MARABA DA WATAN RAMADA N •••••••••••• •••••••• [10]

MARABA DA WATAN RAMADAN . ••••••••••••••••••••• [10]••••••••••••••••••• . ABUBUWAN DA SUKA WAJABA MAI AZUMI YA NISANTA. . Haqiqa dole ne mu sani mai azumi na gaskia shine wanda dukkan ga66ansa suke azumi tare dashi, wajen barin sa6on ALLAH, kuma ya hana cikinsa daga dangogin abinsha da abinci, ya kare farjinsa daga jima'i kuma idan yayi magana bazai yi wadda zata 6ata masa azuminsa ba, sai maganarsa ta zamo mai kyau, ayyukansa su zamo kyawawa. Wannan shine azumi na haqiqa na shari'ah. . Haqiqa Manzon ALLAH (SAW) Ya kwadaitar da mai azumi ga siffantuwa da halaye nagari da kyawawan dabi'u, ya nisanci munanan halaye, da alfasha da surutan banza, duk da kasancewar miyagun halaye an umurci musulmi ya nisance su a kowane lokaci na rayuwarsa, sai dai hani a kansu da nisantarsu acikin wannan wata mai Alfarma lokacin ibadar Azumi yafi tsanani domin haka ne yake wajaba ga musulmi mai azumi ya nisanci, al'amura guda uku ya barsu gaba daya, wadannan abubuwa basa haduwa da azumi a lokaci daya, sune kamar haka:- . 1• FADAR QARYA: wannan yana lalata azumi, kuma yana yanke ladar mai azumi, qarshe ma, ya maida Azumi, tamkar ba ayi ba. Saboda Hadisin Abu- Huraira (RA) Yace: . Manzon ALLAH (SAW) Yace: "Duk wanda bai daina qiran qarya ba a lokacin azumi to ALLAH (SWT) ba yi da buqatar azuminsa, ko yaci abincinsa ko yasha abun shansa duk daya ne a wurin ALLAH (SWT). . (Bukhari 4/99) . 2• MAGANAR BANZA: wannan ma ya wajaba ga dukkan musulmi, ya bar wannan domin ya zama cikin muminai wadanda ALLAH (SWT) Ya yabe su acikin littafinsa. . "Su Muminai idan suka shude inda ake wadannan maganganun banza yasassu, to suna shudewa ne acikin mutuncim basa tsayawa bare har su saurara" . (Surah ta 25 aya ta 82). . Kuma Manzon ALLAH (SAW) Yace: "Ba wai manufar Azumi kamewa daga barin cin abinci ko shan abunsha bane kawai, a'a Azumi yana nufin kamewa daga wadancan da kuma kamewa daga maganar banza da jima'i da sauran duk abinda zai 6ata shi. . Haka nan yazo cikin Hadith cewa: Idan wani ya zageka to sai kace dashi, Ni mai Azumi ne, Ni mai Azumi ne. . (Ibn khuzaimah 1996, Hakeem 1/430) . 3• YIN JIMA'I ko yin abubuwa da zasu iya kaiwa ga yin jima'i kamar kallon mace da sha'awa ko wasa da ita ko yin magana da ita mai kashe jiki (ta jin dadi) da sauransu, duk wannan lallai ne mai azumi ya nisancesu saboda Hadisin Abu- Hurairah (RA) da ya gabata. . ALLAH YA GAFARTA MANA YA AMSA MANA IBADUNMU (Ameen) . -Faridah Salis Umar. (Bintus-sunnah)

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s