MARABA DA WATAN RAMADA N •••••••••••• •••••••• [11]

MARABA DA WATAN
RAMADAN
.
•••••••••••••••••••••
[11]•••••••••••••••••••
.
SALLAR TARAWIHI
(Asham)
.
Haqiqa wannan sallar
sunnah ce daga cikin
sunnonin Annabi (SAW),
kuma an shar'anta
sallar Tarawihi acikin
jama'a saboda Hadithin
Aisha (RA) da tace:
.
"Lallai Manzon ALLAH
(SAW) Ya fito wata
rana a tsakiyar dare,
yayi sallah a masallaci,
sai wasu mazaje suka
yi koyi da sallarsa,
washe gari magana ta
yadu, a wani daren sai
jama'a suka taru sosai,
sai Manzon ALLAH
(SAW) Yayi sallah, suka
yi sallah tare dashi,
washe gari kuma labari
ya qara yaduwa akan
haka, a dare na uku
kuma aka cika
masallaci, sai Manzon
ALLAH (SAW) yayi
sallarsa suka yi sallah
bayansa, a dare na hudu
masallaci ya kasa
daukar jama'a, Manzon
ALLAH (SAW) bai fito ba
sai a lokacin sallar
asuba, bayan ya qare
sallar asuba tare da su
sai ya fuskance su Yace:
"Ban rena qoqarinku ko
matsayinku ba, amma
ina jin tsoron a farlanta
ta agareku ku kasa
aiwatar da ita. Al'amarin
sallar Tarawihi bai
gushe ba akan haka har
Manzon ALLAH (SAW)
Ya rasu"
.
(Bukhari 3/220, Muslim
761)
.
Manzon ALLAH (SAW)
bayan tabbatar da
shari'ah kuma tsoron da
Annabi yake yiwa
al'ummarsa kada a
wajabta musu sallar
tarawihi ya gushe,
domin haka damar
cigaba da tarawihi acikin
jam'i ta tabbata.
.
Sayyidina Umar dan
Khattab (RA) ya rayar
da wannan sunnah
kamar yadda
Abdurrahman dan
Abdullah Al-kari yace:
"Na fito tare da Umar
Dan Khattab (RA) zuwa
masallaci a wani dare
cikin Ramadan, sai g
mutane warwatse
kowa yana sallah shi
kadai, sai ga wasu
jama'a suna sallah
bayan wani mutum, sai
Umar (RA) yace: "Ina
ganin cewa na hada
mutanen nan ga
makaranci daya ya
jagorance su sallah yafi,
sannan yayi niyya sai ya
hada su da Ubayyu dan
Ka'ab domin ya
jaqorance su a sallar
Tarawihi"
.
Abdurrahman Yace:
"sannan na fito tare da
umar a wani daren, sai
ga mutane suna sallah
da sallar makarancinsu,
sai Umar (RA) yace: "
Madallah da wannan
aikin mai kyau wanda
na qirqiro"
.
Sai dai yin sallar
Tarawihi bayan an
kwanta (tsakiyar dare)
to yafi lada daga yinta a
farkon dare. Sai mutane
suka kasance suna
tsayuwar sallar
Tarawihi a farkon
dare" .
(Bukhari 4/218,
Abdurrazak 7723)
.
••ADADIN RAKA'O'IN
SALLAR TARAWIHI••
.
•Malamai sun yi sa6ani a
adadin raka'o'in wannan
sallah, amma zance
mafi dacewa da shiriyar
Manzon ALLAH (SAW)
shine: Lallai sallar
Tarawihi Raka'a
Takwas ce ba tare da
shafa'i ko wutiri ba,
Abunda ke tabbatar da
haka shine Hadithin
Nana Aisha (RA) tace:
"Manzon ALLAH (SAW)
bai kasance yana qari a
kan raka'a goma sha
daya ba, a sallar sa ta
dare cikin Ramadan ko
waninsa"
.
(Bukhari 3/16, Muslim
736)
.
•Ra'ayin Jabir Dan
Abdullah (RA) yayi daidai
da bayanin Aisha (RA)
yayin da yace: "Lallai
Manzon ALLAH (SAW)
yayi sallah raka'a
takwas lokacin da ya
rayar da dare tare da
mutane sannan sai yayi
witiri"
.
(Ibn Hibban 920,
Dabarani 108)
.
•Kuma lokacin da Umar
Dan Khattab (RA) ya
rayar da wannan
sunnah TARAWIHI ya
hada mutane da
limaminsu akan raka'o'i
goma sha daya (11) ne
daidai da abunda ya
tabbata a sunnah
ingantacce.
.
•Imam maleek ya
ruwaito da isnadi mai
kyau yace: Ankar6o
daga Muhammad Dan
Yusuf daga Sa'ib Dan
Yazid, lallai yace: " Umar
dan Khattab ya umurci
Ubayyu Dan Ka'ab da
Tamimu Addaariy, suyi
qiyamullaili (sallar dare)
tare da jama'a raka'a
goma sha daya (11).
.
[Muwatta maleek
1/115]
.
Akwai ruwayoyi da
yawa ma banbanta da
suka zo akan bayanin
adadin sallar tarawihi,
amma dukkan wata
ruwaya data zo akan
sa6anin ruwayar Aisha
da Jabir (RA) ruwayoyi
ne masu rauni qwarai
wadanda suka sa6awa
ruwayoyi ingantattu.
.
A Lura cewa riqo da
abunda ya inganta daga
Manzon ALLAH (SAW)
shine mafifici abun koyi
ga al'ummah.
.
ALLAH shine mafi sani.
.
ALLAH YA AMSA MANA
IBADUNMU (Ameen)
.
-Faridah Bintu Salis.
(Bintus-sunnah)

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s