ME YA FARU A KARBALA? 13 (Dr mansur sokoto)

ME YA FARU A
KARBALA? 13
Labarin Kisan Husaini
Ya Game Duniya
Da sauri kuma ba da
bata lokaci ba wannan
mugun labari ya game
duniya. Ana mamaki ya
aka yi musulmi mai
neman ceton Manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wa
Alihi Wasallam ya iya
kashe jikansa, farin cikin
rayuwarsa?! Wannan
labari ya mantar da
musulmi sauran musibu
da fitinun da suka
gabata. Daman an ce,
ba a jin warin bera in
ana babbakar giwa.
A hedikwatar halifanci
Sham, Yazidu ya samu
wannan labari mai ban
mamaki. Sai dai kamar
yadda muka fadi a
baya, ruwayoyi sun sha
banban game da irin
tarbon da Yazidu ya yi
ma wannan labari.
Riwayoyi mafi kusa da
gaskiya sune wadanda
suka ce, Yazidu ya
firgita da jin wannan
labari, ya yi taslima.
Sannan ya yi rantsuwa
shi bai ce a kashe
Husaini ba, kuma bai ji
dadin kisan ba. Ya la’anci
gwamnansa Ubaidullahi,
ya ce bai kiyaye
alfarmar Manzon Allah
ba.
Wannan magana ba a
cikin littattafan Sunnah
kawai ba har a cikin na
Shi’ah akwai ta. Misali, a
cikin KITABUL IHTIJAJ
na Tabarsi cewa ya yi:
A lokacin da aka zo da
Ali bin Al Husain wajen
Yazid ya ce ma sa, na
samu labarin cewa zaka
kashe ni. Idan har haka
ne, ina son wadannan
‘yan mata (yana nufin
kannensa da aka zo da
su) ka nemi wanda zai
kai su Madina. Sai Yazidu
ya ce masa, ai ba
wanda zai kai su in ba
kai ba. Allah ya la’anci
Ibnu Murjanah –
Ubaidullahi bin Ziyad
kenan – wallahi ban sa
shi kashe babanka ba.
Kuma da ni ne a wurin
wallahi ba zan kashe shi
ba. Sannan ya yi masa
kyauta mai yawa, ya
mutunta shi, ya hada
shi da ‘yan rakiya tare
da sauran matan suka
wuce Madina.
Kisan Husaini ya yi kama
da kisan Zubair bin Al
Awwam Dan gwaggon
Manzon Allah Safiyyah
bint Abdil Muttalib
wanda ya kasance tare
da su Nana Aisha a cikin
yakin rakumi. Yakin da
makasan sayyidina
Usman, wadanda suka
yi masa juyin mulki suka
hasa wutarsa tsakanin
sarkin musulmi Ali da
talakawansa da suka
fito don daukar fansar
Usman. Yaki ya koma ba
ji ba gani tsakanin ‘yan
uwa – Su Zubairu, Dalha
da Aisha a daya
bangare, da kuma Ali,
Ammar bin Yasir da
sauransu a bangare
daya. Da Ibnu Jarmuz ya
kashe Zubair sai ya zo
yana murna da bushara
ga sayyidina Ali. Sai Ali
Radiyallahu Anhu ya ce
masa: Tabbas na ji
Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wa Alihi Wasallam
yana cewa: “Ka yi
bushara ga wanda zai
kashe Dan Safiyyah da
shiga wuta”. Duba
BIHARUL ANWAR
(32/336).
Babu shakka tambaya
ta farko da mutum zai
yi a nan ita ce, to in
haka ne don me da
Yazid bai yi wa
Ubaidullahi hukunci ba?.
Alal akalla ai ya kamata
ya cire shi daga
gwamna. Haka ne.
Amma dai wannan
mas’ala ce ta siyasa. Ai
ka ga ko sayyidina Ali ba
wani hukuncin da ya yi
wa Ibnu Jarmuz wanda
ya kashe Zubair. Daga
karshe ma shi Ibnu
Jarmuz na cikin
wadanda suka yi ma
Alin tawaye har suka yi
yunkurin kashe shi, kai
ma suka kashe shi din.
Dalilin kasancewar
lamarin na siyasa shi ne,
duban yanayin Kufa ita
kanta da yake babu
salihin mutum da ke iya
zama gwamna a garin.
Sahabbai da dama suka
sa aka dauke masu har
da wanda suka
tuhumta da rashin iya
sallah, alhalin tun
zamanin Manzon Allah
yake gwamna! Don
haka, a zamanin daular
Bani Umayyah zaka ga
duk wani fasikin
gwamna maras imani –
irin su Hajjaj – a can ne
aka tura shi. Na
tattauna wannan
matsala a mukalar da
aka buga a fitowa ta 3
ta mujallar Degel, June
2000 (FAIS, Usmanu
Danfodiyo University,
Sokoto) mai taken “The
Umayyad Dynasty
Between Facts and
Fiction: A Study of the
Genesis of the Dynasty
and Critical Analysis of
it’s Historical Sources”.
Husaini dai ba shi kadai
Allah ya azurta da
shahada ba a Karbala.
Akwai da dama daga
cikin ‘yan uwansa da ya
fito da su wadanda
suka hada da kannensa
Ja’afar da Abbas da
Muhammad da
Abubakar da Umar da
Usman duk ‘ya’yan
sayyidina Ali. Akwai
kuma ‘ya’yan wansa Al
Hasan: Abdullahi da
Qasim da Abubakar. Sai
‘ya’yansa shi kansa
Husaini: Ali babba da
Abdullahi. Karamin
dansa kam Ali Zainul
Abidin – Wanda ake ma
lakabi da Abubakar – bai
samu wannan daraja da
danginsa suka samu ba,
saboda ba shi da lafiya
a wannan rana, don
haka bai yi yaki ba, su
kuma arnan ba su taba
shi ba. Mun bada
cikakken tarihinsa a
cikin littafin MAI RABON
GANIN BADI: ALI
ZAINUL ABIDIN, wanda
aka buga a shekara
2004.
Daga cikin wadanda
Allah ya karrama da
shahada a tare da
Husaini har wayau
akwai ‘ya’yan baffansa
Akilu. Su ne, Ja’far da
Abdullahi da
Abdurrahman. Sai kuma
Muhammad bin Muslim
wanda aka kashe
mahaifinsa tun kafin
isowar Husaini. Daga
cikin ‘ya’yan Abdullahi
bin Ja’far kuwa akwai
Aunu da Abdullahi. In ka
hada da Husaini mutane
18 kenan dukansu ‘yan
gidan Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wa Alihi
Wasallam. Wannan
kuma shi ya sa musibar
ta kara tsananta a kan
musulmi.
Amma ko me ya sa su
‘yan Shi’ah suke
maganar Husaini, suna
makokinsa shi kadai, ba
sa ko nuni da sunayen
sauran abokan
shahadarsa? Wannan su
ya kamata su bada
amsa da kansu.
A gaba zamu yi
maganar abinda ya biyo
bayan wannan fitina,
sannan mu yi sharhi a
kan matsayinmu game
da Yazidu da hukuncin
la’antarsa.
Allah ya yi mana kariya
daga fitinu na zahiri da
na boye.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s