ME YA FARU A KARBALA? 17 (Dr mansur sokoto)

MEYA FARU A
KARBALA? 17
Mu Koma Kan Yazid
Nuni ya gabata a can
baya zuwa ga irin
sabanin mawallafa a
game da Yazid. Bisa ga
wannan ne mutane
suka kasu kashi uku a
kan shi. Wasu na zagi
har ma da la’antar sa,
wasu na yabon sa da
gwarzanta shi. Kashi na
uku su ne wadanda
suka tsaya a tsakani
suna neman ayi masa
adalci a ajiye shi a
matsayin sauran ire-
irensa daga cikin
sarakunan musulunci
masu rauni wadanda
suka tafka kurakurai a
cikin mulkinsu. A sa su a
cikin ayar da
madaukakin sarki yake
cewa
(ﻭﺁﺧﺮﻭﻥ ﺍﻋﺘﺮﻓﻮﺍ
ﺑﺬﻧﻮﺑﻬﻢ ﺧﻠﻄﻮﺍ ﻋﻤﻼ ﺻﺎﻟﺤﺎ
ﻭﺁﺧﺮ ﺳﻴﺌﺎ ﻋﺴﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻥ
ﻳﺘﻮﺏ ﻋﻠﻴﻬﻢ ﺍﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻏﻔﻮﺭ
ﺭﺣﻴﻢ ( ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻟﺘﻮﺑﺔ: ١٠٢
“Kuma wadansu sun yi
ikirari da laifukansu, sun
gauraya aiki na kwarai
da wani maras kyawo,
yana yiwuwa Allah ya yi
tuba a kan su, lalle Allah
Mai yawan gafara ne,
mai gamammen jinkai”.
Suratut Taubah: 102
Mu saurari wani daga
cikin malamai masu irin
wannan matsakaicin
ra’ayi, shi ne Imam Abu
Abdillahi Adh Dhahabi.
Ga abinda ya ce a cikin
tarihin Yazid a littafinsa
SIYAR A’LAM AN
NUBALA (7/36):
ﻟﻪ ﻋﻠﻰ ﻫﻨﺎﺗﻪ ﺣﺴﻨﺔ ﻭﻫﻲ
ﻏﺰﻭ ﺍﻟﻘﺴﻄﻨﻄﻴﻨﻴﺔ، ﻭﻛﺎﻥ
ﺍﻣﻴﺮ ﺫﻟﻚ ﺍﻟﺠﻴﺶ، ﻭﻓﻴﻬﻢ
ﻣﺜﻞ ﺍﺑﻲ ﺍﻳﻮﺏ ﺍﻻﻧﺼﺎﺭﻱ
ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ… ﺍﻟﻰ ﺍﻥ ﻗﺎﻝ :
ﻭﻳﺰﻳﺪ ﻣﻤﻦ ﻻ ﻧﺴﺒﻪ ﻭﻻ
ﻧﺤﺒﻪ، ﻭﻟﻪ ﻧﻈﺮﺍﺀ ﻣﻦ ﺧﻠﻔﺎﺀ
ﺍﻟﺪﻭﻟﺘﻴﻦ، ﻭﻛﺬﻟﻚ ﻓﻲ ﻣﻠﻮﻙ
ﺍﻟﻨﻮﺍﺣﻲ، ﺑﻞ ﻓﻴﻬﻢ ﻣﻦ ﻫﻮ
ﺷﺮ ﻣﻨﻪ ..
Tare da tubatubansa
yana da alheri guda
daya, shine yakar
Qustantiniyah. Kuma shi
ya jagoranci yakin, alhali
a cikin rundunar akwai
manya irin su Abu
Ayyub Al Ansari mai
masaukin Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wa Alihi
Wasallam.. Har dai inda
Dhahabi ya kai ga cewa,
“Yazidu na cikin
wadanda ba ma zagin
su, ba ma kuma kaunar
su. An yi ire-irensa da
dama daga cikin
halifofin daulolin guda
biyu (yana nufin
Umawiyyawa da
Abbasiyyawa), haka ma
a cikin gwamnoni an yi
ire-irensa da ma
wadanda shi ya dara su
dama.
A baya mun kawo
hadisin da ya nuna
falalar wannan jihadi da
su Yazidu suka yi
wanda Bukhari ya
ruwaito shi – hadisi na
2924 – daga Ummu
Haram Al Ansariyyah
matar sayyidina Ubada
bin Samit wadda ta ce,
Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wa Alihi Wasallam
ya ce “runduna ta farko
daga al’ummata
wadanda zasu yi yaki a
kan teku an gafarta
masu. Sai na ce, ya
Manzon Allah, ni ina
cikinsu? Ya ce, eh, kina
cikinsu. Sannan ya ce,
kuma runduna ta farko
daga al’ummata da
zasu yaki birnin Qaisar –
Qustantiniyah – su ma
an gafarta masu. Na ce,
Manzon Allah ina
cikinsu? Sai ya ce, a’a.
Kuma mun fadi ba ta ga
wannan yakin da Yazidu
ya jagoranta ba don ta
cika bayan gama
wancan yaki wanda
babansa Mu’awiyah ya
jagoranta kai tsaye.
Kamar yadda bakin da
ba ya karya ya fada
mata.
Game da la’antar Yazid
kuwa da ma la’antar
kowane irin musulmi –
kai har da kafiri – ba
aikin mutanen kirki ba
ne. Domin kuwa
manzonmu Sallallahu
Alaihi Wa Alihi Wasallam
ya ce a hadisin Abdullahi
bin Mas’ud Radiyallahu
Anhu: “Musulmi ba mai
yawan suka ne ba, ba
mai yawan la’anta ne
ba, ba kuma mai fadin
kazamar magana ne ko
kalmar alfasha ba”.
Imam Al Bukhari ya
ruwaito shi a cikin AL
ADABUL MUFRAD, Hadisi
na 312, haka ma Ibnu
Hibban a cikin Sahihin
littafensa (1/421) Hadisi
na 192, haka ma Imam
Ahmad a cikin MUSNAD
(1/404) da kuma
Tirmidhi a cikin SUNAN
(4/350), Hadisi na 1977.
Albani da Arna’ut sun
inganta shi.
Magabata da dama sun
kasance suna kame
bakinsu daga la’antar ko
da dabba ce, domin
watarana a cikin tafiye
tafiyen Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wa Alihi
Wasallam ya ji wata
mata ta la’anci
rakumarta don ta kusa
kayar da ita, sai ya yi
umurni a dauke kayan
da ke kan rakumar a
sake ta. Ya ce, “An riga
an la’ance ta”. Imran bin
Husain da ya ruwaito
Hadisin ya ce, yanzu
haka kamar ina ganin ta
tana tafiyarta kowa ya
fita batunta. Duba
SAHIH MUSLIM (8/23),
Hadisi na 6769.
Wani muhimmin al’amari
da ya kamata mu yi
nuni gare shi a nan shi
ne tasirin farfagandar
JAISHUT TAWWABIN
da muka ambata a baya
na karin gishiri ga mafi
yawan labaran
abubuwan da suka faru.
Misali, masu tantance
ruwayoyi sun yi suka
ainun ga riwayoyin da
suka ce, an je da kan
sayyidina Husaini har
birnin Sham wurin Yazid,
ballantana sauran
almarar da aka hikaito
ta cewa ya fashe
haushi, da nuna murna
har da wasu baitoci na
rashin kunya. Haka
kuma game da iyalansa
bai inganta cewa, an yi
masu wulakanci ko dan
kadan ba. Maimakon
haka ma da aka zo da
su wurin Yazidu ya
mutunta su, kuma ya yi
masu rantsuwa cewa
bai yi umurni da haka
ba, bai kuma ji dadi ba.
Juyayi da makokin
Husaini dai babu shakka
wata bidi’a ce babba da
take da manufar ci gaba
da tona mikin da tuni
wadanda suka yi shi
sun gamu da Allah ya
hukunta su. Da yana
cikin addini a yi makokin
wani ai kuwa da an
shar’anta ayi na kakan
Husaini wanda shine
fiyayyen talikai. In kuma
sun ce ai saboda an
zalunce shi ne, to da shi
da mahaifinsa wa aka fi
zalunta? Shi ya yi fito na
fito har ya samu sa’ar
halaka mutane 88 a
cikinsu ya aika su zuwa
Jahannama a wurin
kokarinsu na kama shi,
sannan shi ma suka
samu kashe shi bayan
kama shi din ya faskara.
Amma shi mahaifinsa
kwanton bauna aka yi
masa yana hanyar
tafiya masallaci cikin
duhun asuba aka kashe
shi. To, don Allah a
tsakanin su biyun wa
aka fi zalunta? Kuma in
wannan ne dalilin yin
makoki don me da ba a
yin na babansa? Haka
su ma Halifofi biyu da
suka gabaci Ali
kowanensu yana
matsayin shugaban
musulmi aka kashe shi
kuma a cikin birnin
manzon Allah mai
alfarma. Idan kuma sun
ce don ya yi shahada ne
wajen kare addini, sai
mu ce wannan kam ai
abin buki ne, da Shari’a
ta amince da yin bukin.
Wane ne ba ya son ya
samu shahada? Sai a
zauna ayi ta kururuwa
ana yanka jiki don wani
masoyinmu ya tafi
aljanna? Kuma da haka
ne da shugaban Shahidai
Hamza baffan Manzon
Allah ya fi Husaini
cancanta. In sun ce ai
kisan na wulakanci ne,
to, ai kowa ya san irin
wulakancin da aka yi ma
gawar sayyidina
Hamza, abinda ya
bakanta ran Manzon
Allah matuka. Amma
duk da haka, masu
hannu ga wannan lamari
duk sun tuba, kuma
Annabi Sallallahu Alaihi
Wa Alihi Wasallam ya
karbi tubansu, ya bar su
da Allah idan tuba na
gari suka yi Allah ya
sani. In ma ba haka ba
to, can su da Allah
masanin gaibi.
Alkur’ani ya fada mana
cewa, Banu Isra’ila sun
yi ta kisan Annabawan
Allah. (Duba misali,
Suratul Baqara: 87 da
kuma 91). In da makoki
Ibada ne don me da ba
a umurci Manzo
Sallallahu Alaihi Wa Alihi
Wasallam ya yi masu
makoki ba?
Allah ya jikan babban
malamin Tabi’una;
Rabi’u bin Khuthaim, a
lokacin da aka gaya
masa an kashe Husaini
sai ya ce, sun kashe
shi? Aka ce masa eh. Ya
ce INNA LILLAHI WA
INNA ILAIHI RAJI’UN.
Sannan ya karanta aya
ta 46 a Suratuz Zumar
inda Allah ke cewa: “Ka
ce, Ya Allah! Mai kaga
halittar sammai da
kasa, masanin fili da
boye, Kai ne ke hukunci
a tsakanin bayinka a
cikin abinda suka
kasance suna saba wa
juna a cikinsa”. Bayan
haka Malam Rabi’u bai
sake cewa uffan ba.
Duba AL AWASIM
MINAL QAWASIM na Al
Qadi Abubakar Ibnul
Arabi Al Ishbili, shafi
131.
Ranar Ashura kafin ta
zama ranar shahadar
Husain ta kasance rana
mai tarihi da ya sa
Annabi Sallallahu Alaihi
Wa Alihi Wasallam yana
azumtar ta tun yana
Makka kamar yadda
mushrikai su ma suna
yi. Da ya zo Madina
kuma ya tarar Yahud su
ma suna yi, ya umurci
musulmi su ma su yi shi
a matsayin farali har sai
da aka saukar da
azumin Ramadhan
sannan aka dauke
faralci aka bar shi a
matsayin Sunnah. Duk
abinda ya faru bayan
wucewar Manzon
rahama ba zai canza
shari’ar da shi Manzon
ya bar mu a kanta ba.
Alhamdu Lillah.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s