SAMUN MASU WA’AZI CIKIN AL’UMMA BABBAN ALHERI NE : Dr Ibrahim Jalo Jalingo

SAMUN MASU WA'AZI
CIKIN AL'UMMA BABBAN
ALHERI NE:
Lalle a samu mutane
cikin wata al'umma
suna tashi suna yin
wa'azi, suna kiran
jama'a da su tsaida
Sunnah, su gusar da
bidi'ah, su lazimci
gaskiya cikin dukkan
lamari, su yaki karya
cikin dukkan kome, lalle
wannan alheri ne babba.
Idan wani ya ce: ai irin
wannan aiki yana
jawowa mai yin shi
wahalhalu da yawa:
wani lokaci ya kan zama
sanadiyyar mutuwarsa,
ko dukansa, ko zaginsa,
ko cin mutuncinsa, ko
rasa wani hakki nasa da
ya kamata ya samu,
saboda haka abin da ya
fi shi ne kowa ya kame
bakinsa, domin samun
lafiyar jikinsa, da
mutuncinsa. To sai a ba
shi amsa da cewa: Ai
malamai magada suke
ga Annabawa, su kuwa
Annabawa ba gadon
kudi suka bari ba, a'a
gadon ilmin sanin
gaskiya ne da kuma aiki
da gaskiyar ko ana ha-
maza-ha-mata. Wannan
shi ne ma ya sa wasu
daga cikinsu suka rasa
rayukansu, wasu kuwa
aka dudduke su, wasu
kuwa aka zazzage su,
wasu kuwa aka cicci
mutuncinsu tamhanyoyi
daban daban.
Misali: babu irin cin
mutuncin da ba a yi wa
Annabi Muhammad mai
tsira da amincin Allah
ba, an yayyake shi, an
masa raunuka daban-
daban, an masa
jamhuru an ce shi
tababbe ne mahaukaci,
an ce mai raba kan
jama'a ne, mai kawo
hargitsi cikin al'umma ne
…..,,
Babban malamin Sunnah
masanin Hadithi, da
Tafsiri, da Tarihi, da
Sirah, Ibnu Katheer ya
ce cikin littafinsa
Albidayatu wannihayah
3/55-56:-
((ﻋﻦ ﺳﻌﻴﺪ ﺑﻦ ﺟﺒﻴﺮ
ﻭﻋﻜﺮﻣﺔ ﻋﻦ ﺍﺑﻦ ﻋﺒﺎﺱ
ﻗﺎﻝ: ﺍﺟﺘﻤﻊ ﻋﻠﻴﺔ ﻣﻦ ﺍﺷﺮﺍﻑ
ﻗﺮﻳﺶ ﻭﻋﺪﺩ ﺃﺳﻤﺎﺀﻫﻢ ﺑﻌﺪ
ﻏﺮﻭﺏ ﺍﻟﺸﻤﺲ ﻋﻨﺪ ﻇﻬﺮ
ﺍﻟﻜﻌﺒﺔ، ﻓﻘﺎﻝ ﺑﻌﻀﻬﻢ ﻟﺒﻌﺾ :
ﺍﺑﻌﺜﻮﺍ ﺍﻟﻰ ﻣﺤﻤﺪ ﻓﻜﻠﻤﻮﻩ،
ﻭﺧﺎﺻﻤﻮﻩ ﺣﺘﻰ ﺗﻌﺬﺭﻭﺍ
ﻓﻴﻪ، ﻓﺒﻌﺜﻮﺍ ﺍﻟﻴﻪ ﺍﻥ ﺍﺷﺮﺍﻑ
ﻗﻮﻣﻚ ﻗﺪ ﺍﺟﺘﻤﻌﻮﺍ ﻟﻚ
ﻟﻴﻜﻠﻤﻮﻙ، ﻓﺠﺎﺀﻫﻢ ﺭﺳﻮﻝ
ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ
ﺳﺮﻳﻌﺎ، ﻭﻫﻮ ﻳﻈﻦ ﺍﻧﻪ ﻗﺪ
'ﺑﺪﺍ ﻟﻬﻢ ﻓﻲ ﺃﻣﺮﻩ ﺑﺪﺀ، ﻭﻛﺎﻥ
ﺣﺮﻳﺼﺎ ﻳﺤﺐ ﺭﺷﺪﻫﻢ ﻭﻳﻌﺰ
ﻋﻠﻴﻪ ﻋﻨﺘﻬﻢ، ﺣﺘﻰ ﺟﻠﺲ
ﺍﻟﻴﻬﻢ. ﻓﻘﺎﻟﻮﺍ: ﻳﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﺍﻧﺎ
ﻗﺪ ﺑﻌﺜﻨﺎ ﺇﻟﻴﻚ ﻟﻨﻌﺬﺭ ﻓﻴﻚ،
ﻭﺍﻧﺎ ﻭﺍﻟﻠﻪ ﻻ ﻧﻌﻠﻢ ﺭﺟﻼ ﻣﻦ
ﺍﻟﻌﺮﺏ ﺍﺩﺧﻞ ﻋﻠﻰ ﻗﻮﻣﻪ ﻣﺎ
ﺃﺩﺧﻠﺖ ﻋﻠﻰ ﻗﻮﻣﻚ؛ ﻟﻘﺪ
ﺷﺘﻤﺖ ﺍﻵﺑﺎﺀ ﻭﻋﺒﺖ ﺍﻟﺪﻳﻦ،
ﻭﺳﻔﻬﺖ ﺍﻵﻟﻬﺔ ﻭﻓﺮﻗﺖ
ﺍﻟﺠﻤﺎﻋﺔ، ﻭﻣﺎ ﺑﻘﻲ ﻣﻦ ﻗﺒﻴﺢ
ﺍﻻ ﻭﻗﺪ ﺟﺌﺘﻪ ﻓﻴﻤﺎ ﺑﻴﻨﻨﺎ
ﻭﺑﻴﻨﻚ ..)).
Ma'ana: ((Daga Sa'id
Daga Jubair da Ikrimah,
daga Dan Abbas ya ce:
Shugabannin
Quraishawa sun hadu a
Dakin Ka'abah, sannan
suka aika wa Annabi
mai tsira da amincin
Allah cewa suna
bukatar zama da shi,
nan-da-nan Annabi mai
tsira da amincin Allah ya
je ya same su saboda
tsammanin da yake yi
na cewa za su
musulunta ne, domin
yana son musu alheri,
kuma ba ya son abin da
zai wahalce su. Da ya zo
ya zauna a inda suke sai
suka ce da shi: Ya
Muhammad! Lalle, mun
aika Maka ne domin mu
yanke uzurinmu gare
ka, wallahi mu ba mu
taba ganin wani mutum
daga cikin Larabawa da
ya kawo musiba cikin
jama'arsa, kamar yadda
ka kawo musiba cikin
jama'arka ba. Hakika ka
zagi iyayenmu, kuma ka
aibanta addininmu,
sannan ka maida
mahankaltanmu
wawaye, ka kuma zagi
allolinmu, ka raba
kawunan jama'armu.
Babu dai wani
mummunan abu da ya
rage wanda ba ka
sanya shi tsakaninmu
ba..)).
Kun ga dai abin mamaki
karara a nan,
Quraishawa dai kafurai
ne masu bautar
gumaka, mashaya giya,
maciya riba, masu
aikata kusan dukkan
nau'i na sabo, amma
kuma su ne suka sa
Annabi a gaba suna
zazzaro masa
wadannan maganganu!!
Suna cewa shi mai raba
kawunan jama'a ne
saboda kawai ya ce da
su su bi Addinin gaskiya,
su kuma lazimci gaskiya
su daina karya, da
hasada, da hikdu, su
daina karban umurnin
kowa matukar dai ya
saba wa umurnin Allah
Madaukakin Sarki.
Wannan ita ce al'adar
karkatattu cikin ko
wane zamani, sawa'un
kafurai ne masu bautar
gumaka, ko kuwa
Yahudawa ne da
Nasara, ko kuwa cikin
jumlar Musulmi ne suke.
A lokacin da Sheik
Muhammad Dan
Abdullwahhab, ya fara
yi wa jama'arsa wa'azin
su daina ayyuka irin na
shirka da bidi'ah, su
tuba su yi riko da
Alkur'ani da Sunnah,
haka da yawa daga cikin
masu mulkinsu, da
malamansu da jahilansu
suka yi caa a kansa,
suka cutar da shi cuta
mai yawa!
A lokacin da Sheik
Uthmanu Dan Fodiyo ya
fara yi wa jama'ar
kasar Hausa wa'azin su
bar ayyuka irin na
shirka, da bidi'ah, su
dawo zuwa ga Alkur'ani
da Sunnah, da yawa
daga cikin sarakuna da
malaman zamaninsa da
jahilan da ke tare da su,
sun yi ta musguna
masa ta hanyoyi daban-
daban.
A lokacin da Sheik
Abubakar Mahmud Gumi
ya fara yin wa'azi kan
barnar da take gudana a
zamaninsa ta bidi'ar
sufaye da abin da ya yi
kama da haka, ya kuma
shiga rubuce-rubuce
domin bayyanar da
gaskiyar lamari cikin
haka, lalle sarakuna, da
malamai, da kuma
jahilan da ke tare da su
sun yi caa a kansa, sun
yi kokarin kashe shi ba
sau daya ba, ba sau
biyu ba, sun yi kokarin
bata masa suna ta
hanyoyi daban daban.
Allah Ya tabbatar da
dugaduganmu a kan
gaskiya da adalci, Ya
kuma raba al'ummarmu
da sharrin azzalumai na
boye da na bayyane.
Ameen.
April 13 at 12:21pm ·

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s