AL KITABU WAL “ITRA” KO AL KITABU WAS “SUNNAH”? (Dr mansur sokoto)

AL KITABU WAL
“ITRA” KO AL KITABU
WAS “SUNNAH”?
Bismillahir Rahmanir
Rahim
Abinda muka sani ne
cewa, daga cikin
manyan ginshikan Shi’a
da suka dogara gare su
kuma suka gina
akidarsu a kai shi ne,
cewa Annabinmu
Sallallahu Alaihi Wa Alihi
Wasallam ya yi wasici
da abi Alkurani da
“ITRA” wato iyalan
gidansa. Sa’annan kuma
sai suka dauka cewa,
bin jikokin sayyidina
Husaini shi ake nufi
domin su ne magadan
ilimin annabta. (mutum
tara ne daga cikin zuri’ar
Husaini suka sa a cikin
imamansu goma sha
biyu amma babu na
Hasan ko guda!). A kan
wannan fahimta tasu
sun hakikance cewa an
saba ma umurnin
Manzon Allah tun da
farko, don haka tafiya
ta gurbace tun daga
asalinta, musulmin
farko – almajiran Annabi
da masu bi masu – duk
sun bar tafarkin shiriya,
a fahimtar ‘yan Shi’ah.
Muna so mu tattauna a
tsanake dangane da
wannan Hadisi da
ruwayoyinsa, domin mu
gano ingancinsa ko
rashin haka. Sannan mu
yi tsokaci game da
ma’anarsa wadda ta yi
daidai da abinda aka
sani na koyarwar
ma’aiki Sallallahu Alaihi
Wa Alihi Wasallam.
Kafin mu shiga wannan
bayani, zai yi kyau muyi
nuni ga matsalar da
take shiga a cikin
rubuce-rubucen
malaman Shi’a idan
suka zo magana a kan
hadisai. Wannan bayani
a hakikaninsa na
masanan Hadisi ne,
yana yiwuwa ya dan yi
nauyi ga wasu daga
cikin masu karatu.
Amma na ga ya zama
dole ne a matsayin
shimfida ga wannan
bayani da muke son yi.
Da farko dai malaman
Shi’ah sukan zo su
dauko hadisai
nagartattu ingantattu
wadanda a duniyar
Sunnah an gama
sallama masu, an
amince da su. Amma sai
su ba wadannan hadisai
wata ma’ana wadda ta
yi daidai da tasu
fahimta. Kamar wasu
hadisai da ke nuna
falalar sayyidina Ali da
darajojinsa. Ba ma
musun hadisan, kuma
ba ma rage ma
sayyidina Ali girmansa,
amma su sai su ce
wadannan hadisan hujja
ne a kan an zalunce shi
tunda ba a ba shi
halifanci ba tun da
farko. Sai su manta – ko
su yi gangancin
mantawa – cewa,
halifofi na gaba da shi
su ma suna da irin nasu
darajoji.
Kashi na biyu shi ne
hadisan da suke masu
rauni ne a wurin
ma’abota ilimi, an
bayyana illolin da ke
tattare da su, sai su
dauko wadannan
hadisan su rinka hujja
da su a kan mu, suna
cewa to, ga su nan ma
daga littafanku! Idan
aka yi sa’a hadisin
mashahuri ne da ake iya
samu a littafai da yawa
sai su yi ta cika takarda
da sunayen wadanda
suka kawo shi. Wanda
bai sani ba bai iya gane
cewa magana guda ce
ake maimaitawa, kuma
Hadisin daga mafita
guda yake. A wurin
malaman Sunnah kuwa
Hadisi ba ya zama hujja
sai an ruwaito shi ta
hanya gangariya wadda
babu sofane a cikin
maruwaitanta, kuma an
samu saduwar su
dukansu da juna,
sannan ba a samu wata
tangarda da ke iya
kawo suka abar
dubawa ba ga ita kanta
hanyar ko abinda shi
Hadisin ya kunsa. Irin
wadannan hadisan zaka
tarar da malaman
Sunnah da suka kawo
su sun fade su ne don
bayyana aibinsu, amma
sai su kuma wadannan
su cire maganar
wannan aibi su ce, to
gasu nan a cikin
littafanku muka dauko
su. Wannan kuwa wani
nau’i ne na boye ilimi
daidai yadda Yahudawa
suka so su yi wa
Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wa Alihi Wasallam
– ganin bai iya karatu ba
– sai Allah ya ba shi ikon
da ya ce, to ku dage
yatsanku daga nan ku
karanta mana sauran.
Sai ga su sun yi tsuru
tsuru! Hadisin da ya ce
“Ni ne birnin ilimi, Ali ne
kofarsa” ya shahara
kwarai, ga kuma yawan
hanyoyi, amma da an bi
su za a gan su wayau,
don ba nagartacciyar
hanya guda daya da aka
samo shi da ita.
A wata sa’ar kuma
malaman Shi’ah sukan
tsallake littafan hadisi
da aka sani gaba daya
su dauko wani labari ko
wata almara daga
littafan mawaka ko na
tarihi ko na adabi ko ma
wani mawallafi kawai
da yake wallafa
tatsuniya. Misali irin su
SUBHUL A’SHA na
Qalqashandi ko AL
AGANI na Abul Faraj Al
Asfahani ko littafan
Ahmad Shauqi ko na
Abbas Mahmud Al
Aqqad. Idan aka kawo
hadisan irin wadannan
littafan wani lokaci a
fadi littafin, wani lokaci
kuma a ce RAWAHUL
BUKHARI!!!
Akwai kuma littafan da
aka rubuta da sunan
Sunnah amma a
hakikanin gaskiya
mawallafansu ‘yan
Shi’ah ne. Kamar su Ibnu
Abil Hadid da Ibnus
Sabbag da Qanduri da
makamantansu
wadanda masana sun
dade da tantance
labarinsu.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s