa rasuwa kuma
dukkan masu fada a ji
sun yi mubaya’a kai
tsaye ga Yazidu in
banda biyu daga cikin
wadancan da muka
ambata. Shi dai
Abdurrahman Dan
sayyidina Abubakar
Allah ya yi masa cikawa
kafin haka. Shi kuma
sayyidina Abdullahi Dan
Umar ya hakura ya yi
mubaya’a tare da su
Ibnu Abbas da sauran
mutane. Ya ce, daman ni
ban yarda ayi sarki biyu
ne ba, amma yanzu
tunda mahaifinsa ya
mutu, kuma al’umma ta
taru ta amince da
abinda aka yi to, ni ba ni
da jayayya. Wadanda
suka rage kenan su ne
HUSAINI da Ibnuz
Zubair, Allah ya yarda
da su.
Sauran bayani sai ku
tare mu a gaba.
Wassalam

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s