MARABA DA WATAN RAMADAN ••••••••••••••••••••[06]

MARABA DA WATAN
RAMADAN
.
•••••••••••••••••••••[6]
••••••••••••••••••••
.
BUDA BAKI DA
HUKUNCE-HUKUNCENSA
.
Haqiqa buda baki yana
daga cikin Sunnar
Annabi (SAW).
.
•BUDA BAKI: shine mai
Azumi ya buda baki
(Yaci wani abu) idan
rana ta fadi, yini ya
bada baya dare kuma
ya gabato, daga
wannan lokacin buda
baki yayi ga mai Azumi.
.
•GAGGAUTA BUDA
BAKI:
.
Gaggauta buda baki
yana kawo wa
al'ummar musulmi
alkhayri, saboda
Hadithin Sahal dan Sa'ad
(RA) ya tabbatar cewa:
.
Manzon ALLAH (SAW)
Yace: "Mutane ba zasu
gushe tare da alkhayri
ba matuqar suna
gaggauta buda
baki" (Bukhari 4/173,
Muslim 1093)
.
Idan al'ummar Musulmi
suna gaggauta buda
baki to haqiqa sun
wanzar da Sunnar
Annabi (SAW), Yazo a
hadithin Sahal dan Sa'ad
(RA) cewa:
.
Manzon ALLAH (SAW)
Yace: "Al'ummata ba
zata gushe a kan
sunnata ba matuqar
bata jiran 6ullowar
taurari, a wajen buda
bakinta ba" (Ibn Hibban
891 ya ruwaito shi da
ingantaccen isnadi)
.
kuma an ruwaito Hadith
daga Abu Hurayrah (RA)
cewa:
.
Manzon ALLAH (SAW)
Yace: "Addinin Musulunci
ba zai gushe ba
rinjayayyen addini
matuqar musulmi suna
gaggauta buda baki
lokacin Azumi. Saboda
yahudu da nasara suna
jinqirta buda baki" (Abu-
dawud 891 ya ruwaito
shi da ingantaccen
isnadi).
.
•ABUNDA YA KAMATA
A BUDA BAKI DASHI:
.
Haqiqa Manzon ALLAH
(SAW) Ya kasance yana
kwadaitar da
al'ummarsa akan su
buda baki dabino kamar
yadda yazo a Hadithin
Ans dan Malik (RA)
Yace:
.
Manzon ALLAH (SAW)
Ya kasance yana buda
baki da danyen dabino
kafin yayi sallah, idan
bai samu ba sai yayi da
busashshe, idan bai
samu ba sai ya kamfaci
ruwa, saboda shi mai
tsarki mai tsarkakewa
ne"
.
(Mutane 5 suka ruwaito
shi, Ibn Khuzaimah, Ibn
Hibban, Hakeem sun
inganta shi)
.
•ADDU'A A WAJEN
BUDA BAKI:
.
Ya 'Yan uwana haqiqa
Addu'armu a wajen
buda baki kar6e66iya
ce, saboda haka muyi
addu'o'i muna masu
sakankacewar an kar6a
mana. Amma mu sani
cewa ALLAH baya
kar6ar addu'ar wanda
zuciyarsa rabkananniya
ce mai wasa daga
ambaton ALLAH.
.
Abu-Hurayrah (RA) ya
ruwaito Hadith cewa:
.
Manzon ALLAH (SAW)
Yace: "Addu'o'i 3 abin
kar6awa ne: Addu'ar
mai Azumi, Addu'ar
wanda aka zalunta,
Addu'ar matafiyi,
wannan sune addu'ar
da ba a mayar wa.
.
A wani Hadith kuma
Abu-Hurayrah (RA)
Yace: Manzon ALLAH
(SAW) Yace: " Addu'o'i 3
ba'a mayar dasu ko
kuma mutum 3 ba a
komar da addu'arsu:
Addu'ar mai Azumi
lokacin buda baki,
Addu'ar shugaba mai
adalci, Addu'ar wanda
aka zalunta"
.
•MAFIFICIYAR ADDU'A
A WAJEN BUDA BAKI:
.
Haqiqa an samo daga
Hadith cewa Manzon
ALLAH (SAW) Ya
kasance duk lokacin da
zai buda baki yana
cewa:
.
"ZHABAZ ZAMA'U
WABTALATIL URUQU
WA THABATAL AJRU
INSHAA ALLAH"
.
Ma'ana "Qishirwa ta
tafi, jijiyoyi sun
sanyaya, ladar (ALLAH)
ta tabbata in ALLAH
yaso"
.
(Abu-dawud 2/306,
Baihaqi 4/239, Hakeem
1/422)
.
ALLAH YA AMSA MANA
IBADUNMU (Ameen).
.
-Faridah Bintu Salis.
(Bintus-sunnah)

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s