MARABA DA WATAN RAMADAN ••••••••••••••••••••[03]

MARABA DA WATAN
RAMADAN
.
•••••••••••••••••••••[3]
••••••••••••••••••••
.
GANIN WATA DA
HUKUNCE- HUKUNCENSA.
.
Haqiqa ALLAH (SWT) ya
sanya rana ta zama
ma'auni ga bayinsa don
su san lokutan wasu
ibadodi kamar Sallah. To
haka kuma ya sanya
Wata a matsayin alama
ta sanin lokutan wasu
ibadodi na bauta masa
kamar Azumi da kuma
Hajji.
.
•ALLAH (SWT) Yace:
.
" ﻳَﺴْﺄَﻟُﻮﻧَﻚَ ﻋَﻦِ ﺍﻟْﺄَﻫِﻠَّﺔِ ﻗُﻞْ
ﻫِﻲَ ﻣَﻮَﺍﻗِﻴﺖُ ﻟِﻠﻨَّﺎﺱِ ﻭَﺍﻟْﺤَﺞِّ "
ﺍﻟﺒﻘﺮ ١٨٩
.
Ma'ana: "Suna
tambayarka game da
jinjirin wata kace musu,
an sanya su don
mutane su San lokuta
da kuma aikin Hajji"
.
(Suratul Baqara aya ta
189)
.
• ALLAH (SWT) ya
Sanya watanni guda 12
acikin shekara kamar
Yadda Yace:
.
" ﺇِﻥَّ ﻋِﺪَّﺓَ ﺍﻟﺸُّﻬُﻮﺭِ ﻋِﻨﺪَ ﺍﻟﻠَّﻪِ
ﺍﺛْﻨَﺎ ﻋَﺸَﺮَ ﺷَﻬْﺮًﺍ ﻓِﻲ ﻛِﺘَﺎﺏِ
ﺍﻟﻠَّﻪِ …." ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻟﺘﻮﺑﺔ ٣٦
.
Ma'ana: "Haqiqa
qididdigar watan ni a
wurin ALLAH guda 12
ne acikin littafin
ALLAH….."
.
(Suratul Taubah aya ta
36)
.
• Kuma ALLAH (SWT)
daga cikin watanni 12
ya ke6ance wasu
ibadodi na musamman
da ake aikatawa
acikinsu. Kamar yadda
Yace:
.
" ﺍﻟْﺤَﺞُّ ﺃَﺷْﻬُﺮٌ ﻣَّﻌْﻠُﻮﻣَﺎﺕٌ …."
ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻟﺒﻘﺮﺓ ١٩٧
.
Ma'ana: "shi aikin Hajji
yana da watanni
sanannu…."
.
(Suratul Baqara aya ta
197)
.
• Kuma ALLAH (SWT)
ya fada game da
Ramadan (Azumi)
cewa:
.
" ﺷَﻬْﺮُ ﺭَﻣَﻀَﺎﻥَ ﺍﻟَّﺬِﻱ ﺃُﻧﺰِﻝَ
ﻓِﻴﻪِ ﺍﻟْﻘُﺮْﺁﻥُ ﻫُﺪًﻯ ﻟِّﻠﻨَّﺎﺱِ
ﻭَﺑَﻴِّﻨَﺎﺕٍ ﻣِّﻦَ ﺍﻟْﻬُﺪَﻯٰ ﻭَﺍﻟْﻔُﺮْﻗَﺎﻥِ
ﻓَﻤَﻦ ﺷَﻬِﺪَ ﻣِﻨﻜُﻢُ ﺍﻟﺸَّﻬْﺮَ
ﻓَﻠْﻴَﺼُﻤْﻪُ ….." ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻟﺒﻘﺮﺓ
١٨٥
.
Ma'ana. "Watan
Ramadana shine watan
da aka sauqar da
Alqur'a ni acikinsa domin
shiriya ga mutane da
hujjoji da shiriya da
kuma rarrabewa
tsakanin gaskiya da
qarya saboda haka
Kowa ya shaida anga
wata daga cikin ku to
ya azumce shi…."
.
(Suratul Baqara aya ta
185)
.
BAYANIN GANIN WATA
DAGA MANZON ALLAH
(SAW) !!!
.
Haqiqa Annabi (SAW)
yayi mana bayani mai
gamsarwa acikin
Hadithai daban daban
kamar haka:
.
• Bukhari da Muslim sun
ruwaito daga Abdullahi
dan Umar (R.A) Yace:
Annabi (SAW) Yace:
"Wata kamar haka yake
da kuma haka" wato
yana nuni da yatsun
tafin hannunshi biyu
sau 3 yana nufin kwana
30. Sannan yace da
kuma haka" yana nufin
kwana 29.
.
Yana nufin wani lokaci
Wata kwana 30 ne
wani lokaci kuma
kwana 29. Malaman
Hadith sunyi muwafaqa
akan ingancinsa.
.
• Bukhari da Muslim sun
ruwaito daga Abu
Hurairata (R.A) Yace:
Annabi (SAW) Yace: "
kuyi Azumi idan kunga
wata kuma Ku ajiye
Azumi kuyi sallah idan
kunga wata, idan an
kare muku ganin wata
saboda wasu giragizai
to sai Ku cika qirgar
sha'aban kwana 30"
.
ABUBUWA GUDA 2
DAKE TABBATAR DA
WATAN RAMADAN !!!
.
1• Ganin jinjirin watan
idan sama ta kasance
tangaram ba abin sake
hana a ganshi na
giragizai ko qura da
makamantansu.
.
2• cika qirgan sha'aban
kwana 30 idan ba a
samu ganin watan ba
ranar 29, wannan yana
daga cikin dalilin Hadith
da ya gabata.
.
GAME DA GANIN WATA
A WASU QASASHE !!!
.
Idan ganin wata ya
tabbata ga wani yanki
na wata qasa to ya
wajaba sauran yankuna
su dauki Azumi idan
sanarwa tazo musu ta
hanyar da zata wajabta
musu daukar Azumi, ba'
a lura da banbancin
sa6anin mafitar wata.
.
Wannan shine ra'ayin
Mazhabobi guda 3 wato:
Imam Abu-hanifa,
Imam Maleek da Imam
Ahmad.
.
Amma a wajen Imam
Shafi'ee sun inganta
wannan hukunci ga
makusanta wannan
gari kawai, idan akwai
nisa tsakaninsu da inda
aka ga Wata to kowace
qasa zata yi aiki da
ganin watanta.
.
JAN HANKALI GAME DA
GANIN WATA !!!
.
Ganin Wata ba wani
Girma bane ko daraja
bare ace sai sheikh ko
malam wane zasu fara
ganin shi ko kuma sai
qasa mai tsarki ta
ganshi kafin wata qasa
ta ganshi ba, ba haka
abun yake ba.
.
Ana iya ganin wata a
America ko Isra'eela
amma Saudia basu
Ganshi ba.
.
Kafiri yana iya ganin
wata, musulmi bai
Ganshi ba illa dai ba'a
amsar shedun ganin
wata saiga Musulmai
Adilai kawai.
.
Domin a zamanin
Annabi (SAW) an samu
wani Baqauye yazo
daga garinsu yacewa:
Manzon ALLAH (SAW)
sunga wata da zaran
Manzon ALLAH (SAW)
ya gamsu da shaidarsa
a matsayinsa na
musulmi sai kawai Yace
Bilal (R.A) ya bada
sanarwar daukar Azumi
ko kuma ajiye shi.
.
Saboda haka a kula
musulunci Addini ne mai
sauqi ga wanda ALLAH
ya sauqaqewa.
.
ALLAH Ya taimake mu
(Ameen)
.
-Faridah Bintu Salis
(Bintus-sunnah)

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s