ME YA FARU A KARBALA? 14 (Dr mansur sokoto)

ME YA FARU A
KARBALA? 14
Me ya biyo bayan
kashe Husaini?
Bayan da mutanen Kufa
suka ga abinda ya faru
a ranar Ashura sai suka
hakikance sun ci amanar
sayyidina Husaini tun da
su suka gayyato shi
amma kuma suka
tozarta shi. Sun fito da
shi daga amintaccen
gari kuma sun yi biris da
zuwansa har mai
aukuwa ta auku. To,
sannan ne fa suka fara
tunanin yadda zasu
kankare ma kansu
wannan laifi. A nan ne
wata kungiya ta
bayyana mai suna
“Jaishut Tawwabin”
rundunar masu tuba.
Babbar manufar
wannan kungiya tasu
ita ce yin gangami don
fada da gwamnatin
Banu Umayyah da ta
zama gwamnatin ‘yan
ta’adda wadda ba ta
kiyaye alfarmar jinin
gidan Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wa Alihi
Wasallam ba. Manufa ta
biyu ita ce daukar
fansar jinin ‘ya’yan
gidan Manzon Allah da
aka kashe. To, sai dai
wannan fargar jaji da
‘yan Shi’ah suka yi ba ta
yi wani tasiri na azo a
gani ba. A maimakon
haka sai ta ida dagula
lamurra, ta kara auka
al’ummar musulmi cikin
rikici. Duk abinda ‘ya’yan
wannan kungiya ta ‘yan
tuba suka yi bai wuce
kamfe ne da
furofaganda ba ta
batunci ga gwamnatin
Yazid da kokarin wanke
hannun ‘yan Shi’ah daga
wannan ta’asa. A cikin
wannan kungiyar ne aka
samu wani dan ta’adda
mai suna Mukhtar bin
Abi Ubaid Ath Thaqafi
wanda ya lashi takobin
sai ya ga bayan duk
masu hannu ga kisan
Husaini. A cikin haka
kuwa ya halaka mutane
masu dinbin yawa
wadanda ba su ji ba, ba
su gani ba, tare da
cewa kuma lalle ya
kashe da dama daga
cikin mutanen waccan
la’anannar runduna ta
Bin Ziyad. Daga karshe
dai Mukhtar ya yi
da’awar cewa, yana
haduwa da mala’ika
Jibrilu a kullum don
tattauna matakan da
yake dauka a cikin
wannan Jan aiki da ya
dora ma kansa. Ya dai
zamo wani dan karamin
annabi kenan. Daga cikin
babban tasirin da
kungiyar Tawwabuna
ta yi ta shigar da
mutanen Makka da
Madina cikin wannan
rikici. Ina nufin yunkurin
juya gwamnati mai ci ta
Yazidu. Kodayake ba lalle
ne a dora masu dukan
alhakin abinda ya faru
ba. A Makka tun da
labarin Karbala ya je ma
su sai Abdullahi bin
Zubair ya nemi goyon
bayan jama’a a kan
zama khalifa, kuma ya
samu nan take. Kamar
dai mutanen Makka na
ganin duk gwamnatin
da ta iya tafka wannan
danyen aiki to, tawaye
a kanta ya zama wajibi.
A Madina birni Manzo
kuwa, jama’a sun tashi
haikan don nuna
alhininsu game da
abinda ya faru. Tuni
suka tsige gwamnansu
Usman bin Muhammad
bin Abi Sufyan, suka
kuma gargada duk
dangin Banu Umayya da
ke zaune a Madina suka
fitar da su daga cikinta
a mtasayin wani
gargadi na yin tawaye
ga gwamnatin Yazidu.
Wannan ya faru bayan
an tattara su a cikin
gidan Marwan bin Al
Hakam inda suka yi
fursuna na wani dan
lokaci. Kuma an ruwaito
cewa adadinsu na da
yawan gaske. Bayan
sama da watanni goma
da aka yi ana famar
sasanta wannan lamari,
mutanen Madina sai
kara cijewa a kan
matsayinsu suke yi. A
nan ne Yazid ya tashi
wata runduna da ya yi
mata izinin yakar gari
mai alfarma bayan
gargadi na kwana uku
da ya amince a ba su na
su dawo ma doka.
Wanda ya jagoranci
wannan runduna shine
Muslim bin Uqbah. A nan
ne fa Yazid ya iyar da
kife sauran kimar da
yake da ita a idon
jama’ar musulmi na
duniya ta wancan lokaci.
Domin kuwa duk
kokarin da rundunar
Muslim ta yi na shawo
kan mutanen Madina su
koma ga da’a cin tura
ya yi. Masu shiga
tsakani duk suka
hakura. Daga karshe
kaddarar Allah ta
gudana da ayi
ta’addancin halasta
wannan birni da Manzon
Allah ya haramta. An yi
hasarar rayuka da dama
na mutanen kirki masu
ibada da matasa da
malamai har da wasu
daga cikin ‘ya’yan
sahabbai. Bayan da
Muslim ya tarwatsa
rundunar mutanen
Madina, ya karya karfin
mayakansu sai ya nada
masu sabon gwamna
shine Ruhu bin Zinba’u.
Wannan kuwa ya faru a
farkon watan Dhul Hajji
na shekara ta 53H. Da
Muslim ya gama
wannan barna sai ya
tasar ma birnin Makka
mai alfarma bisa ga
umurnin sarki Yazid. To,
amma Allah bai yi masa
jinkiri ba tunda rai ya yi
halinsa tun yana kan
hanya. Wanda ya karasa
tafiya da rundunar shi
ne Husaini bin Numair.
Sun isa Makka daidai
lokacin aikin hajji, suka
je Minna da Arafat,
suka yi hadaya tare da
jifar Shedan. Amma fa
ba hanyar shiga Makka
balle ayi dawafi da
sa’ayi tunda rundunar
Ibnuz Zubair ta yi zobe
ta cikin garin Makka.
Haka su kuma Ibnuz
Zubair da jama’arsa sun
yi dawafi da sa’ayi
amma ba zancen tsayin
Arafat tunda ba su iya
fita gari. Sai aka yi
canzaras; ba wanda
hajjinsa ya inganta a
wannan shekarar. La
haula wala kuwwata
Illa billah. Watanni hudu
rundunar Yazid na fake
da Makka, bayin Allah na
ciki suna shan azabar
rayuwa, ba a shiga ba a
fita, sai ga ikon ubangiji
ya bayyana, labari ya iso
cewa sarki Yazidu ya
gama da duniya. To, ko
ya wannan kunyatattar
runduna ta karasa da
Ibnuz Zubair da
mutanen Makka? Zamu
ci gaba in sha Allah.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out / Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out / Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out / Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out / Change )

Connecting to %s