MARABA DA WATAN RAMADAN ••••••••••••••••••••[02]

MARABA DA WATAN
RAMADAN
.
•••••••••••••••••••••[2]
••••••••••••••••••••
.
MA'ANAR AZUMI DA
KUMA LOKACINSA:
.
AZUMI: ibada ce daga
cikin cika-cikan
musulunci guda biyar.
.
AZUMI: shine barin ci da
sha da saduwa da iyali
da kuma Barin dukkan
abubuwan ci, tun daga
6ullowar alfijir har Zuwa
faduwar rana acikin
dukkan kwanakin
watan Ramadan.
.
Wannan bayani yana
nuna iyakancewar yinin
mai azumi tun farkon
yinin har qarshensa,
wato daga 6ullowar
alfijir har zuwa faduwar
rana da fuskantowar
dare da kuma 6oyuwar
kaskon rana acikin
shamaki. Wannan shine
cikakken lokacin fara
azumi da kuma qare sa.
.
ALLAH (SWT) Yace: "An
halatta muku saduwa
da iyalinku acikin
dararen watan
Ramadana, su
(iyalanku) sutura ne
agare ku kuma sutura
ne agare su"
.
Har zuwa fadansa
(SWT) "kuci kuma Ku
sha har sai farin silale
ya bayyanar muku daga
baqin silale na alfijir,
sannan Ku cika azumi
zuwa dare".
.
(Surah ta 2 aya ta 158)
.
Hadith yazo daga Umar
ya tabbatar da
iyakancewar lokacin
azumi Inda Yace:
.
Manzon ALLAH (SAW)
Yace: "idan dare ya
fuskanto daga nan yini
ya bada baya daga can
kuma rana ta fadi to
lokacin buda baki yayi
ga mai Azumi"
.
(Bukhary 4/671, Muslim
1100)
.
•NIYYAR MAI AZUMI:
.
Niyya ita ce qudurta
wani abu a zuciya,
wato Mutum yayi
qudurin ko wani irin aiki
na ibada a zuciyarsa,
domin ko wani aikin
ibada baya inganta sai
da Niyya.
.
Manzon ALLAH (SAW)
Yace: " dukkan ayyuka
basa inganta sai da
niyya, kuma ana
sakawa kowane
Mutum da abunda yayi
niyya"
.
(Bukhary da Muslim
suka ruwaito shi Umar
(RA)
.
YADDA AKE YIN NIYYAR
AZUMIN WATAN
RAMADAN:
.
Bayanin malamai ya
tabbatar da cewa:
wajibi ne kwana da
niyya a axumin farilla na
(Ramadan) wato tun
kafin 6ullowar alfijir idan
an tabbatar da ganin
watan Ramadan daga
adilan mutane ko
shugaba, ko kuma
lokacin da kwanakin
watan sha'aban suka
cika talatin.
.
A wannan lokaci ya
wajaba akan duk
musulmi baligi namiji ko
mace suyi niyyar
azumin watan ramadan
cikin dare kafin 6ullowar
alfijir.
.
Kamar Yadda Annabi
(SAW) Yace: "Wanda
duk bai wayi gari da
(Niyyar) azumi ba kafin
alfijir to bayi da azumi"
.
(Nasa'i 4/196)
.
Da kuma fadarsa
(SAW) cewa: "Wanda
bai kwana da niyyar
azumi ba tun da dare to
babu azuminsa'
.
(Tirmizi 730)
.
Malamai sun ce " Zuciya
ita ce wurin niyya,
Amma yin furuci da ita
bidi'ah ne koda kuwa
mutane na ganin yin
haka abu ne mai kyau.
.
Saboda Manzon ALLAH
(SAW) da sahabbansa
basu ta6a yin furuci da
Niyya ba"
Domin qarin bayani
duba:
.
(siffatu saumin Nabiy
(SAW) shafi na 30)
.
-Faridah Bintu Salis
(Bintus-sunnah)

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s