FARKON SHIGA ALJANNAH (SAWW).

FARKON SHIGA
ALJANNAH (SAWW).
*************
*************
******
Farkon wanda zai shiga
Aljannah aranar
Alqiyamah shine
Annabinmu
Muhammadu (saww)
kamar yadda Imamu
Muslim ya ruwaito daga
Sayyiduna Anas bn Malik
(rta) yace Manzon Allah
(saww) yace:
"ZAN ZO KOFAR
ALJANNAH ARANAR
ALQIYAMAH, SAI IN
KWANKWASA, SAI MAI
TSARONTA (WATO
MALA'IKA RIDHWAN)
YACE : "KAI WANENE?".
ZAN CE MASA
"MUHAMMADU NE". SAI
YACE : "SABODA KAI
AKA UMURCENI KAR IN
BUDE MA WANI KAFIN
KA".
Acikin wata ruwayar
kuma yace: "NINE NAFI
DUKKAN ANNABAWA
YAWAN MABIYA, KUMA
NINE FARKON WANDA
ZAI KWANKWASA
(KOFAR ALJANNAH)."
(Muslim ne ya
ruwaitoshi).
Acikin ruwayar Abu
Hurairah kuma Annabi
(saww) yace: "MUNE NA
KARSHE KUMA MUNE NA
FARKO ARANAR
ALKIYAMAH. KUMA
MUNE FARKON
WADANDA ZASU SHIGA
ALJANNAH".
(Bukhariy da Muslim ne
suka ruwaitoshi).
Akwai kuma hadisan da
suka nuna cewar
Talakawan wannan
al'ummar sai sun riga
mawadata (Masu kudi)
shiga Aljannah, kamar
yadda Imamu Ahmad
da Tirmidhiy suka
ruwaito Daga Sayyiduna
Abu Hurairah (ra) yace
Manzon Allah (saww)
yace:
"TALAKAWAN
MUSULMAI ZASU RIGA
SHIGA ALJANNAH KAFIN
MAWADATANSU DA
TSAWON RABIN WUNI
GUDA, WATO SHEKARU
DARI BIYAR KENAN (500
years).
Imamu Muslim kuma ya
ruwaito daga Sayyiduna
Abdullahi bn Amru bn
Al-Aas (ra) yace
Manzon Allah (saww)
yace:
"TALAKAWA DAGA
CIKIN SAHABBAN DA
SUKAYI HIJIRA, ZASU
RIGA MAWADATANSU
SHIGA ALJANNAH
ARANAR ALKIYAMAH
DA TSAWON SHEKARU
ARBA'IN".
(Muslim ne ya
ruwaitoshi).
Don haka ya kai 'dan
uwa, Kada wadata tasa
ka rika yin Girman kai ko
Alfahari. Domin girman
kai babu inda zai kaika
sai wuta. Kuma koda ka
tsaya ka bi Allah, sai
Talakawa sun rigaka
shiga Aljannah kamar
yadda Sahihan hadisan
nan suka tabbatar.
Ba wani abu ne zai
kawo maka wannan
jinkirin shiga Aljannar
ba, illa hisabin dukiyarka
da za'ayi ma. Domin ba
zaka gushe daga gaban
Zatin Allah ba, sai an
tambayeka akan
kowanne kwabo da Sisi
da Naira da dollars : Ta
ina ka sameta? Kuma ta
ina ka 'batar da ita?.
Acikin bin Allah, ko
kuma bin sha'awar son
zuciyarka?
Shi kuwa Talaka bashi
da komai sai ransa. Don
haka babu abin
tambaya sosai akansa.
Amma duk da haka ina
jan hankalin 'Yan uwana
Talakawa cewa mu
Zage damtse wajen
neman ilimi da bauta ma
Allah ta hanyoyin da
suka dace domin samun
babban rabo awajen
Allah. Kar mu sake
wasu sun fimu jin dadi
aduniya, kuma alahirar
ma su sha gabanmu.
Hakika mun gode ma
Allah da ya sanyamu
acikin wannan al'ummar
ta Annabi Muhammad
(saww). Allah yasa
muna daga cikin sahun
farkon wadanda zasu
shiga Aljannah aranar
Alqiyamah. Acikin
Makobtaka da
Masoyinmu (saww).
DAGA ZAUREN FIQHU
WHATSAPP
(15-09-1437)
20-06-2016.

Advertisements

TSARABAN RAMADAN (Dr. Ibrahim jalo jalingo)

Ibrahim Jalo Jalingo
TSARABAR RAMADAN:
(1) Shaikhul Islam Ibnu
Taimiyyah ya ce cikin
Majmuu'ul Fataawa
6/505:-
(( ﻭﺍﻟﺨﻴﺮ ﻛﻞ ﺍﻟﺨﻴﺮ ﻓﻲ
ﺍﺗﺒﺎﻉ ﺍﻟﺴﻠﻒ ﺍﻟﺼﺎﻟﺢ
ﻭﺍﻻﺳﺘﻜﺜﺎﺭ ﻣﻦ ﻣﻌﺮﻓﺔ
ﺣﺪﻳﺚ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ
ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻭﺍﻟﻔﻘﻪ ﻓﻴﻪ
ﻭﺍﻻﻋﺘﺼﺎﻡ ﺑﺤﺒﻞ ﺍﻟﻠﻪ
ﻭﻣﻼﺯﻣﺔ ﻣﺎ ﻳﺪﻋﻮ ﺍﻟﻰ
ﺍﻟﺠﻤﺎﻋﺔ ﻭﺍﻷﻟﻔﺔ ﻭﻣﺠﺎﻧﺒﺔ ﻣﺎ
ﻳﺪﻋﻮ ﺍﻟﻰ ﺍﻟﺨﻼﻑ ﻭﺍﻟﻔﺮﻗﺔ
ﺍﻻ ﺍﻥ ﻳﻜﻮﻥ ﺃﻣﺮﺍ ﺑﻴﻨﺎ ﻗﺪ
ﺍﻣﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺭﺳﻮﻟﻪ ﻓﻴﻪ ﺑﺄﻣﺮ
ﻣﻦ ﺍﻟﻤﺠﺎﻧﺒﺔ، ﻓﻌﻠﻰ ﺍﻟﺮﺃﺱ
ﻭﺍﻟﻌﻴﻦ )).
Ma'ana: ((Sannan alheri
kuma dukkan alheri
yana cikin bin magabata
na gari, da kuma
yawaita ilmin hadithin
Manzon Allah mai tsira
da amincin Allah, da
kyakkyawar fahimta
cikinsa, da yin riko da
igiyar Allah, da lazimtar
abin da ke kira zuwa ga
jama'a da hadin kai, da
nisantar abin da ke kira
zuwa ga sabani da
rarraba, sai fa abin da
ya kasance al'amari ne
bayyananne da tabbas
Allah da manzonSa ne
suka yi umurni cikinsa
da wani umurni na a
nisanta, to wannan
kam biyayya sau da
kafa)).
(2) Alhaafiz Ibnu Rajab
ya ce cikin littafinsa
Alhikamul Jadiiratu Bil
Izaa'ah shafi na 12:-
(( ﻓﺎﻟﻮﺍﺟﺐ ﻋﻠﻰ ﻛﻞ ﻣﻦ ﺑﻠﻐﻪ
ﺍﻣﺮ ﺍﻟﺮﺳﻮﻝ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ
ﻭﺳﻠﻢ ﻭﻋﺮﻓﻪ ﺍﻥ ﻳﺒﻴﻨﻪ ﻟﻼﻣﺔ
ﻭﻳﻨﺼﺢ ﻟﻬﻢ ﻭﻳﺄﻣﺮﻫﻢ ﺑﺎﺗﺒﺎﻉ
ﺃﻣﺮﻩ ﻭﺍﻥ ﺧﺎﻟﻒ ﺫﻟﻚ ﺭﺃﻱ
ﻋﻈﻴﻢ ﻣﻦ ﺍﻻﻣﺔ، ﻓﺎﻥ ﺍﻣﺮ
ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ
ﻭﺳﻠﻢ ﺍﺣﻖ ﺍﻥ ﻳﻌﻈﻢ
ﻭﻳﻘﺘﺪﻯ ﺑﻪ ﻣﻦ ﺭﺃﻱ ﺍﻱ
ﻣﻌﻈﻢ ﻗﺪ ﺧﺎﻟﻒ ﺃﻣﺮﻩ ﻓﻲ
ﺑﻌﺾ ﺍﻻﺷﻴﺎﺀ ﺧﻄﺎ، ﻭﻣﻦ
ﻫﻨﺎ ﺭﺩ ﺍﻟﺼﺤﺎﺑﺔ ﻭﻣﻦ ﺑﻌﺪﻫﻢ
ﻋﻠﻰ ﻛﻞ ﻣﺨﺎﻟﻒ ﺳﻨﺔ
ﺻﺤﻴﺤﺔ، ﻭﺭﺑﻤﺎ ﺍﻏﻠﻈﻮﺍ ﻓﻲ
ﺍﻟﺮﺩ ﻻ ﺑﻐﻀﺎ ﻟﻪ، ﺑﻞ ﻫﻮ
ﻣﺤﺒﻮﺏ ﻋﻨﺪﻫﻢ ﻣﻌﻈﻢ ﻓﻲ
ﻧﻔﻮﺳﻬﻢ، ﻭﻟﻜﻦ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ
ﺍﺣﺐ ﺍﻟﻴﻬﻢ، ﻭﺃﻣﺮﻩ ﻓﻮﻕ ﺍﻣﺮ
ﻛﻞ ﻣﺨﻠﻮﻕ، ﻓﺈﺫﺍ ﺗﻌﺎﺭﺽ
ﺍﻣﺮ ﺍﻟﺮﺳﻮﻝ ﻭﺃﻣﺮ ﻏﻴﺮﻩ
ﻓﺄﻣﺮ ﺍﻟﺮﺳﻮﻝ ﺍﻭﻟﻰ ﺍﻥ
ﻳﻘﺪﻡ ﻭﻳﺘﺒﻊ )).
Ma'ana: ((Abin da ke
wajibi a kan dukkan
wanda umurnin manzon
Allah mai tsira da
amincin Allah ya same
shi kuma ya san shi to
ya bayyana shi ga
Al'umma, ya musu
nasiha, ya umurce su da
bin umurninsa koda
kuwa hakan ya saba
wa ra'ayin wani babba
cikin Al'umma, domin
umurnin Manzon Allah
shi ya fi cancanta da a
girmama kuma a yi koyi
da shi a kan ra'ayin wani
wanda ake girmamawa
da ya saba wa
umurninsa cikin sashin
wasu abubuwa a bisa
kure, daga ma nan ne
Sahabbai da wadanda
ke bayansu suke yin
raddi a kan dukkan mai
saba wa Sunnah
Sahihiya, sau da dama
ma sukan yi kaushi cikin
raddin, ba kuma saboda
nuna kiyayya gare shi
ba, a'a yana nan abin so
a gare su kuma abin
girmamawa a cikin
rayukansu, to sai dai
manzon Allah shi ya fi
soyuwa a wurin su,
kuma umurninsa yana
sama da umurnin ko
wace halitta, saboda
haka idan umurnin
Manzo ya yi karo da
umurnin waninsa,
umurnin Manzon ne ya fi
cancanta da a gabatar
kuma a bi)).
(3) Shehu Uthmanu Dan
Fodiyo ya ce cikin
littafinsa Ihyaa'us
Sunnah Wa Ikhmaadul
Bid'ah shafi na 8:-
(( ﻗﺪ ﺍﻧﻌﻘﺪ ﺍﻹﺟﻤﺎﻉ ﻋﻠﻰ ﺍﻥ
ﺁﺭﺍﺀ ﺍﻟﻤﺠﺘﻬﺪﻳﻦ ﻛﻠﻬﺎ
ﻣﺴﺎﻟﻚ ﺍﻟﻰ ﺍﻟﺠﻨﺔ ﻭﻃﺮﻕ ﺍﻟﻰ
ﺍﻟﺨﻴﺮﺍﺕ، ﻓﻤﻦ ﺳﻠﻚ ﻣﻨﻬﺎ
ﻃﺮﻳﻘﺎ ﻭﺻﻠﻪ ﺍﻟﻰ ﻣﺎ ﻭﺻﻠﻮﺍ
ﺍﻟﻴﻪ ﺣﻘﺎً، ﻭﻣﻦ ﻋﺪﻝ ﻋﻨﻪ
ﻗﻴﻞ ﻟﻪ ﺳﺤﻘﺎ، ﻭﻳﺠﻮﺯ
ﺗﻘﻠﻴﺪﻫﻢ ﻓﻲ ﻛﻞ ﺭﺃﻱ ﺍﻻ ﻣﺎ
ﺧﺎﻟﻒ ﻧﺺ ﺍﻟﻘﺮﺍﻥ ﺍﻭ ﻧﺺ
ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ ﺍﻭ ﺍﻟﻘﻮﺍﻋﺪ ﺍﻭ
ﺍﻹﺟﻤﺎﻉ ﺍﻭ ﺍﻟﻘﻴﺎﺱ ﺍﻟﺠﻠﻲ
ﻓﺎﻓﻬﻢ )).
Ma'ana: ((Hakika Ijmaa'i
ya kullu a kan cewa lalle
ra'ayoyin Mujtahidai
dukkansu hanyoyi ne
zuwa Aljannah, kuma
hanyoyi ne zuwa
alkhairai, wanda duk ya
bi wata hanya daga
cikinsu to tabbas za ta
kai shi zuwa inda suka
kai, wanda kuma ya
karkata ga barin hakan
sai a ce da shi tir. Kuma
yin koyi da su na halatta
cikin dukkan wani ra'ayi,
sai dai abin da ya saba
wa nassin Alkur'ani, ko
nassin Hadithi, ko
Ka'idodi, ko Ijmaa'i, ko
Bayyanannen Kiyasi, ka
fahimta)).
Muna rokon Allah
Madaukakin Sarki da Ya
cusa mana son
sahihiyar Sunnah da
kuma son yin aiki da ita
cikin dukkan wani abu
na Aqiidah, ko Ibaadah,
ko Mu'aamalah. Ameen.

FATAWOYIN LAYYA2(Sheikh Abdulwahhab Abdullah)

A wannan
darasi za mu
amsa
tambayoyi
kamar haka;
*Tambaya:
Mene ne
sharuddan
layya?
AMSA:
Yana daga cikin
sharuddan
layya:
abin da za a
yanka, lallai ya
kasance daga
cikin “bahimatul
anʿām” (dabbobin
ni’ima), irin su:
rakuma da
shanu da awaki
da
tumaki). Domin
haka, ba ya
cikin
sharuddan
layya, a yi ta da
namun
daji, kuma ba
za a yanka kaji
da
sauran
tsuntsaye ba,
kamar yadda
wasu daga
cikin ‘yan
Zahiriyyah
suka tafi a kai.
Dalili kuwa
fadin
Ubangiji
subhanahu wa
ta’ala
cewa:
ﻭﻟﻜﻞ ﺃﻣﺔ ﺟﻌﻠﻨﺎ
ﻣﻨﺴﻜﺎ ﻟﻴﺬﻛﺮﻭﺍ
ﺍﺳﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﻣﺎ
ﺭﺯﻗﻬﻢ ﻣﻦ ﺑﻬﻴﻤﺔ
ﺍﻟﺄﻧﻌﺎﻡ )34 ( …
ﺍﻟﺤﺞ: ٣٤
Ma’ana:
Kowacce
al’umma mun
sanya
musu ibadunsu,
domin su
ambaci
sunan Allah a
bisa abin da
(Allah)
ya arzuta su da
shi daga cikin
dabbobin
ni’ima…
Wannan aya ta
nuna cewa,
Ubangiji
subhanahu wa
ta’ala ya
ambaci
dabbobin ni’ima
ne, kuma
ya nuna cewa
lallai ne idan za
a
yanka su, a
ambaci
sunansa.
Amma ayar ba
ta ambaci
cewa ana
iya layya da
namun daji ba,
ko
tsuntsaye,
kamar kaji da
sauransu.
Kuma koda a
cikin dabbobin
ni’ima
din ba a
yankawa sai
wacce ta cika
wadannan
sharuddan:
1- Shanu: Sai
sun cika
shekara
biyu zuwa
sama.
2-Raquma: Sai
sun cika
shekara
biyar zuwa
sama.
3-Tumaki da
Awaki: Sai sun
cika
shekara daya
zuwa sama. Sai
dai
idan ya
ta’azzara ba a
samu
shekararriya
ba, to babu laifi
a
yanka wacce
ba ta shekara
ba
amma ta kusa
cika shekara a
cikin
raguna ko
awaki (watau
jaz’a),
saboda hadisin
da aka karbo
daga
Jabir Ibn
Abdullah
radhiyallahu
anhuma ya ce:
Manzon Allah
sallallahu alaihi
wa sallama ya
ce:
ﻟﺎ ﺗﺬﺑﺤﻮﺍ ﺇﻟﺎ
ﻣﺴﻨﺔ ﺇﻟﺎ ﺃﻥ
ﻳﻌﺴﺮ ﻋﻠﻴﻜﻢ
ﻓﺘﺬﺑﺤﻮﺍ
ﺟﺬﻋﺔ ﻣﻦ ﺍﻟﻀﺄﻥ.
Ma’ana:
Kada ku yanka
sai
shekararriya,
sai dai idan ya
gagareku , sai
ku
yanka wacce
ake kira jaz’a
daga
raguna.
Haka kuma,
ana so dabbar
da za a
yi layya da ita
ta kasance
kubutacciya
daga aibu.
Saboda
hadisin da aka
karbo daga
Bara’u
Ibn Azib
radhiyallahu
anhuma ya
ce: Manzon
Allah sallallahu
alaihi
wa sallama ya
ce:
ﻻ ﻳﻀﺤﻰ ﺑﺎﻟﻌﺮﺟﺎﺀ
ﺑﻴﻦ ﻇﻠﻌﻬﺎ ﻭﻻ
ﺑﺎﻟﻌﻮﺭﺍﺀ ﺑﻴﻦ
ﻋﻮﺭﻫﺎ ﻭﻻ
ﺑﺎﻟﻤﺮﻳﻀﺔ ﺑﻴﻦ
ﻣﺮﺿﻬﺎ ﻭﻻ
ﺑﺎﻟﻌﺠﻔﺎﺀ
ﺍﻟﺘﻲ ﻻ ﺗﻨﻘﻲ
Ma’ana:
Ba a yanka
ramammiya
wacce
ramarta ta
bayyana, ko
gurguwa
wacce
gurguntakarta
ta bayyana,
ko mara lafiyar
da rashin
lafiyarta
ta bayyana, Ko
me ido daya.
Banda
wadannan
siffofi na
dabbobi, akwai
wasu siffofin.
saidai
hadisan ba su
inganta ba, don
haka ba mu
kawo su a nan
ba.
Kuma lallai ne
abinda za a
yanka
na layya, ya
kasance
mallakarsa
aka yi ta
hanyar halal, ba
ta hanyar
haram ba.
Wato wajibi ne
ya
kasance ba na
sata ko kwace
ba
ne, kuma ba
dabbar da aka
bayar
jingina ko
amana ba ce.
Kuma ya
kamata mai yin
layya ya
sani cewa ba
cewa aka yi ya
yi
azumi ko rikon
baki ba. Domin
haka, ba a hana
shi ci ko shan
abin
sha ba
matukar yana
bukata.
*Tambaya:
Yaushe ya
kamata a
yanka abin
layya?
AMSA:
Jumhurun
malamai sun
tafi a kan
cewa, ana
yanka abin
layya ne,
bayan sallar idi
ko da liman bai
yanka ba.
Dalilinsu kuwa
shi ne
fadin Manzon
Allah sallallahu
alaihi
wa sallama
cewa:
ﻣﻦ ﻛﺎﻥ ﺫﺑﺢ
ﺃﺿﺤﻴﺘﻪ ﻗﺒﻞ ﺃﻥ
ﻳﺼﻠﻲ ﺃﻭ ﻧﺼﻠﻲ
ﻓﻠﻴﺬﺑﺢ ﻣﻜﺎﻧﻬﺎ
ﺃﺧﺮﻯ ﻭﻣﻦ ﻛﺎﻥ
ﻟﻢ ﻳﺬﺑﺢ ﻓﻠﻴﺬﺑﺢ
ﺑﺎﺳﻢ ﺍﻟﻠﻪ .
Ma’ana:
Wanda ya
yanka abin
layyarsa
kafin sallarmu,
to, ya sake
yanka
wata dabbar
maimakonta
bayan
sallar idi,
wanda kuma
bai yanka
ba (sai bayan
sallarmu), to,
ya
yanka da sunan
Allah.
Saidai kuma
Imam Mālik ya
tafi a
kan sabanin
abinda jamhur
suka
tafi akai inda
ya ke cewa:
Ba a yanka abin
layya sai bayan
liman ya yanka
nasa.
Dalilinsa kuwa
shi ne, hadisin
da
aka karbo daga
Jabir Ibn
Abdullah
radhiyallahu
anhu ya ce,
ﺻﻠﻰ ﺑﻨﺎ ﺍﻟﻨﺒﻲ
ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ
ﻭﺳﻠﻢ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻨﺤﺮ
ﺑﺎﻟﻤﺪﻳﻨﺔ ﻓﺘﻘﺪﻡ
ﺭﺟﺎﻝ ﻓﻨﺤﺮﻭﺍ
ﻭﻇﻨﻮﺍ ﺃﻥ ﺍﻟﻨﺒﻲ
ﺻﻠﻰ
ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻗﺪ
ﻧﺤﺮ ﻓﺄﻣﺮ ﺍﻟﻨﺒﻲ
ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ
ﻭﺳﻠﻢ ﻣﻦ ﻛﺎﻥ
ﻧﺤﺮ ﻗﺒﻠﻪ ﺃﻥ ﻳﻌﻴﺪ
ﺑﻨﺤﺮ ﺁﺧﺮ ﻭﻟﺎ
ﻳﻨﺤﺮﻭﺍ ﺣﺘﻰ ﻳﻨﺤﺮ
ﺍﻟﻨﺒﻲ. ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ
ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ
Ma’ana:
Mun yi salla
tare da Manzon
Allah
sallallahu alaihi
wa sallama a
Madina ranar
babbar salla,
sai
wasu mazaje
suka je suka yi
yanka, suna
tsammani
Manzon
Allah sallallahu
alaihi wa
sallama
ya yi yanka, sai
Manzon Allah
sallallahu alaihi
wa sallama ya
ce:
duk wanda ya
yi yanka kafin
na yi,
to ya sake
yankansa. Ya
kara da
cewa: Kada su
yanka har sai
Annabi
sallallahu alaihi
wa sallama
ya yanka.
Wannan shi ne
zance mafi
rinjaye
domin wannan
hadisin da
Imam
Malik ya kafa
hujja da shi ya
fada
karara cewar
ba’a yanka sai
bayan
liman yayi
yankan sa,
sabanin
dalilin jamhur.
Don haka sai
mutum ya
hakura har
liman ya
yanka. Idan
kuma mutum
yana
nesa da gari ne,
sai ya kintaci
lokacin da ya
kamata a ce
liman ya
yanka dabbar
layyarsa, sai ya
yanka tasa.
Wanda kuma
ya yanka
kafin salla, to
namansa ba na
layya
ba ne, ya zama
naman miya
kenan, ko ya
sani ko bai sani
ba.
Saboda haka
sai ya sake
yanka
wata
maimakonta.
Dalili kuwa shi
ne: wani sahabi
Uwaīmir Ibn
Ashkar
radhiyallahu
anhum ya taba
yanka dabbar
layyarsa kafin
sallar īdī, sai
Manzon Allah
sallallahu alaihi
wa
sallama ya ce:
ﺃﻋﺪ ﺃﺿﺤﻴﺘﻚ .
Ma’ana:
Ka sake yanka
wata a
maimakonta.
A nan Annabi
sallallahu alaihi
wa
sallam bai
tambaye shi ko
ya sani,
ko bai sani ba.
Wallahu a’alam!
*Tambaya:
A ina ya
kamata liman
ya yanka
abin layyarsa a
sunnance?
AMSA:
A bisa koyarwa
irin ta Manzon
Allah sallallahu
alaihi wa
sallama
liman zai yanka
abin layyarsa
ne a
filin idi, domin
al’umma su
shaida,
kuma su sami
damar yin ta su
layyar, ba tare
da wani
kokwanto
ba. Dalili kuwa
shi ne hadisin
Jabir
radhiyallahu
anhum ya ce:
ﺷﻬﺪﺕ ﻣﻊ ﺭﺳﻮﻝ
ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ
ﻭﺳﻠﻢ
ﺍﻷﺿﺤﻰ ﺑﺎﻟﻤﺼﻠﻰ
ﻓﻠﻤﺎ ﻗﻀﻰ ﺧﻄﺒﺘﻪ
ﻧﺰﻝ ﻣﻦ
ﻣﻨﺒﺮﻩ ﻭﺃﺗﻲ
ﺑﻜﺒﺶ ﻓﺬﺑﺤﻪ
ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ
ﺍﻟﻠﻪ
ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺑﻴﺪﻩ .
Ma’ana:
Na halarci idin
babbar salla
tare da
Manzon Allah
sallallahu alaihi
wa
sallama. Bayan
ya gama
hudubarsa, sai
ya sauka daga
kan
minbarinsa, aka
kawo masa
ragon
layyarsa, sai ya
yanka shi da
hannunsa (mai
albarka).
Haka kuma an
karbo wani
hadisin
daga Abdullahi
Ibn Umar
radhiyallahu
anhum ya ce:
ﺃﻥ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ
ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻛﺎﻥ
ﻳﺬﺑﺢ ﺃﺿﺤﻴﺘﻪ
ﺑﺎﻟﻤﺼﻠﻰ ﻭﻛﺎﻥ
ﺍﺑﻦ ﻋﻤﺮ ﻳﻔﻌﻠﻪ.
Ma’ana:
Hakika Manzon
Allah sallallahu
alaihi wa
sallama ya
kasance yana
yanka abin
layyarsa a filin
idi.
Saboda haka ni
ma na kasance
ina
aikata hakan.
Don haka sai
limamai su yi
koyi.

FALALAR SAHABBAI ( Sheikh Abdulwahhab Abdullah)

Alhamdu lillahi
rabbil A’lamin,
wa
Sallallahu wa
sallama ala
Nabiyyina
Muhammadin
Wa ala a’alihi
wa
sahbihi ajma’in.
Amma ba’ad,
hakika hadisi ya
tabbata
daga Anas Bin
Malik
radhiyallahu
anhu ya ce;
ﻛﺎﻧﺖ ﺍﻷﻧﺼﺎﺭ ﻳﻮﻡ
ﺍﻟﺨﻨﺪﻕ ﺗﻘﻮﻝ
ﻧﺤﻦ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﺑﺎﻳﻌﻮﺍ
ﻣﺤﻤﺪﺍ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺠﻬﺎﺩ
ﻣﺎ ﺣﻴﻴﻨﺎ ﺃﺑﺪﺍ
ﻓﺄﺟﺎﺑﻬﻢ
ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻻ ﻋﻴﺶ ﺇﻻ
ﻋﻴﺶ ﺍﻵﺧﺮﻩ
ﻓﺄﻛﺮﻡ ﺍﻷﻧﺼﺎﺭ
ﻭﺍﻟﻤﻬﺎﺟﺮﻩ
Ma’ana
Ansar sun
kasance a
yayin da suke
haka ramin
khandaku suna
cewa;
“Mu ne
wadanda suka
yiwa Manzon
Allah sallallahu
alaihi wa
sallama
mubaya’a akan
jihadi muddin
muna
raye har
abada”. Sai
Manzon Allah
sallallahu alaihi
wa sallama ya
ce;
“Ya Ubangiji
babu wata
rayuwa sai
rayuwar lahira.
Ya Allah ka
girmama Ansar
da
muhajirai”
‘Yan uwa
wannan ya
nuna bai
halatta
wani mutun ya
zagi sahabbai
wadan
suke kaunar
Manzon Allah
sallallahu
alaihi wa
sallama shima
yake
kaunarsu ba,
duk wanda ku
ka ji yana
zaginsu ku Sani
wannan
tababbe ne,
yayi asara
duniya da lahira.
wa Sallallahu
wa sallama ala
Nabiyyina
Muhammadin
Wa ala
a’alihi wa
sahbihi ajma’in.

Mece ce alamar son Manzon Allah (S.A.W)? ( Sheikh Abdulwahhab Abdullah)

Amsa:
Kafin mu amsa
wannan
tambayar ya
na da kyau
muyi wa
kanmu
wadannan
tambayoyin:
-Mece ce
soyayya?
-Mene ne yake
sa a so
mutum?
-Mene ne rabe-
raben so?
-Mece ce
alamar so?
Daga nan kuma
sai musan
mece ce
hakikanin
soyayyar
Manzon Allah
(S.A.W)?
Mece ce
soyayya?
Hafiz Ibin hajar
babban
malamin
hadisin nan da
yayi sharhin
sahihul
bukhari yace:
haqiqanin
soyayya
awajen
masana; wata
aba ce da ba’a
iya
bayyanata,mai
yinta kawai shi
ne
ya san yadda
yake
jinta,amma
baya
yiwuwa ya
furta yadda
take.
Mallam ibnul
Qayyim yace:
Ba’a
bayyana
soyayya da
wani bayani
fiye
da ace mata
soyayya. Duk
abin da
za’a bayyana
game da ita ba
zai kara
mata komai ba
sai
buya,bayaninta
kawai shi ne
samuwarta, ba
kuma a
sifantata da
wata siffa fiye
da soyyya.
Mutane kawai
suna yin
maganane
game da abinda
yake jawota,da
abinda yake
wajabta ta, da
alamominta da
shaidunta da
abinda
ake samu idan
anyi ta.
Mene ne yake
sa aso mutum
a
dabi’ance?
Akan so
mutum a
dabi’ance
saboda
abubuwa masu
yawa. Kadan
daga
ciki sune kamar
haka:
– Akan so
mutum don
yawan
kyautatawarsa,
-ko don
kyawun
surarsa wadda
take
burge mutane,
– ko don cikar
kamalarsa,
-ko baiwar ilmi,
ko mulki, ko
dukiya,
ko wani abu
wanda yake
burge
mutane.
Haka kuma
akan so
mutum don
kyawawan
halayensa na
gari ko kuma
saboda
amfanarwarsa
ga al’umma.
Manzon Allah
(S.A.W) kuwa
ya
tattare dukkan
wadannan
sababbai da
ninkin-ba-
ninkinsu
wadanda suke
sa
a so mutum.
Don haka ya
zama wajibi a
so shi fiye
da kowane irin
mahluki.
Tambaya;
Menene rabe
raben so?
Amsa;
Imam ibn
bazzar da alkali
Iyadh da
wasunsu sunce
soyayya ta
kasu kaso
uku:
1)- Soyayya
don
girmamawa da
taimakawa;
kamar
soyayyar ‘ya
‘ya ga
iyayensu.
2)- soyayyar
tausayi da jin
kai;
kamar
soyayyar iyaye
ga ‘ya’yansu
3- Soyayyar
bani in baka; ita
ce ke
sanya
kyautatawa
wanda ya
kyautata
maka; kamar
soyayyar da
sauran
al’umma suke
wa junansu.
Idan muka kalli
wadannan
rabe-rabe
da sababbai da
suke sa a so
mutum
zamu ga cewa
Manzon Allah
(S.A.W)
ya tattare
dukkaninsu.
Don haka ibn
Bazzar yace:
“wanda
yake da
cikakken imani
ya san
Manzon Allah
(S.A.W) ya fi
girman
hakki akansa
fiye da hakkin
kansa
akan kansa,
haka zalika
hakkin
iyayensa da na
‘ya’yansa da na
mutanen
duniya baki
daya.
Domin da imani
da kaunar
Manzon
Allah (S.A.W) ne
Allah ya tserar
da
mu daga wuta
kuma ya
shiryar da mu
daga bata.
Mece ce alamar
son Manzon
Allah
(S.A.W)?
Imam alkali
Iyadh yace:
“kusani, lallai
duk wanda ya
so abu dole zai
fifita
shi akan komai
,kuma zai fifita
binsa
kwabo da
kwabo.
Idan kuwa bai
zama haka ba
to
sonsa ba na
gaskiya ba
ne,da’awar
son kawai yake
yi.
Mai son Manzon
Allah (S.A.W) da
gaske shine
wanda
alamomin
soyayya suke
bayyana a gare
shi
kamar haka:
-Na farkon su
shi ne koyi da
shi.
-Aiki da sunnar
sa.
-Bibiyar
zantukansa da
aiyukansa.
-Kwatanta
umarninsa.
-Nisantar hane-
hanensa.
-Ladabtuwa da
ladabansa, a
halin
wahala da
yalwa,da
nishaxi da
damuwa.
Abinda yake
karfafa
wannan shine
fadin Allah
(S.W.T):
ma’ana:
ka fada musu
ya kai wannan
annabi
mai girma, idan
kun kasance
kuna
son Allah, to ku
bi ni sai Allah ya
so
ku, kuma ya
gafarta
zunubanku.
lallai
Allah mai
yawan gafara
ne mai yawan
jinkai”{al-
imrana:31}
Wannan ayar
ta nuna cewa
biyayya
ita ce matakin
farko na
soyayya.
Sannan alkali ya
ci gaba da
cewa:
Da fifita abin
da ya shar’anta
ko
yakwadaitar da
yinsa fiye da
son
zuciyarka da
sha’awarka.saboda
fadin Allah
s.w.t:
Ma’ana:
“Wadanda suka
riki Madina
wurin
zamansu(al-
ansar) da imani
kafin su
(muhajirun)
suna kaunar
wadanda
suka yi hijira
zuwa garesu,
(wato
manzon Allah
da
muhajirun)kuma
basa jin wani
kyashi a
zuciyarsu
game da abinda
Allah ya bawa
(muhajirai na
falala da
matsayi da
daukaka da
gabata a cikin
Ambato da
matsayi),
kuma suna
fifita su
(muhajirai)
akan kansu ko
da kuwa
suna da
matsananciyar
bukata.”
Imam addabari
da imam
assuyidi
kuwa sun
fassara ayar
da cewa:
“Wadanda suka
riki madina
wurin
zamansu(al-
ansar) da imani
kafin su
(muhajirun)
suna kaunar
wadanda
suka yi hijira
zuwa garesu,
(wato
manzon Allah
da
muhajirun)kuma
basa jin wani
kyashi a
zuciyarsu
game da abinda
Manzon Allah
(S.A.W) ya
bawa
(muhajirai da
shi na
ganima da fai’i)
kuma suna
fifita su
(muhajirai)
akan kansu ko
da kuwa
suna da
matsananciyar
bu tata.”
Sannan alkali
iyadh ya
ambaci hadisi
da isnadinsa
zuwa anas bn
malik
(r.a) yace:
Ma’ana:
ya kai Dan
qaramin Dana,
idan ka
sami iko ka
wayi gari ko ka
yammata
ba tare da wani
kulli a zuciyar
ka
game da wani
ba to ka aikata:
wannan yana
daga
sunnata,wanda
ya
raya sunnata
haqiqa ya
soni.wanda
ya soni zai
kasance tare
da ni a cikin
aljana.
Sai alqali iyadh
yace:wanda ya
siffantu da
waxannan
sifofi da suka
gabata to shi
ne mai
cikakkiyar
soyayya ga
allah da
manzonsa.wanda
kuma yasa va
musu a xaya
daga cikin
abubuwan da
aka ambata to
wannan
soyayyarsa
tauyayyiya
ce,duk da ba
za’a kore
musu soyayyar
gaba daya ba.
Haka dai. yayi
ta kawo
alamomin da
su ke nuna
kaunar Manzon
Allah
(S.A.W) ga
wanda ya
siffantu da su.
Acikin wannan
littafi na sa mai
albarka
(asshifa). Ya
rage wa mai
hankali da
tunani ya kalle
su da idon
basira don ya
ga a da’awar
da yake
yita son
Manzon A
awane aji
yake?
Kuma ya yi wa
kansa adalci
wajen
gane cewa
anya kuwa ba
yaudararsa
ake yi ba wajen
nuna masa abin
da
Manzon Allah
(S.) bai yi ba a
ce
masa shi ne
qaunar Manzon
Allah
(a) ? Allah ka
bamu ganewa
amin.
Wa sallallahu
wa sallama ala
nabiyina
Muhammad wa
ala a’lihi wa
sahbihi ajma’in’.

MARABA DA WATAN RAMADAN •••••••••••••••• [20]

MARABA DA WATAN
RAMADAN
.
•••••••••••••••••••••
[20]•••••••••••••••••••
.
•••• LAILATUL QADR •••
.
•LAILATUL QADR: shine
Qaddararren dare, dare
mai daraja mai girma,
daren alkhayri, dare mai
albarka, dare ne wanda
misali bazai gama
rarrabe abunda wannan
dare ya qunsa ba face
ALLAH (SWT) shine
masani.
.
•••FALALAR DAREN
LAILATUL QADR•••
.
Falalar wannan dare mai
girma ce domin an
shedar da sauqar
al'qur'ani acikinsa, kuma
ALLAH (SWT) Ya
ambace sa acikin
LittafinSa a wurare
daban-daban, daga
cikinsu akwai fadar
ALLAH (SWT):
.
"lallai mu muka sauqar
da shi (Alqur'ani) acikin
daren Lailatul Qadr, me
ya sanar da kai abunda
ake qira Lailatul Qadr,
Daren Lailatul qadr yafi
daraja akan wata dubu,
saboda mala'iku suna
sauqa acikinsa tare da
ruhu (jibril) da izinin
Ubangijinsu ga kowane
al'amari, Amincin ALLAH
ne wannan daren (da
abinda ke cikinsa) har
6ullowar alfijir"
.
(Surah ta 97 aya ta 1
zuwa 5)
.
Haqiqa daukakar daraja
ta isa ga wannan dare
na Lailatul Qadr acikin
wadannan ayoyi cewa
yafi watanni dubu, Haka
kuma sauqar mala'iku
acikinsa har da Mala'ika
Jibrilu (AS) wata falala
ce ta wannan daren.
.
Kuma lalla akwai daga
falalar wannan dare
cewa acikinsa ne ake
rarrabe dukkanin
al'amura abin
hukuntawa.
.
ALLAH (SWT) Yace:
"Lallai ne mu mun
sauqar da alqur'ani a
cikin dare mai albarka,
lallai Mu masu gargadi
ne, acikinsa ne ake
rarraba dukkanin al0ura
abin hukuntawa"
.
(Surah ta 44 aya ta 3
zuwa 6)
.
•••LOKUTAN DA AKE
SAMUN DAREN
LAILATUL QADR•••
.
Annabi (SAW) yace: shi
wannan dare, ana
samunsa a daren 21, da
daren 23, da daren 25,
da daren 27 da daren 29
da daren qarshe na
watan Ramadan.
.
Dan Umar (RA) Yace:
wasu mutane daga
sahabban Annabi (SAW)
an nuna musu daren
Lailatul Qadar acikin
barci, acikin kwana
bakwai na qarshen
watan Ramadan, sai
Manzon ALLAH (SAW)
Yace: "Ina zaton cewa
mafarkinku ta dace da
kwana bakwan qarshe,
saboda haka wanda ya
kasance zai nemi ta to
ya neme ta acikin
kwana bakwai na
qarshen watan
Ramadan"
.
(Muttafaqun Alaihi)
.
Mu'awiyya Dan Abu-
sufyan (RA) Yace:
Manzon ALLAH (SAW)
Yace: acikin (Lokacin
ganin) Lailatul Qadari:
"Daren 27 ne" Abu-
Dawud ya ruwaito shi,
kuma zance mafi
rinjaye Hadith ne
mauqufi. Kuma lallai
(Malamai) sunyi sa6ani
acikin ayyana
takamammen daren a
bisa zantuka arba'in.
.
Aisha (RA) tace:
"Manzon ALLAH (SAW)
Ya kasance yana
maqwabtakar masallaci
a kwana goma na
qarshen Watan
Ramadan, Yana cewa ku
nemi daren Lailatul Qadr
a kwana Goma na
qarshen watan
Ramadan "
.
(Bukhari 4 /225, Muslim
1169)
.
Ibn Hajar Yace: Bayan
jeranta bayani akanta
(Lailatul Qadr) mafi
rinjayen zance shine
tana cikin marra ta
Goman qarshe, kuma ita
tana cancanjawa ne.
.
To wadannan sune
Lokutan da ake samun
Daren Lailatul Qadr.
.
••• ALAMAR DAREN
LAILATUL QADR •••
.
Manzon ALLAH (SAW)
Ya siffanta daren
Lailatul Qadr cikin
abunda Dan Abbas (RA)
Ya ruwaito cewa:
.
Manzon ALLAH (SAW)
Yace: "Daren Lailatul
Qadr dare ne mai sauqi
wanda yake a sake, ba
mai zafi bane kuma ba
mai sanyi ba ne, rana
tana wayuwar gari tana
mai rauni (Marar zafi)
mai launin ja"
.
(Ibn Khuzaimah 3/231).
.
•••NEMAN DACEWA DA
"DAREN LAILATUL
QADR"•••
.
Musulmi yana neman
dacewa da wannan
Dare mai albarka ta
hanyoyi kamar haka:
.
1• Tsayuwa da Da'a ga
ALLAH yana mai imani
da kuma kwadayin ladar
Ubangijinsa.
.
Manzon ALLAH (SAW)
Yace: "Wanda duk yayi
tsayuwar daren Lailatul
Qadr yana mai imani da
ALLAH da kuma neman
ladar Ubangiji to an
gafarta masa abunda
ya gabatar na zunubai"
.
(Bukhari 4/217, Muslim
759)
.
2• Musulmi kan iya
neman dacewa da
wannan dare ta hanyar
yawaita addu'a.
Aisha (RA) tace: "Ya
Manzon ALLAH shin ko
kana ganin idan na gane
wani dare ne Lailatu
Qadr me zance acikinsa?
Sai yace kice: .
ALLAHUMMA INNAKA
AFUWWUN TUHIBBUL
AFWA FA'AFU ANNIY"
.
Ma'ana: "Ya ALLAH Lallai
Kai mai yafewa ne
kuma kana son yafewa
to ina roqonka ka yafe
min"
.
(Tirmizi 3760, Ibn Majah
3850)
.
3• Raya kwana 10 na
qarshen Watan
Ramadan da ibada, da
kuma nisantar
abubuwan sha'awa da
yawaita ayyukan Da'a
zuwa ga ALLAH (SWT).
.
Aisha (RA) tace: Manzon
ALLAH (SAW) Ya
kasance yana yawaita
qoqarin ibada a kwana
10 na qarshen Watan
Ramadan, irin qoqarin da
baya yin irinsa a
kwanakin da ba
wadannan ba"
.
(Muslim 1174)
.
4• Yawaita ambaton
ALLAH irin wanda aka
samo daga Manzon
ALLAH (SAW) da kuma
yawaita karatun
Alqur'ani mai Girma da
Haddarsa, da kuma
qiran mutane zuwa ga
ayyukan alkhayri, dayi
musu hani akan
mummuna.
.
YA ALLAH KA BAMU
DACEWA DA DAREN
LAILATUL QADR KUMA
KA AMSA MANA
IBADUNMU. (Ameen)
.
-Faridah Bintu Salis.
(Bintu-sunnah)

Yaushe ne ya fi dacewa a yi sahur? (Sheikh Abdulwahhab Abdullah)

Alhamdu lillahi
rabbil A’lamin,
Wa sallallahu
wa sallama ala
Nabiyyina
Muhammad wa
ala alihi wa
sahbihi ajma’in.
Amma ba’ad;
Lallai wanda
yake son
Manzon Allah
sallallahu alaihi
wa sallama zai
fifita
shi akan duk
abin da yake da
girma
ko daraja ko
tsada a gunsa.
Domin
son Allah da
manzonsa
sune imani,
kuma imanin
bawa bazai
cika ba sai
da su. Allah
subhanahu wa
ta’ala
yace:
“ kace idan har
iyayenku da
‘ya’yanku da
‘yan uwanku
da
matanku da
danginku da
dukiyar da
kuka
tsuwurwurta
da kasuwancin
da
kuke jin tsoron
tasgaronsa da
gidaje
da kuke yarda
dasu sune suka
fi
soyuwa a
gareku daga
Allah da
Manzonsa da
jihadi saboda
Allah ;to
ku zauna har
Allah ya zo da
al’amarinsa,
allah baya
shiryar da
fasikai” {Tauba
:24}
Wannan ayar
nassi ce karara
a bisa
wajibcin kaunar
Manzon Allah
sallallahu alaihi
wa sallama,da
wajibcin
gabatar da
wannan kaunar
akan duk wani
abin kauna.
Alkali Iyadh
yace: “wannan
ayar ta
isa wajen
zaburarwa da
fadakarwa da
shiryarwa da
zama hujja ta
gaske a
bisa wajibcin
kaunar Manzon
Allah
sallallahu alaihi
wa sallama da
cancantarsa da
wannan
soyayyar,
domin Allah ya
kwankwashi
wadanda
dukiyarsu da
iyalansu da ‘ya
‘yansu
suka fi soyuwa
a garesu fiye
da Allah
da
manzonsa,kuma
yayi musu
narko
cewa su jira
har Allah ya zo
da
al’amarinsa,sannan
ya fasikantar
da
su, ya kuma
sanar da su
cewa sun
bacewa hanya
madaidaiciya,
Allah ba
zai shiryar da
su ba.
Hakanan kuma
wanda ya yi
la’akari
da wannan
ayar zai ga
cewa umarnin
bai tsaya ga
samuwar
soyayya ga
Allah da
Manzonsa
kadai ba,
barima
dai dole ne sai
wannan son ya
zama
sama da son
duk wani abu
wanda ba
su ba.
Wa sallallahu
wa sallama ala
Nabiyyina
Muhammad wa
ala alihi wa
sahbihi ajma’in.