ME YA FARU A KARBALA? 11 (Dr. Mansur sokoto)

ME YA FARU A
KARBALA? 11
Husaini Ya Isa
Karbala
Da sayyadi Husaini ya
kusa isa Kufa sai ya
gamu da Umar bin Sa’ad
dauke da sakon kaninsa
Muslim wanda sai yanzu
ne ya san cewa an
kashe shi. Muslim ya
nemi Husaini da ya
koma abinsa tunda
mutanen Kufa ba da
gaske suke ba. Shi dai
Umar bin Sa’ad daman
yana cikin ‘yan Shi’ar Ali
kamar yadda shi ma
wannan sabon gwamna
Ubaidullahi bin Ziyad
yake. Duba KITABUR
RIJAL na TUSI Shafi na
54 don haka Bin Sa’ad
sai ya bada labarin
kashe Muslim yana kuka
ta yadda ya zaburar da
‘yan uwansa, ya kuma
ja hankalinsu ga daukar
fansa. Husaini ya so ya
komawarsa amma
sauran dangi na ganin
dole ne a isa Kufa zuwa
daukar fansar jinin dan
uwansu.
Duk mai hankali zai iya
lura da hannun kaddara
a cikin wannan lamari.
Domin kuwa ya za a iya
daukar fansar wanda
hukuma ta kashe shi?
Kuma a kan wa za a
dauki fansa? Sannan su
waye zasu dau fansar?
Husaini ba wani shirin
yaki da ya zo da shi. Bil
hasili ma kaffatanin na
tare da shi mata ne da
kananan yara.
Abinda ya fi kome ban
mamaki shi ne
dawowar Umar bin
Sa’ad bayan ya koma
Kufa, a yanzu wai ya zo
ne yana jagorancin wani
ayari na dakaru 4000
dauke da umurnin
Ubaidullahi bin Ziyad na
a kama Husaini! Sun
tarar da Husaini ya
karaso hanyar Kufa har
ya sauka a Karbala.
Bayan wasu
muhawarori a tsakanin
su sayyidina Husaini ya
aminta da komawa inda
ya fito. Umar bin Sa’ad
ya ce, sai mun nemi
amincewar gwamna
Ubaidullahi.
Da farko da aka sanar
da shi, Ubaidullahi ya ce
ba damuwa a bar shi ya
komawarsa. Amma
wani fitaccen dan
Shi’ah, makiyin Allah,
maras imani, shine
Shamru bin Dhil Jaushan
wanda ya kasance cikin
sojojin sayyidina Ali
kamar yadda Shahrudi
ya fada a cikin littafinsa
MUSTADRAK ILMI
RIJALIS HADITH (4/224)
, wannan munafukin
dan Shi’an sai ya yi
fadanci zuwa ga
Ubaidullahi da cewa, ai
har yanzu Husaini na da
hadari ga mulkin Yazid,
domin akwai yiwuwar in
ma ya tafi ya dawo.
Don haka babu mafita in
ban da a kama shi.
Da aka ki karbar
bukatar Husaini ta
komawa Makka sai ya
ba da wasu zabi guda
biyu; ko dai ya tafi
wurin masu jihadi a
matsayin daya daga
cikin sojoji ko kuma ya
tafi wurin Yazidu da
kansa ya yi mubaya’a.
Amma dai duk
wadannan muradun
basu samu ba ﻟﻴﻘﻀﻲ ﺍﻟﻠﻪ
ﺃﻣﺮﺍ ﻛﺎﻥ ﻣﻔﻌﻮﻻ don
Allah ya zartar da
kaddarar da ya hukunta.
Ya zama dole bayan
haka ta faru Husaini ya
shirya don kare kansa
daga wulakanci. A nan
ne ya yi wata huduba a
daren Tasu’a wadda a
cikinta ya fada ma ‘yan
rakiyarsa cewa fa yana
ganin akwai arangama a
tsakaninsa da
wadannan mutane
gobe. Sannan ya yi izni
ga duk wanda ke da
bukatar juyawarsa ya
tafi. Nan wasu suka yi
amfani da wannan
dama kafin a wayi sun
tafi abinsu.
Wayuwar garin Ashura
Husaini ya shirya tare
da mutanen da basu
wuce 50 ba daga asalin
72 da ya fito da su
domin su fuskanci
rundunar gwamnatin
Ubaidullahi mai soji 4000.
Abin tambaya a nan shi
ne, ya aka yi aka samu
wannan adadin sojoji a
Kufa garin da yake na
Shi’ah ne zalla amma ga
su sun zo su yaki ko su
kama Husaini? Ina duk
magoya bayan da suka
sa hannu a kan
takarda? Ina masu
mubaya’a 18,000 da
suka damka hanayensu
ga Muslim dan Aqilu a
madadin Husaini?
Wannan shi ya sa
malaman Shi’a suka
tuhumci mabiyansu da
aikata danyen aikin da
zamu yi magana a kan
sa. Kafin mu kawo
maganganunsu bari mu
kammala fadin wannan
abin kunya, abin takaici
da ya cimma al’ummar
musulmi.
A lokacin da aka ja daga
tsakanin rundunonin
guda biyu, Shamru ne ya
bada koren haske sai
aka fara karawa. Kuma
akalla soji 88 sun
kwanta dama daga cikin
wannan tsinanniyar
runduna. Ganin irin
hasarar soji da suka yi
kuma ba wani alamun
saranda daga sayyidina
Husaini sai Zur’atu At
Tamimi wanda shi ma
dan Shi’ah ne ya kai
sara ga Husainin a
kafadarsa, Sinanu dan
Anas -wani dan Shi’ar
shi ma – ya kai ma
Husaini hari ga
makogaronsa, Sannan
ya sare shi a kirji. Kafin
Husaini ya kai kasa wani
shaidani ana ce masa
Khuli Al Asbahi – dan
Shi’ah – ya sa takobi ya
cire kansa. Kada Allah ya
yarda da su baki daya.
Zamu kawo sharhin
malaman Shi’ah kan
wannan lamari daga
littafansu Sannan mu je
birnin Sham don mu ji
yadda Yazidu ya tari
wannan mugun labari.
Ku ci gaba da biyo mu.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s