AL KITABU WAL “ITRA” KO AL KITABU WAS “SUNNAH”? 3 (Dr mansur sokoto)

AL KITABU WAL
“ITRA” KO ALKITABU
“WAS SUNNAH” 3
Bari mu soma
magana kan Hadisin
da muke nufi:
Wannan Hadisi ya zo ta
hanyar sahabbai da
dama. Dukansu suna
cikin wadanda ‘yan
Shi’ah suka jingina ma
ridda bayan wafatin
Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wa Alihi Wasallam.
Kamar su Abu Huraira
da Zaid bin Arqam da
Jabir bin Abdillah da Amr
bin Auf da Abu Sa’id Al
Khudri. Amma kuma
suna azzama Hadisin
kwarai da gaske da
ruwaya guda daya daga
cikin ruwayoyinsa
wadda suke ganin ta
karfafi akidarsu. Haka
kuma sukan hautsina
ruwayoyin hadisin don
su fitar da wacce suke
bukata.
Zamu tattauna kan
wannan Hadisi – cikin
yardar Allah – ta
fuska uku:
Fuska ta farko ita ce,
hanyoyin da aka samo
Hadisin da su. Domin
abinda bakin malamai ya
hadu a kansa ne cewa,
Hadisi ba ya zama hujja
a addinin Allah, har a iya
jingina shi ga Manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wa
Alihi Wasallam sai an
amince da hanyar da
aka samo shi. Ma’ana
sai maruwaitansa sun
zamo masu sheda ta
kwarai daga bakunan
wadanda suka san su,
suka yi hulda ta ilimi da
su. Wannan ma shi ya
sa aka kai matsaya kan
amsar hadisan sahabbai
baki daya ba tare da
wariya ba. Tunda yake
muna neman wanda
muka amince ma ne, sai
muka sami su Allah ya
ce ya amince masu. Mun
kuwa sani wannan
maganar ba karama ba
ce, kuma Allah Ta’ala da
ya yi ta ya san abinda
take nufi, kuma bai
taba warware ta ba.
Saboda haka
Ahlussunnah sun
wadatu da shedar
mahaliccinmu a kan su.
Amma duk Wanda ba
su ba sai an tambayi
‘yan zamaninsa an ji
labarinsa sannan ne in
ya cancanta ake sanya
shi cikin amintattu.
Yawan hanyoyi kawai
ba ya sa a inganta
Hadisi a wurin masana
ballantana shahararsa
kamar a same shi a
littafi 100 misali.
Wannan kadai ba ya sa
a karbe shi sai an yi
nazarin tsanin da aka
taka aka dauko shi. Shi
ya sa wanda bai sani ba
sai ya rudu da yadda
‘yan Shi’ah ke yi; su
jejjero sunayen littafai
da na malamai don
tabbatar da ingancin
Hadisi maimakon mayar
da hankali a kan
isnadinsa. Ga shi kuma
ba su Jin kunyar su fesa
karya, su jingina
magana ga wanda bai yi
ta ba, sannan su kai
matsayar ce ma Hadisi
mutawatiri ne wanda
babu kokwanto a
kansa, alhalin rubabben
hadisi ne da ba ya da
madogara ko kwara
daya ingantatta.
Wannan shine abinda
bawan Husaini, ina nufin
ABDUL HUSAIN AL
MUSAWI ya yi a
littafinsa mai suna AL
MURAJA’AT wanda a
yau shi ne wasu ke
kwafowa suna tinkaho,
suna cika baki kamar
sun zo da wani ilimi mai
amfani. Uzurinsu shine
ba su sani ba, kuma ba
su iya gane basu sani ba
ballantana su koma
makaranta. To, amma
ko wannan uzurin zai
ishe su gaban Allah?
Rokon da muke yi Allah
ya hada mu da su a kan
shiriya baki daya.
Fuska ta biyu da zamu
kalli wannan Hadisi ita
ce lafuzzan da ya zo da
su. Hadisi ya kan iya
zuwa da lafazi biyu ko
abinda ya fi. A kan
kuma iya samun
dukansu sun inganta
matukar ba su ci karo
da juna ba. Haka kuma
Ana iya samun daya
daga cikinsu kuskure ne
ko ma ganganci daga
wani maruwaici wanda
ba amintacce ba. Irin
nan da zaran an samu
son zuciya sai ka ga
wasu sun rike wancan
lafazin wanda yake
kuskure ne sun azzama
shi, sun masa wanka da
ado har da fesa turare
don daukar hankali.
Amma duk wannan bai
hana masanan Hadisi su
jajirce su rarrabe zare
da abawa.
Fuska ta uku ita ce
ma’anarsa da fikihun da
ya kunsa. Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wa Alihi
Wasallam balarabe ne.
Kuma da harshen
larabcin ne ya bayyana
duk wata karantarwa
da ya yi. Don mu fahimci
abinda yake nufi kuwa
dole ne mu san wannan
yare kuma mu yi amfani
da sanin cikin fahimtar
maganarsa. Haka kuma
kowace magana da ta
fito daga tsarkakakken
baki to, malamai sukan
fitar da fikihunta da

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s