MARABA DA WATAN RAMADAN ••••••••••••••••••••[05]

MARABA DA WATAN
RAMADAN
.
•••••••••••••••••••••[5]
••••••••••••••••••••
.
FA'IDODIN AZUMI TARE
DA FALALARSA.
.
Da yawa daga cikin
ayoyin Alqur'ani da
Hadithan Manzon
ALLAH (SAW) sun
bayyana Fa'idar Azumi
da kuma Falalarsa,
kamar haka:
.
• SAMUN GAFARA DA
LADA MAI GIRMA GA
MASU AZUMI MAZA DA
MATA:
.
ALLAH mai Girma da
daukaka Yace:" lallai
musulmai maza da
musulmai mata, da
muminai maza da
muminai mata, da
masu gaskiya maza da
masu gaskiya mata, da
masu haquri maza da
masu haquri mata, da
masu tsoron ALLAH
maza da masu tsoron
ALLAH mata, da masu
sadaqa maza da masu
sadaqa mata, da masu
azumi maza da masu
azumi mata da masu
tsare farji su maza da
masu tsare farjinsu
mata da masu
ambaton ALLAH maza
da masu ambaton
ALLAH mata,ALLAH
yayi musu tattalin
gafara da sakamako
mai girma"
.
(surah ta 33 aya ta 35)
.
Kunga a wannan ayar
azumi tazo acikinta.
.
• AZUMI GARKUWA NE
DAGA WUTA KUMA
KARIYA CE DAGA
SHA'AWA:
.
Kamar yadda fiyayyen
halitta Annabi (SAW)
Yace: " ya ku taron
samari wanda duk ya
samu hali daga cikinku
to yayi aure, domin
shine mafi runtsewa ga
ido kuma mafi
kiyayewa ga farji,
wanda kuma bai zamu
iko ba to sai yayi Azumi
domin shi Azumi kariya
ne agareshi"
.
(Bukhary 4/109, Muslim
1400 daga Ibn Mas'ud
R.A)
.
Kuma Manzon ALLAH
(SAW) Yace: " Babu
wani Bawa da zai
azumci wani yini saboda
ALLAH, face sai ALLAH
ya juyar da fuskarsa
daga barin wuta da
Nisan shekara saba'in"
.
(Bukhary 6/35, Muslim
Hadith mai lamba 1153)
.
A wani fadin nasa
kuma: "Azumi garkuwa
ne wanda Bawa ke
kariya da ita daga
wuta"
.
(Ahmad 3/241)
.
• HAKA KUMA AZUMI
NA ZAMA DALILIN
SHIGA ALJANNAH GA
MAI YINSA:
.
Tunda mun San cewa
azumi yana nisantar da
mai yinsa daga wuta to
lallai kuma yana
kusantar da mai yinsa
zuwa ga aljannah.
.
Hadithin Abu Umamah
Al-bahiliy ya tabbatar
da haka yayin da Yace"
sai nace Ya Manzon
ALLAH (SAW) ka shiryar
dani ga wani aiki wanda
zai shigar dani aljannah,
sai Manzon ALLAH
(SAW) Yace na
umurceka da Azumi
babu tamka agare sa"
.
.( Bukhary 4/95, Muslim
1156)
.
• ALLAH (SWT) YANA
CIKAWA MASU AZUMI
LADAR SU BA TARE DA
IYAKANCEWA BA:
.
Wannan wata falala ce
da fa'ida mai girma
wadda ta cancanci
masu azumi. Duba ga
wannan hadith din:
.
Abu-hurayrah (RA)
Yace: Manzon ALLAH
(SAW) Yace: "dukkan
kyakykyawan aiki da
dan Adam yayi ana
ninja masa ladar aikin
har zuwa ninki goma ko
zuwa ninki 700, amma
sai ALLAH (SWT) Yace:
shi Azumi nawa ne
kuma Ni me sakawa a
kansa"
Wannan Hadith yana
tabbatar mana da
cewar ALLAH ne kadai
yasan yawan ladar da
mai yin azumi yake
samu.
.
• AZUMI YANA CETON
MAI YINSA A RANAR
ALQIYAMA:
.
"Azumi da Alqur'ani
suna ceton Bawa a
ranar alqiyama, Azumi
zai ce: Ya Ubangijina na
hana bawanka cin abinci
da kuna sha'awarsa
domin haka ka bani
cetonsa, Alqur'ani
shima zai ce: nima na
hana masa barci da
dare yana karanta ni,
domin haka ka bani
cetonsa, sai ALLAH ya
basu ceto sai su ceci
wannan Bawa.
.
(Ahmad 6626, Hakim
1/554)
.
• ALLAH (SWT) YA
KE6ANCE WATA QOFA
DAGA QOFOFIN
ALJANNAH:
.
Haqiqa ALLAH (SWT) ya
ke6ance wata qofa
daga cikin qofofin
aljannah ga masu azumi
kuma ya ambace ta da
suna "RAYYAN"
.
Manzon ALLAH (SAW)
Yace:"lallai acikin
Aljannah akwai wata
qofa ana ambatonta da
Suna Rayyan, a ranar
qiyama masu azumi
suna Shiga ta cikinta
babu mai Shiga ta
cikinta sai su, idan suka
qare Shiga sai a rufe
qofar, kuma duk wanda
ya Shiga ta wannan
qofar za'a shayar dashi
abin sha wanda bazai
sake qishin ruwa ba
har'abada"
.
(Bukhary 4/95)
.
• AZUMI YANA ZAMA
KAFFARA:
.
daga cikin falalar da
Azumi ya ke6antu dashi
ALLAH (SWT) ya Sanya
shi a matsayin kaffara
ne ga wasu laifuffuka.
.
ALLAH YA DATAR
DAMU DA ALKHAYRAN
DAKE CIKIN WANNAN
WATA (Ameen)
.
-Faridah Bintu Salis
(Bintus-sunnah)

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s