AL KITABU WAL “ITRA” KO AL KITABU WAS “SUNNAH”? 2 (Dr mansur sokoto)

AL KITABU WAL
“ITRA” KO AL KITABU
WAS “SUNNAH”? 2
kashi na Uku shi ne
hadisan da malamanmu
suka yi sabani a kan
ingancinsu ko rauninsu.
Ka’idarmu a nan ita ce
hujja, ba Malam wane
ya fada ba. Amma da
zaran an samu haka sai
su yi fararat su ce, ai
Malaminku wane ya
inganta shi. Daga nan
sai su gina abinda shi
malamin da an tambaye
shi zai ce ba haka ne ba.
Idan mun zo fitar da
Hadisin “ITRA” zamu ga
wannan baro baro.
Kashi na Hudu shi ne
hadisan da suke sukar
mu a kansu, alhalin
yadda suke a
littafanmu haka suke a
nasu. Kamar Hadisin
fitsari a tsaye, da yawa
sukan zage mu a kansa,
su ce bamu san girman
Manzon Allah ba, alhalin
Hadisin yana a cikin
littafansu su ma! Da
kuma Hadisin cewa, ba
a gadon Annabawa. A
kullum sai ka ji suna
zagin sayyidina
Abubakar a kansa suna
cewa ya shara ta,
alhalin Majilisi da wasu
Malamansu sun kawo
shi ta nasu hanyoyi
kuma sun inganta shi.
Kashi na Biyar shi ne irin
hadisan da aka inganta
su da lafazin da suka zo
da shi ingantacce. Sai
Malaman Shi’ah su
kawo nasu lafazin mai
rauni su ce mun inganta
shi. In ka bi salsala zaka
tarar lalle ya inganta
amma ba a yadda suka
kawo shi ba. Kuma
nasun kitsa shi aka yi
domin wata manufa.
Wani lokaci fa har sauyi
na ganganci ake yi ma
kalma a cikin Hadisi don
ta dace da ma’anar da
suke so. Kamar yadda
suka yi da Hadisin
“ ﺗﺮﻛﺖ ﻓﻴﻜﻢ ﻣﺎ ﺍﻥ
ﺗﻤﺴﻜﺘﻢ ﺑﻪ ﻟﻦ ﺗﻀﻠﻮﺍ..”
Wannan “bihi” da ke
cikin Hadisin sukan
mayar da shi “bihima”
kamar yadda zamu gani
a nan gaba, don su
batar da Ma’anar da
Manzon Allah yake nufi
su tabbatar da nasu
son zuciya. Eh, ya zo da
“bihima” amma
karshensa “Wa sunnati
nabiyyihi” ne, ba “Wa
itrati” ba. Kamar yadda
yake a cikin MUWATTA
na Imam Malik tare da
sharhinsa TANWIRUL
HAWALIK (2/308). To,
amma su sai su kalato
wannan riwaya su yi
mata kai da waccan.
A nan kuma zamu iya
kawo wani hadisin da
suke yawan hujja da shi
“ ﻣﻦ ﻣﺎﺕ ﻭﻟﻢ ﻳﻌﺮﻑ ﺍﻣﺎﻡ
ﺯﻣﺎﻧﻪ ﻣﺎﺕ ﻣﻴﺘﺔ ﺟﺎﻫﻠﻴﺔ”
Mu sam a wurinmu ba
haka Hadisin yake ba. Ga
yadda yake:
“ ﻣﻦ ﺧﻠﻊ ﻳﺪﺍ ﻣﻦ ﻃﺎﻋﺔ ﻟﻘﻲ
ﺍﻟﻠﻪ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻘﻴﺎﻣﺔ ﻻ ﺣﺠﺔ ﻟﻪ،
ﻭﻣﻦ ﻣﺎﺕ ﻭﻟﻴﺲ ﻓﻲ ﻋﻨﻘﻪ
ﺑﻴﻌﺔ ﻣﺎﺕ ﻣﻴﺘﺔ ﺟﺎﻫﻠﻴﺔ ”
Banbancin da ke
tsakanin wadannan
ruwayoyi guda biyu ba
karami ba ne. Nasu yana
tabbatar da wata akida,
namu kuma yana
tabbatar da wata ta
daban. Amma sai su
kawo nasu su yi mana
hujja da shi. Idan kana
so ka kwatanta su sai
ka duba namu a SAHIHU
MUSLIM (6/22) hadisi na
4899 da kuma AS
SUNAN AL KUBRA na
Baihaqi (8/156) hadisi na
17055 sannan sai ka
duba nasu a cikin AL
KAFI na Kulini (1/377) da
KASHFUL ASRAR na
Khumaini, shafi na 197.
Bayan ka hakikance
banbancinsu sai ka sake
duba abinda Khomaini ya
ce, wai wannan Hadisi
sananne ne a wurin
Shi’ah da Sunnah!!!
Haka hadisin khalifofi
goma sha biyu
Kuraishawa. Su kan
dauko ingantattar
ruwayarsa su buga ta
da mai rauni sai su fitar
da cewa Hadisin ya
tabbata a yadda suke
son kawo shi.
In sha Allahu zamu ci
gaba.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s