ME YA FARU A KARBALA? 12 (Dr mansur sokoto)

ME YA FARU A
KARBALA? 12
Wa ya kashe
sayyidina HUSAINI?
Bayan duk bayanin da
ya gabata na abinda ya
faru, muna son amsa
wannan tambaya. WA
YA KASHE SAYYIDINA
HUSAINI? Amma a
wannan karon littafan
Shi’ah kadai muke son
su bada amsa.
1. Ga abinda Allamah As
Sayyid Muhsin Al Amin
ya fada a cikin A’yanus
Shi’ah (1/34):
ﺑﺎﻳﻊ ﺍﻟﺤﺴﻴﻦ ﻋﺸﺮﻭﻥ ﺃﻟﻔﺎ
ﻣﻦ ﺍﻫﻞ ﺍﻟﻌﺮﺍﻕ، ﻏﺪﺭﻭﺍ ﺑﻪ
ﻭﺧﺮﺟﻮﺍ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺑﻴﻌﺘﻪ ﻓﻲ
ﺃﻋﻨﺎﻗﻬﻢ ﻭﻗﺘﻠﻮﻩ
“‘Mutane 20,000 daga
‘yan Iraqi sun yi ma
Husaini mubaya’a, sun
YAUDARE shi kuma
suka fito a kansa, alhali
mubaya’arsa na ga
wuyansu, kuma suka
kashe shi”.
2. Ga kuma abinda Hurru
bin Yazid – daya daga
cikin ‘yan rakiyar Husain
-ya ce ma rundunar da
take kokarin kashe
HUSAINI a Karbala:
ﺍﺩﻋﻮﺗﻢ ﻫﺬﺍ ﺍﻟﻌﺒﺪ ﺍﻟﺼﺎﻟﺢ،
ﺣﺘﻰ ﺍﺫﺍ ﺟﺎﺀﻛﻢ ﺍﺳﻠﻤﺘﻤﻮﻩ،
ﺛﻢ ﻋﺪﻭﺗﻢ ﻋﻠﻴﻪ ﻟﺘﻘﺘﻠﻮﻩ،
ﻓﺼﺎﺭ ﻛﺎﻻﺳﻴﺮ ﻓﻲ ﺃﻳﺪﻳﻜﻢ؟
ﻻ ﺳﻘﺎﻛﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻈﻤﺎ .
“Yanzu zaku kira
wannan bawan Allah na
kirki, sai da ya zo maku
sannan ku mika shi,
Sannan ku yi tsalle a
kansa don ku kashe shi,
har ya zama kamar
wani fursuna a
hannunku?! Kada Allah
ya shayar da ku ranar
kishirwa”. Duba AL
IRSHAD na Al Mufid,
shafi na 234 da I’LAMUL
WARA BI A’LAMIL HUDA
na Tabarsi, shafi na
242.
3. Sai kuma abinda
Tabrasi ya hikaito cewa
shi kansa sayyidina
Husaini yana cewa:
” ﺃﻟﻢ ﺗﻜﺘﺒﻮﺍ ﺇﻟﻲ ﺃﻥ ﻗﺪ
ﺃﻳﻨﻌﺖ ﺍﻟﺜﻤﺎﺭ ، ﻭ ﺃﻧﻤﺎ ﺗﻘﺪﻡ
ﻋﻠﻰ ﺟﻨﺪ ﻣﺠﻨﺪﺓ؟ ﺗﺒﺎً ﻟﻜﻢ
ﺃﻳﻬﺎ ﺍﻟﺠﻤﺎﻋﺔ ﺣﻴﻦ
ﺍﺳﺘﺼﺮﺧﺘﻤﻮﻧﺎ ﻭﺍﻟﻬﻴﻦ ،
ﻓﺸﺤﺬﺗﻢ ﻋﻠﻴﻨﺎ ﺳﻴﻔﺎً ﻛﺎﻥ
ﺑﺄﻳﺪﻳﻨﺎ ، ﻭﺣﺸﺸﺘﻢ ﻧﺎﺭﺍً
ﺃﺿﺮﻣﻨﺎﻫﺎ ﻋﻠﻰ ﻋﺪﻭﻛﻢ
ﻭﻋﺪﻭﻧﺎ ، ﻓﺄﺻﺒﺤﺘﻢ ﺃﻟﺒﺎً ﻋﻠﻰ
ﺃﻭﻟﻴﺎﺋﻜﻢ ﻭ ﺳﺤﻘﺎً ، ﻭ ﻳﺪﺍً
ﻋﻠﻰ ﺃﻋﺪﺍﺋﻜﻢ . ﺍﺳﺘﺴﺮﻋﺘﻢ
ﺇﻟﻰ ﺑﻴﻌﺘﻨﺎ ﻛﻄﻴﺮﺓ ﺍﻟﺬﺑﺎﺏ ،
ﻭ ﺗﻬﺎﻓﺘﻢ ﺇﻟﻴﻨﺎ ﻛﺘﻬﺎﻓﺖ
ﺍﻟﻔﺮﺍﺵ ﺛﻢ ﻧﻘﻀﺘﻤﻮﻫﺎ
ﺳﻔﻬﺎً ، ﺑﻌﺪﺍً ﻟﻄﻮﺍﻏﻴﺖ ﻫﺬﻩ
ﺍﻷﻣﺔ “
“Wai kam ba ku ne kuka
rubuto mana cewa,
‘ya’yan itace sun nuna
ba, kawai zamu zo mu
sami hadaddiyar
runduna? Allah ya abkar
da halaka a gare ku ya
ku wannan taron wofi!
Tunda kun kwala mana
kira a haukace, sannan
kuka daga mana
takobin da muke ganin a
hannunmu yake (Zaku
kashe mu da shi),
Sannan kuka hura
wutar da mun hasa ta
ne don makiyanmu
kuma makiyanku. A
yanzu kun zama masu
fada da masoyanku,
masu hada kai da
makiyanku. Kaico! A
Lokacin da kuke bamu
mubaya’a kun yo sulu
kamar fari amma a
yanzu kun kakkabe
hannayenku kamar ba
ku ne ba. Kai, Allah dai
ya nisantar da ku ya ku
dawagitan wannan
al’umma” Duba I’LAMUL
WARA na Tabarsi, shafi
na 949.
4. A nan ne kuma – in ji
Mufid – sayyidina
Husaini ya yi masu
bakar addu’a yana
cewa:
“ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺇﻥ ﻣﺘﻌﺘﻬﻢ ﺇﻟﻰ ﺣﻴﻦ
ﻓﻔﺮﻗﻬﻢ ﻓﺮﻗﺎً ﻭﺍﺟﻌﻠﻬﻢ
ﻃﺮﺍﺋﻖ ﻗﺪﺩﺍ ، ﻭ ﻻ ﺗﺮﺽ
ﺍﻟﻮﻻﺓ ﻋﻨﻬﻢ ﺃﺑﺪﺍ ، ﻓﺈﻧﻬﻢ
ﺩﻋﻮﻧﺎ ﻟﻴﻨﺼﺮﻭﻧﺎ ، ﺛﻢ ﻋﺪﻭﺍ
ﻋﻠﻴﻨﺎ ﻓﻘﺘﻠﻮﻧﺎ “
“Ya Allah! In har ka
tsawaita rayuwarsu to,
ka tarwatsa su, ka
hahhargitsa su, kada ka
bari su ji dadin mai mulki
ko wane ne sam. Hakika
sun kira mu da sunan
taimakonmu amma sai
suka zabura a kanmu
zasu kashe mu”. Duba
AL’IRSHAD na Al Mufid,
shafi na 241 da Kashful
Gummah na Arbili (2/18
da kuma 2/38).
5. Al Ya’qubi a cikin
Tarihinsa (1/235) shi
kuma cewa ya yi, Zainul
Abidin dan sayyidina
HUSAINI wanda Allah
ya kaddari ya kubuta ba
a kashe shi ba a Karbala
shi ma ya jingina kisan
Husaini da iyalansa ga
‘yan Shi’ah, mutanen
Kufa duk kuwa da
kukan munafurci da ya
tarar suna yi. Ga
maganarsa nan da
nassinta:
ﻟﻤﺎ ﺩﺧﻞ ﻋﻠﻲ ﺑﻦ ﺍﻟﺤﺴﻴﻦ
ﺍﻟﻜﻮﻓﺔ ﺭﺃﻯ ﻧﺴﺎﺀﻫﺎ ﻳﺒﻜﻴﻦ
ﻭﻳﺼﺮﺧﻦ ﻓﻘﺎﻝ ” : ﻫﺆﻻﺀ
ﻳﺒﻜﻴﻦ ﻋﻠﻴﻨﺎ ﻓﻤﻦ ﻗﺘﻠﻨﺎ ؟ “
“A lokacin da Ali bin Al
Husain ya shiga Kufa –
yana nufin bayan rikicin
Karbala – sai ya tarar da
matan garin na ta kuka
da hargowa, sai ya ce,
“Af! Dubi wadannan wai
mu suke wa kuka. To,
wa ya kashe mu ne?
Zamu takaita a haka,
sai gobe mu garzaya
birnin Sham wurin
Yazidu mu ji abinda yake
faruwa a can. Amma
muna son mu jefa
tambaya ga masu
adalci: Don girman Allah,
wa ya kashe sayyidina
HUSAINI?

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s