ME YA FARU A KARBALA? 10 (Dr. Mansur sokoto)

ME YA FARU A
KARBALA? 10
Husaini Ya Kama
Hanyar Kufa
Safiyar 8 ga watan Dhul
Hajji a shekara ta 61H
ita ce ranar da alhazai
suka kama hanyar
zuwa Minna don fara
aikin hajji. Ita ce kuma
ranar da kaddarar Allah
ta gargada Husaini da
iyalansa zuwa darajar
da madaukakin sarki ya
ajiye masu ta samun
shahada a Karbala. AL
BIDAYAH WAN NIHAYA
na Ibnu Kathir (8/171).
A kan hanyarsa ta
zuwa Iraqi sayyidina
Husaini ya gamu da
shahararren mawakin
nan Firazdaq, ya
tambaye shi labarin inda
ya fito, sai ya ce Kufa.
Da ya tambaye shi halin
da ya baro a can sai
Firazdaq ya ce masa,
“Na bar zukatan
mutane na tare da kai,
makamai na ga masu
mulki, sanin gaibu na
wurin Allah”. Da ya
karasa gaba kuma sai
ya gamu da Hurru bin
Yazid At Tamimi wanda
ya fito fili ya ba shi
shawarar ya koma
Makka. Har sayyidina
Husaini ya karkata ga
wannan ra’ayi sai kuma
hukuncin Allah ya
rinjaya, Husaini ya ci
gaba da tafiyarsa.
A wani wuri kuma da ya
yada zango sai ya hadu
da Abdullahi bin Muti’ shi
ma yana dawowa daga
Kufa. Dan Muti’u bai yi
wata wata ba ya
shawarci Husaini da
komawa Makka yana ce
masa “Ka ji tsoron Allah
ya kai Husaini, ka tsare
martabar gidan Manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wa
Alihi Wasallam kada ka
sa a keta ta. Kada ka je
Kufa, kada kuma ka
gitta ma mulkin
wadannan mutane. Idan
ka yi haka wallahi zasu
kashe ka. Allah ne kuwa
kadai ya san karshen
wannan lamari idan ya
faru”. AT TARIKH AL
ISLAMI na Mahmud
Shakir (3/124).
Halin da ake ciki a can
Kufa:
Fitar Husaini daga
Makka ke da wuya sai
labari ya game
garuruwa. Mutane kuwa
suka yi ta ce-ce-kuce a
kan wannan magana.
Da rahotanni suka isa
wurin Yazid a kan
wannan batu sai ya
raina kokarin
gwamnansa sahabi
Nu’uman bin Bashir
Radiyallahu Anhu ta
yadda har ya bari aka yi
mubaya’a ga wakilin
Husaini a cikin garinsa
kuma ko labari bai aika
masa ba. Don haka sai
ya canza shi da
gwamnan Basrah domin
ya magance masa
wannan matsala.
Da sabon gwamna
Ubaidullahi bin Ziyad ya
isa Kufa bai samu wata
wahalar gano Muslim bin
Aqil ba, inda ya sa aka
kamo shi tare da mai
masaukinsa Hani’ bin
Urwa Al Muradi. Kamar
dai da gaske mutanen
Kufa sun nuna alhininsu
a kan kama wadannan
mutane har suka yi jerin
gwano a kan titunan
birni kuma suka wa
gidan gwamna zobe
suna neman a sake su.
An kiyasta wadanda
suka shiga wannan jerin
gwano da mutane 4000
daga Asalin 18,000 da
suka yi masa mubaya’a.
Ba kuma wani matakin
da aka dauka sai ga su
kafin yammaci sun
dawo kimanin 500.
Bayan haka ne
Ubaidullahi ya bukaci
ganawa da shugabannin
kabilu wadanda ya yi
shawara da su a kan
wannan lamari kuma
suka kwantar da
hankalinsa cewa su
zasu shawo masa kan
wannan matsala. A cikin
duhun dare ne suka
rinka sulalewa har suka
watse baki daya. Abin
takaici da ban mamaki
shi ne yadda aka kashe
shi Muslim a fili amma
mutanen garin nan ba
su ko tada jijiyar wuya
ba. Inna Lillahi Wa Inna
Ilaihi Raji’un.
Wannan ya faru ne a
ranar Arafat ta wannan
shekara da muke
magana a kai. Kwana
daya kenan kacal da
fitowar yayansa
sayyidina Husain. Wayyo
Allah, ina wayar salula
da zata kai ma
maigidana Husaini
wannan labari? Ina fax
da telex da telegram?
Duk babu su a wancan
lokaci. A takaice dai
Husaini bai san wainar
da ake toyawa a Kufa
ba har sai da ya iso gat
da wannan gari inda ya
gamu da dan sakon
Muslim wanda ya aike
shi bayan ganin
al’amurra sun rikice don
ya sanar da shi abinda
ake ciki. AL ISABA FI
MA’RIFATIS SAHABA,
na Ibnu Hajar (1/228).
Zamu ci gaba in sha
Allah.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s