MARABA DA WATAN RAMADAN ••••••••••••••••••••[08]

MARABA DA WATAN
RAMADAN
.
•••••••••••••••••••••[8]
••••••••••••••••••••
.
ABUBUWANDA AKA
HALATTAWA MAI
AZUMI !!!
.
Haqiqa saboda tausayin
ALLAH (SWT) ga
bayinsa, yana nufinsu
da sauqi, baya nufin ya
tsananta musu, saboda
haka ne ya halatta wa
mai Azumi wasu
al'amura, kuma ya
dauke masa laifi idan ya
aikata su, ga wasu
daga ciki:-
.
1• YIN ASWAKI GA MAI
AZUMI: Aswaki yana
cikin sunnar Annabawa,
wanda Annabi (SAW)
yayi umurni da ita
kamar yadda yace:
.
"Badon kar na
tsanantawa al'ummata
ba dana umurce su da
yin Aswaki acikin
alwala" (Bukhari 2/311,
Muslim 202)
.
Abunda wannan hadith
ke nunwa shine Manzon
ALLAH (SAW) bai
ke6ance mai azumi ba
daga waninsa ba domin
haka mai azumi da
maras azumi duk zasu
iya yin aswaki a
kowace alwala.
.
2• WAYEWAR GARIN
MAI AZUMI DA
JANABA: Ya kasance
Annabi (SAW) Alfijir na
riskarsa alhali yana da
janaba daga iyalinsa, sai
yayi wanka bayan
6ullowar alfijir ya cigaba
da azuminsa.
.
Hadisin Aisha (RA) ya
tabbatar da haka da
kuma Hadisin Ummu
Salma (RA) sunce: "Lallai
Manzon ALLAH (SAW)
Alfijir yana riskarsa
alhali yana mai janaba
daga iyalinsa, sannan
yayi wanka, ya cigaba
da azumi" (Bukhari
4/123, Muslim 1109)
.
3• KURKURAN BAKI DA
SHAQA RUWA: Manzon
ALLAH (SAW) Ya
kasance yana kurkuran
bakinsa, kuma yakan
shaqa ruwa yana mai
azumi, sai dai yayi hani
ga mai azumi ya kai
matuqa wajen wannan,
saboda ya umurci wani
mutum cewa:
.
"Ka shaqa ruwa sosai a
wajen alwala sai dai,
idan azumi kak
yi" (Tirmizi 3/146, Abu-
dawud 2/308, Ahmad
4/32)
.
wannan yana tabbatar
mana da cewa kada
mai azumi ya kai
matuqa.
.
4• ZUBA RUWA MAI
SANYI A JIKI DOMIN
SANYAYA QISHIRWA:
Imam Bukhari (ALLAH
Ya jiqansa) Yace acikin
littafinsa:
.
Babi mai magana akan
wankan mai Azumi,
Yace: "Ibn Umar (RA) ya
jiqa tufafinsa da ruwa,
sannan ya sanyasu a
jikinsa yana mai
azumi" (Fat-hul Bari
4/153)
.
Haka kuma sha'abiy ya
shiga gurin wanka yana
mai azumi, kuma
Hassan (RA) yace: Babu
laifi ga kurkurar baki da
yin wanka ga mai
Azumi.
.
Kuma Manzon ALLAH
(SAW) Yana zubawa
kansa ruwa yana mai
azumi saboda Qishirwa
da tsananin zafi. (Abu-
dawud 2365, Ahmad
5/376)
.
5• YIN QAHO: daga
farko yin qaho yana
cikin abubuwan da ke
6ata azumi, sai daga
baya aka shafe wannan
hukunci, saboda ya
tabbata daga Annabi
(SAW) cewa yayi qaho
yana azumi.
.
Abdullahi dan Abbas
(RA) Ya ruwaito cewa
Lallai Manzon ALLAH
(SAW) Yayi qaho yana
mai azumi. (Bukhari
4/155)
.
6• DANDANON ABINCI
GA MAI GIRKI: wannan
babu laifi a kansa ga
mai azumi sai dai da
sharadin kada dandanon
ya zarce cikin maqoshi.
Saboda abin da aka
samo daga Abdullahi
dan Abbas (RA) yace:
.
"Babu laifi ga mai azumi
ya dandani wani abincin
da ake dafawa kamar
kunu ko wani abu,
matuqar dandanonsa
ba zai zarce zuwa
maqoshinsa
ba" (Bukhari 4/154)
.
ALLAH YA AMSA MANA
IBADUNMU (Ameen).
.
-Faridah Bintu Salis
(Bintus-sunnah).

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s