ME YA FARU A KARBALA? 16 (Dr mansur sokoto)

MEYA FARU A
KARBALA? 16
Matsayin Malaman
Sunnah a kan
Wadannan Fitinu
Game da tawayen
mutanen Madina
malamai magada
Annabawa ba su ja
bakinsu ba suka yi shiru.
Sun bayyana ma
mutane abinda Allah ya
wajabta na da’ar
shugaba ko da fasiki ne.
Maslahar da ke cikin
wannan ita ce, kauce
ma abinda zai zubar da
jinainan jama’a da kawo
tashin hankalin da ba a
san karshe ko iyakarsa
ba. Littafan Sunnah na
hadisi da na Akida a cike
suke da wadannan
hadisan. Sheikh Abdus
Salam Bin Barjis ya
tattara su tare da
maganganun magabata
a cikin littafinsa
MU’AMALATUL HUKKAM
FI DAU’IL KITAB WAS
SUNNAH, bugun Riyadh
1415H.
Misalai biyu kawai zamu
kawo don bayyana
matsayin malaman
Sunnah a wancan lokaci.
1. Matsayin Abdullahi bin
Umar:
Kamar yadda muka gani
a baya, Abdullahi bin
Umar Radiyallahu
Anhuma na daga cikin
wadanda ba su yi na’am
da nadin Yazidu ba.
Amma da ya ga jama’a
sun yi masa mubaya’a
sai ya kyamaci ya ware
daga mutane. To, a
lokacin da wannan
fitinar ta taso ta yin
tawaye ga Yazid, Ibnu
Umar ya tara dukkan
iyalansa ya gargade su
game da sa hannu cikin
abinda ke gudana. Ya ce
musu, ku sani mun bada
mubaya’armu ga
wannan mutum ne bisa
ga amincin Allah da
sunnar Manzonsa. Kuma
na ji Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wa Alihi
Wasallam yana cewa:
“Duk wanda ya yi
yaudara za a kafa masa
tuta a ranar alkiyama
ace ga yaudarar da
wane ya yi. Babu kuwa
wata yaudara – in dai
ba shirka ce ba – da ta
kai kwance mubaya’ar
da aka yi bisa ga
Sunnah. Don haka kada
ku yi ma Yazid tawaye.
Kada dayanku ya sanya
hannunsa cikin wannan
tashin hankali. Wanda
kuwa duk ya yi haka zai
zama rabuwata da shi
kenan. Duba Sharhin
Sahihu Muslim tare da
sharhin Imam An
Nawawi, Hadisi na 58 da
na 1851 (2/1478).
Sayyidina Ibnu Umar bai
tsaya kawai ga
gargadin iyalinsa ba sai
da ya je wajen jagoran
wannan yunkuri
Abdullahi bin Muti’u.
Abdullahi ya yi wuf ya
dauko masa majingini,
sai Ibnu Umar ya ce
masa dakata. Ni ban zo
don in zauna ba. Na zo
ne in sanar da kai wani
Hadisi da na ji daga
Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wa Alihi Wasallam.
Na ji shi yana cewa:
“Duk wanda ya zare
hannunsa daga biyayya
(ga shugaba) zai gamu
da Allah ba ya da hujja.
Wanda kuwa duk ya
mutu yana mai rabuwa
da jama’ar musulmi to,
zai yi mutuwa irin ta
jahiliyyah”. Duba Sahihu
Muslim a wurin da muka
fadi a dazu.
2. Matsayin Muhammad
Bin Ali Bin Abi Talib
A cikin yawon da suka
yi na neman goyon
bayan jama’a, wadanda
suka shirya tawayen a
Madina sun je wurin
kanen Husaini;
Muhammad Wanda aka
fi sani da Ibnul
Hanafiyyah. Muhammad
ya tambaye su, mene
ne dalilinku na yi wa
Yazidu tawaye? Sai
jagoransu Abdullahi bin
Muti’u ya kada baki ya
ce masa, saboda Yazidu
na shan giya, kuma ba
ya sallah, sannan yana
tsallake hukuncin
Alkur’ani. Muhammad ya
ce masu, to amma ni na
je wajen Yazid ban ga
abinda kuka fadi ba. Na
zauna tare da shi na
wani lokaci, na lura da
yana tsayar da sallah,
yana kamanta yin alheri,
yana tambayar ilimi
kuma yana lazimtar
Sunnah. Sai suka ce, ai
zai iya yin haka don riya!
Ibnul Hanafiyyah ya ce,
to me yake so a gurina
ko yake tsoro da zai
mani riyar abinda bai
saba ba? Ya sha giyar
ne a gabanku? In dai har
kun ga ya sha giya, to
tare kuka sha kenan. In
ba haka ba to bai halalta
ku shedi abinda ba ku
gani ba. Sai suka ce, ba
mu gani ba kam amma
wallahi mun yarda da
wannan magana, kuma
tabbas gaskiya ce. Sai
ya ce, to, Allah Ta’ala
ya soke wannan shaida
taku, don cewa ya yi:
( ﺍﻻ ﻣﻦ ﺷﻬﺪ ﺑﺎﻟﺤﻖ ﻭﻫﻢ
ﻳﻌﻠﻤﻮﻥ ( ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻟﺰﺧﺮﻑ :
٨٦
“Face wadanda suka yi
shaida da gaskiya,
kuma suna sane (da
abinda suka yi shaida a
kansa). Suratuz
Zukhruf: 86
Da Ibnul Hanafiyyah ya
tabbata masu ba shi
tare da su, sai suka ce
kamar dai kana ganin
kai ka fi cancanta mu sa
gaba! Sai ya ce, sam. Ba
na halalta ma kaina yin
wannan al’amari a
kowane matsayi, ina
jagora ko ina mabiyi.
Suka ce, to, amma ai ka
yi yaki tare da babanka.
Ya ce, ku kawo min
wani irinsa in taya shi
yaki.
Suka ce, to ka sa
‘ya’yanka Al Qasim da
Abul Qasim su biyo mu.
Ya ce, in har zan sa
‘ya’yana me zai hana ni
ma in je?
Suka ce, to ka zo mu je
ba sai ka yi yaki ba.
Iyaka kawai ka yi mana
kamfe ga mutane. Ya
ce, tsarki ya tabbatar
ma Allah! In ce mutane
su yi abinda ba na yi?
Suka ce, to lalle ko kana
so ko ba ka so sai mun
fitar da kai ka shiga
cikin wannan lamari. Ya
ce, ba zai maku dadi ba
don zan rinka ce ma
mutane su ji tsoron
Allah, kada su yardar da
wani mahaluki a cikin
fushin ubangiji. Daga
karshe dai Muhammad
ya fice ya bar Madina
zuwa Makka don gudun
wannan fitina. Duba AL
BIDAYA WAN NIHAYA
na Ibnu Kathir (8/604)
da kuma MUKHTASAR
TARIKH DIMASH na
Ibnu Manzhoor (8/256).
Zamu dawo magana
kan Yazid in Allah ya so.
Ku dakace mu.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s