ME YA FARU A KARBALA? 9 (Dr. Mansur sokoto)

ME YA FARU A
KARBALA? 9
An ci gaba da
shawartar Husaini
Kamar yadda muka gani
a baya mutanen Iraqi
sun riga sun bada
amincin Allah a kan
tarbon sayyidina Husaini
da halifantar da shi a
madadin Yazid. Kuma
sun aike masa wasiku
masu dinbin yawa a kan
haka. Haka ma zuwan
da Muslim bin Aqil ya yi
bai sa liki ya balle aka
gano mugun nufinsu ba,
amma dai masu nazari
sun yi ta ba Husaini
shawara kada ya
amince musu. Akwai
kuma wadanda suka
aike masa da wasiku na
rarrashi da ban hakuri
don hana shi fita kamar
Abdullahi bin Ja’afar bin
Abi Talib da Amru bin
Sa’id bin Al Ass da wata
mashahuriyar malamar
hadisi ta wancan lokaci
ana ce da ita Amrah.
Shi Abdullahi bin Umar
wanda da farko suka
dauki matsayi daya da
Husaini a yanzu sai da
ya bi Husaini ko bayan
fitar sa yana rarrashin
sa kan ya dawo.
Kwanan sa biyu a tare
da shi a kan hanya yana
kokarin shawo kansa,
yana ce masa “ka tuna
rashin kirkin mutanen
Iraqi da rashin cika
alkawarinsu. Wace irin
wahala ce mahaifinka
bai sha a hannunsu ba?
Kuma wace irin
tozartawar ce basu yi
ma yayanka ba?” Daga
karshe dai Husaini ya
dauko tulin takardunsu
ya nuna masa. Da Ibnu
Umar ya hakikance ba
zai iya shawo kansa ba
sai ya rungume shi yana
bankwana da shi, har ya
fadi wata kalma mai
ban tausayi wadda ke
nuna ya hakikance
Husaini ba zai kai labari
ba. Yana mai zubar da
hawaye ya ce masa
ﺃﺳﺘﻮﺩﻋﻚ ﺍﻟﻠﻪ ﻣﻦ ﻗﺘﻴﻞ
“Ina ba Allah kalihunka
ya kai wanda za a
kashe”!
Martanin da Husaini
Radiyallahu Anhu yake
maida ma duk masu ba
shi shawara shi ne
“Allah ya saka ma da
alheri. Na fahimci duk
abinda kake nufi na
shawara da nasiha. Ina
gode ma a kan haka.
Abinda Allah ya nufa
kuwa shi zai faru ko na
yi aiki da shawararka ko
ban yi ba”.
Idan mutum ya
kwatanta matsayin
Husaini da na dan
uwansa Al Hasan zai
sha mamaki. Al Hassan
nadadden sarki ne da
‘yan Shi’ar mahaifinsa
suka taru suka nada shi
bayan cikawar mahaifin
nasa. Akalla yana tare
da runduna ta kai
mayaka 100,000. Da ya
so zasu yi shekaru ana
yaki da Mu’awiyah da
jama’arsa. Amma sai ya
fifita zaman lafiya a
kan zubar da jinainan
musulmi. Don haka, ya
nemi Muawiyah suka
sasanta, ya dauki
ragamar al’umma ya
rataya masa, kuma ya
sa duk mutanensa suka
yi mubaya’a. Da haka
sai al’umma ta samu
kwanciyar hankali akalla
na tsawon shekaru 20
da Muawiyah ya yi a kan
karagar sarauta. Amma
shi Husaini saboda
hukuncin Allah bai kalli
irin abinda yayansa ya
kalla ba da aka zo
wannan lokaci. Domin ya
fito zuwa Kufa ba shi a
tare da kowa in banda
iyalansa. Wadanda ya
dogara ga
gudunmawarsu kuma
ba masu iya fidda suhe
wuta ne ba. Dukansu
(Hasan da Husaini) sun
yi ijtihadi ne. Kuma dole
ne dayansu ya zama
daidai, daya a kan
kuskure. Sai dai su ‘yan
Shi’ah sun ce dukansu
ma’asumai ne da ba sa
tuntube. To, ko me
zasu ce a kan wannan?
Zamu yi maganar fitar
Husaini zuwa ga
kaddarar Allah. Ku biyo

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s