MARABA DA WATAN RAMADAN ••••••••••••••••••••[07]

MARABA DA WATAN
RAMADAN
.
•••••••••••••••••••••[7]
••••••••••••••••••••
.
SAHUR DA HUKUNCE-
HUKUNCENSA.
.
•SAHUR: Shine abincin da
Musulmi ke ci a qarshen
rabin kashin daren
Azumi, kafin 6ullowar
alfijir.
.
Annabi (SAW) yayi
umurni da sahur domin
bambantawa tsakanin
Azuminmu da Azumin
ma'abota littafi (Yahudu
da Nasara)
.
Manzon ALLAH (SAW)
Yace: "Banbancin
Azuminmu dana
ma'abota littafi (Yahudu
da Nasara) shine cin
abincin Sahur" (Dabarani
6127)
.
•FALALAR YIN SAHUR:
.
Akwai albarka cikin yin
sahur, wannan kuma
yazo a hadith masu
yawa, daga cikinsu
akwai Hadithin Salman
(RA) Yace:
.
Manzon ALLAH (SAW)
Yace: "Ana sanya
albarka acikin abubuwa
guda 3:- daga cikinsu
akwai sahur" (Dabarani
6127)
.
Da kuma Hadithin Abu-
Hurayrah (RA) Yace:
Manzon ALLAH (SAW)
Yace: "Lallai ALLAH
(SWT) Ya sanya albarka
acikin sahur"
.
wani Sahabin Annabi
(SAW) Yace: Na shiga
wurin Manzon ALLAH
(SAW) a lokacin yana
sahur, sai yace: "Lallai
(shi sahur) albarka ce
wanda ALLAH (SWT) Ya
baku ita, kada kuyi
wasa da ita" (Nasa'i
4/145, Ahmad 5/970).
.
Malamai sun tabbatar
da cewa an so a jinqirta
yin sahur sai kusan
6ullowar alfijir, saboda
Manzon ALLAH (SAW)
da Zaid Bin Thabit (RA)
sunyi sahur lokacin da
suka qare, sai Annabi
(SAW) ya tashi zuwa
sallar asuba yayi sallah.
.
Anas dan Malik ya
ruwaito daga Zaid Bin
Thabit (RA) yace: "Mun
yi sahur da Manzon
ALLAH (sAW) sannan
ya tashi zuwa sallah,
Anas Yacewa Zaid Ibn
Thabit, daga qiran
sallah zuwa sahur wani
lokaci ne ke tsakaninsu?
Sai Yace: Gwargodon
(Tsawon) karanta aya
50 (Hamsin)" (Bukhari
4/118, Muslim 1097).
.
•HIKIMAR YIN SAHUR:
.
1•Bambanta tsakanin
Azumin Musulmi dana
Yahudu da Nasara.
.
2•Yin kyakykyawan shiri
domin fuskantar Azumi
da rana.
.
3•Sahur sunnah ce mai
qarfi kamar yadda ya
tabbata a Hadithai
ingantattu.
.
•HUKUNCIN YIN SAHUR:
.
Acikin hukuncin yin
sahur akwai magana
kashi biyu:
.
1•Sashen Malamai sun
tafi akan cewa Sahur
Mustahabbi ne (Abin so
a shari'a) saboda
Hadithai sun nuna haka:
.
Manzon ALLAH (SAW)
Yace: "Wanda duk zai yi
azumi to idan yaso yayi
sahur, da wani
abu" (Bukhari da Muslim
suka ruwaito shi)
.
2•Wasu Malamai sun ce
Sahur Sunnah ce mai
qarfi, saboda Annabi
(SAW) ya fada a wani
hadith cewa: "ALLAH ne
da kansa ya baku shi
(Sahur) kada ku
barshi" (Nasa'i 4/145,
Ahmad 5/270)
.
Magana mafi rinjaye ita
ce: Sahur Sunnar Annabi
(SAW) ce mai Qarfi.
.
ALLAH YA BAMU IKON
GABATAR DA IBADUN
MU (Ameen).
.
-Faridah Bintu Salis
(Bintus-sunnah)

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s