ME YA FARU A KARBALA? 15 (Dr mansur sokoto)

ME YA FARU A
KARBALA? 15
Mutuwar Sarki Yazid
Ga dukkan alamu Yazidu
ya bar duniya da juyayin
abu guda daya da yake
fargaban gamuwa da
Allah a kan sa. Wannan
lamarin kuwa shine
kisan Husaini da
danginsa. An fadi cewa,
karshen kalaman da ya
furta a duniya su ne:
“Ya Allah! kada ka rike ni
da abinda ban so ba
kuma ban bada umurni
ba. Ya Allah! Kayi
hukunci a tsakani na da
Ibnu Ziyad – yana nufin
gwamnansa na Kufa
wanda ya sa aka kashe
Husain. Yazid ya rasu a
ranar 14 ga Rabi’ Awwal
na shekarar 64H. Duka
duka mulkinsa bai cika
shekaru hudu ba amma
al’ummar musulmi ta
samu ja da baya
matuka daga karfinta
da kwarjininta a cikin
wannan bakin lokaci.
Rundunar Husain bin
Numair wacce take
tsare da Ibnuz Zubair
da jama’arsa suna dako
a wajen Makka ba su
samu labarin mutuwar
Yazid ba sai bayan sati
uku cur. Abu kadan ya
rage wannan runduna
ta hada kai da Ibnuz
Zubair bayan sun samu
wannan labari. Amma
abinda ya kawo cikas
shi Bin Numair ya nemi
ya dora hannunsa a kan
na Ibnuz Zubair ya yi
masa mubaya’a da
sharadin a yafe duk
jinainan da suka gudana
a baya. Ya ce kuma idan
an yi haka na lamunce
ma kasar Sham gaba
daya zan sa su yi maka
mubaya’a. Shi kuma sai
ya ki karbar wannan
sharadi. A nan ne Bin
Numair ya juya yana
nadama, ya ce, “Dubi
yadda nake kiran sa
zuwa sarauta yana
neman ci gaba da
fitina”. Ashe dai Allah
bai kaddare shi da zama
sarki ba. A can kuma
birnin Dimashka ta
Sham an sha
takaddama sosai a kan
wa za a nada bayan
Yazidu tun da shi bai bar
wani wasici a kai ba.
Daga bisani sai aka dora
wa dansa Mu’awiyah
karami jan wannan
ragama. Amma ina
dadin mulki a lokacin
tashin hankali! Ba da
jimawa ba shi wannan
sai ya yi murabus ya bar
wuri wayam ana ta
muhawara ba mai
bukata. A nan ne
Umawiyyawa suka
bukaci su je su sasanta
da Ibnuz Zubair a
Makka, su yi masa
mubaya’a daga bisani
kuma sai Allah ya sa
aka jitu a kan Marwan
bin Al Hakam wanda shi
ne mulki ya ci gaba a
cikin zuriyarsa. Matsayin
Malaman Sunna A Kan
Wadannan Fitinu
Annabinmu Sallallahu
Alaihi Wa Alihi Wasallam
ya sanar da cewa fitinu
zasu gudana a bayansa.
Kuma ya fadi cewa
alherinka yana
gwargwadon
nisantarka daga gare
su. Wadannan hadisai
suna na a shimfide cikin
littafan Sunna a Kitabul
Fitan na kowane littafi.
Duba alal misali: Sahihul
Bukhari, Kitabul Fitan,
Babun takunu fitnatun
al qa’idu fi ha khairun
minal qa’im, Hadisi na
6670. Game da abinda
ya faru a Karbala, ba
wani sabani a tsakanin
malamai cewa, an tafka
barna wadda ba ta dace
ba. Abin takaici ne da ya
nuna cewa ba a
mutunta Manzon Allah
ba a cikin sha’anin
iyalinsa. Wanda kuwa
duk yake da hannu a ciki
to, ba abinda zai hana
shi gamuwa da fushin
Allah in ba tuba ya yi ba
tuba ingatacciya. Amma
a game da wa ke da
alhakin wannan ta’asa,
to kowa ya fadi
albarkacin bakinsa. Duk
wanda yake da
kyakkyawan nazari da
sa adalci cikin hukunci
zai iya lura da cewa
kaddarar Allah ita ce
babban jigon abinda ya
faru. Kuma duk abinda
ka ga Allah ya yi to,
tabbas akwai hikima a
cikinsa, ko mun san ta
ko bamu sani ba.
Hasashen da Ibnu
Taimiyyah ya yi a nan
abin sauraro ne matuka.
Ga abinda ya ce: Hasan
da Husaini sun rayu a
cikin kuruciya zamanin
Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wa Alihi Wasallam.
Don haka ba su samu
damar taimaka masa
ba a wajen jihadi da
yada kalmar Allah
kamar yadda sauran
sahabbai suka yi. (A
Lokacin wafatin Manzon
Allah, Hasan yana da
shekaru bakwai ne da
wata tara, a yayin da
Husaini yake da shekaru
shida da watanni
takwas). Duk
wahalhalun da sahabbai
suka sha a Makka da
tsangwama da tashin
hankali, haka ma duk
gwagwarmayar da
suka yi bayan sun bar
gidajensu da yakokan
duk da aka yi; Badar da
Uhud da Khandak da
Tabuk da sauransu inda
Allah ya yi ta rabon
darajoji da gafara ga
sahabbai su wadannan
bayin Allah ba su samu
kasancewa a ciki ba.
Kasancewar Allah ya
zaba masu wani babban
matsayi a aljanna ya sa
Allah ya jarabce su da
wata jarabawa a irin
nasu matsayi kuma ya
basu shahada. Don haka
ma Ibnu Taimiyyah ya
kara da cewa,
kashedinka ka zargi
Husaini a kan fitowar da
ya yi bayan duk
shawarwarin da aka ba
shi. Ka sani Allah ne
yake ingiza shi zuwa ga
daukaka da darajar da
ya hukunta masa. Duba
Minhajus Sunnatin
Nabawiyyah na Ibnu
Taimiyyah (4/527-536).
Zamu ci gaba da yardar
Allah.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s