MARABA DA WATAN RAMADAN ••••••••••••••••••••[04]

MARABA DA WATAN
RAMADAN
.
•••••••••••••••••••••[4]
••••••••••••••••••••
.
FALALAR WATAN
RAMADAN MAI
ALBARKA !!!
.
•ALLAH mai girma da
daukaka yace: "Waccan
wata falala ce ta
ALLAH yana bayar da
ita ga wanda yaso,
kuma ALLAH ma'abocin
daukakar falala ne mai
girma"
.
(surah ta 62 aya ta 4)
.
Yana daga cikin abunda
babu sa6ani a tsakanin
malamai game da shi
cewa lallai watan
Ramadan watane mai
alkhayri da albarka
wanda ALLAH ya
ke6ance shi da falala
mai yawa, kamar yadda
wannan bincike zai
bayyana.
.
•ALLAH mai girma da
buwaya ya sauqar da
littafinsa a matsayin
shiriya ga mutane da
waraka ga muminai da
hujjoji bayyanannu daga
shiriya da kuma rabewa
(tsakanin qarya da
gaskia). Yana shiryarwa
zuwa ga hujja mafi
qarfi kuma da yana
bayyana tafarkin
shiriya. An sauqar dashi
ne a daren LAILATUL
QADRI daren daraja
acikin watan Ramadan
mai alkhairai.
.
•ALLAH (SWT) yana
cewa: "Watan Ramadan
ne wanda ALLAH ya
sauqar da Alqur'ani a
cikinsa yana shiriya da
rarrabewar (gaskia da
qarya) to wanda ya
halarci watan daga cikin
ku sai ya azumce sa….
.
(surah ta 2 aya ta 185)
.
Sauqar da alqur'ani a
wannan watan yana
nuni ne akan falalar
watan. Daure shaidanu
da rufe qofifin wuta da
bude qofofin aljanna
wata dalala ce da ta
ke6anci watan
Ramadan.
.
•Manzon ALLAH (SAW)
Yace: "idan Ramadan
tazo ana bude qofofin
aljannah kuma ana rufe
qofofin wuta kuma ana
daure shaidanu"
.
(Tirmizi 682, Ibn majah
1642 daga Abu-
hurairah)
.
kuma duk wannan aiki
ana yin sane a farkon
daren watan Ramadan
.
•Annabi (SAW) yace:
"idan farkon daren
watan Ramadan yazo
ana daure shaidanu da
kangararrun aljanu.
.
Kuma ana bude qofofin
Aljannah ana rufe
qofofin wuta ba a bude
ko wace qofa daga
cikinta, kuma ana bude
qofofin aljannah ba a
rufe ko wace qofa a
cikinta, sannan sai wani
mai qira yayi qira
(cewa): "Ya kai mai
neman alkhairi fuskanci
aukin alkhayri kuma Ya
kai mai neman aikata
sharri ka taqaita (bari)
kar ka aikata! Kar ka
aikata" kuma ko wani
dare ALLAH yana 'yanta
wadansu bayi daga
wuta"
.
(Bukhary 4/97, Muslim
1079)
.
Haka kuma samun
daren LAILATUL QADRI
a watan Ramadan
wata falala ce wadda
wannan watan kadai
keda ita.
.
ALLAH (SWT)
Yace:"Lallai ne mun
sauqar dashi (Alqur'ani)
acikin daren LAILATUL
QADRI (daren daraja).
To me ya sanar da kai
abunda ake cewa
LAILATUL QADRI ?
Mala'iku da ruhi suna
sauqa acikinsa, da izinin
Ubangijinsu saboda ko
wani umurni, aminci ne
shi daren har fitar alfijir"
.
(surah ta 97 aya ta 1
zuwa ta 5)
.
ALLAH YA DATAR
DAMU DA
ALKHAYRINSA (Ameen)
.
-Faridah Bintu Salis
(Bintus-sunnah)

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s