ME YA FARU A KARBALA? 8 (Dr. Mansur sokoto)

ME YA FARU A
KARBALA? 8
Yarima Ya Zama
Sarki
Tun daga hudubar farko
da Yazid ya yi ya fara
sauya siyasar mulki
daga ta babansa kamar
yadda hausawa suka ce
Sarki Goma Zamani
Goma. Yazid ya soma da
jajanta ma jama’a
game da mutuwar
sarkin musulmi
Mu’awiyah, Sannan ya
bada sanarawar game
ma mutane albashin
wata uku (a wancan
lokaci talaka albashi
gwamnati ke masa,
sunnar da sarkin
musulmi Umar Dan
Haddabi ya fara),
Sannan Yazidu ya ce ya
jinkirta yaki a bangaren
teku saboda shigowar
lokacin sanyi. Daga
juyayi sai mutane suka
koma murna.
Ba a Sham kadai aka yi
wa Yazidu mubaya’a ba,
a’a har da Makka da
Madina da sauran
garuruwan musulmi.
Amma mutum biyu da
muka sani cewa ba su
yi mubaya’a ba suna
nan a kan matsayinsu.
Kuma ganin kamar
gwamnan Madina Al
Walid bin Utbah zai yi
yunkurin tilasta su sai
suka sauya mazauni su
biyun suka koma Makka.
Hussaini Radiyallahu
Anhu ya kwashe duk
iyalansa ya tafi da su, in
ban da kanensa
Muhammad bin Ali (Ibnul
Hanafiyyah) shi kam
daman ya yi mubaya’a
kuma ya shawarci
Husaini da ya canza
ra’ayi shi ma ya yi.
Yin wannan hijira da
sayyidina Husaini ya yi
sai ta ba mutanen Iraqi
irin damar da suke
nema. Take kuwa suka
fara aike masa sakonni
suna nuna masa
cancantar ya dawo
garinsu. Wasa wasa sai
magana ta girma,
Iraqawa sun dau
alkawalin tumbuke
gwamnatin Yazidu da
kafa sabuwa da sabon
sarki shi ne Husaini.
Masu lura da al’amurra
sun ga abinda ke kai da
komo, kuma sun bada
shawarwarin da ya
kamata. Abdullahi bin
Abbas cewa ya yi, a
ra’ayina ya kamata
mutanen Iraqi su fara
cire gwamnansu su
damka maka kujerarsa
idan har da gaske suke
yi. In ya so sai ka fara
daga can. In ba haka ba
ba na ganin ya kamata
ka bar Makka saboda
wadannan mutane
mayaudara ne.
HUSAINI ya aiki
kanensa Muslim bin Aqil
bin Abi Talib don ya
bincika masa gaskiyar
mutanen. Da tafiya ta yi
tafiya ya aiko a fada
ma Husaini tafiyar tana
da wahala sosai yana
rokon ya bar shi ya
koma Makka sai Husaini
ya roke shi ya hakura ya
ci gaba da tafiya. Isar
sa Kufa ke da wuya sai
yan Shi’ah suka kewaye
shi, suka jaddada
mubaya’arsu ga Husaini
ta hannunsa. Kimanin
mutane 18,000 ne suka
dau alkawari ga Allah na
kare HUSAINI. Ganin
haka sai Muslim ya
tayar da manzo na
musamman don ya
sanar da shi abinda ake
ciki, alabashi shi kuma
ya kama hanya ya iso.
Sai dai kamar yadda
zamu gani nan gaba duk
wannan yaudara ce
kawai ba maganar arziki
ba. Shi kansa Muslim za
a kashe shi a fili ko
dangwara fuskar wani
ba ayi ba.
A Makka dai mutane
masu dinbin yawa ne
suka shawarci Husaini
da kada ya dauki
wannan mataki. Cikinsu
har da sahabbai irin su
Jabir Dan Abdullah da
Abu Sa’id Al Khudri da
Abu Waqid Al Laithi da
Umar bin Abdirrahman
bin Al Harith da Ibnu
Abbas dai sauran su.
Anya kuwa wadannan
shawarwari da nasihu
sun yi amfani? Babu
shakka HUSAINI ya
saurari wadannan
shawarwari da zuciya
wankakka sai dai
Kaddara ta Riga fata!
Zamu ci gaba gobe in
sha Allah.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s