MARABA DA WATAN RAMADA N •••••••••••• •••••••• [12]

MARABA DA WATAN
RAMADAN
.
•••••••••••••••••••••
[12]•••••••••••••••••••
.
FALALAR CIYAR DA MAI
AZUMI !!!
.
Haqiqa ayoyin alqur'ani
mai girma sun zo da
kwadaitar da Musulmi
akan ciyarwa saboda
ALLAH a lokacin Azumi
da lokacin da bana
Azumi ba, da
taimakawa matalauta
da mabuqata domin
yaqar talauci a tsakanin
al'ummar musulmai,
kuma yin haka na qara
tabbatar da 'yan
uwantakar musulunci a
tsakanin musulmai.
Daga cikin wadannan
ayoyi akwai fadar
ALLAH (SWT) cewa:
.
"wadanda suke ciyar da
dukiyoyinsu dare da
rana , 6oye da bayyane,
suna da sakamakon
lada a wurin Ubangijinsu
kuma basu tare da
kowane irin tsoro ko
baqin ciki (a ranar
alqiyama) (Surah ta 2
aya ta 274)
.
"(Ku ciyar) daga Abunda
muka fitar muku na
(tsirrai) daga qasa, kada
ku nufi maras kyau
acikinsa kuna ciyar
dashi, alhali ku baku
kar6arsa, sai in (kun
daure) kun runtse ido,
ku sani ALLAH (SWT)
mawadaci ne ga abinda
duk zaku ciyar kuma
wanda ya cancanci yabo
ne acikin ko wani hali"
.
(Surah ta 2 aya ta 267)
.
"Ba zaku samu
cikakkiyar lada, har sai
kun ciyar da abunda
kuke so, abunda duk
kuka ciyar na alkhayri,
to ALLAH Masani ne
game dashi"
.
(Surah ta 3 aya ta 92)
.
"Misalin masu ciyar da
dukiyoyinsu saboda
ALLAH, kamar qwayar
hatsi ce wadda ta fitar
da zangarniya bakwai,
acikin kowace
zangarniya akwai
qwaya dari, kuma
ALLAH yana lullunkawa
ga wanda yaso, ALLAH
Mayalwaci ne, kuma mai
sani akan duk abunda
kuka ciyar"
.
(Surah ta 2 aya ta 261)
.
Wadannan ayoyi duk
suna nuni akan falalar
ciyarwa saboda ALLAH
acikin dukkan yanayi da
lokuta. Ciyarwa saboda
ALLAH bata ke6anta ga
wani lokaci ba, sai dai
ciyarwa a wannan
mafificiyar watan yafi
falala.
.
Kamar yadda ayoyi suka
gabata suna
kwadaitarwa akan
ciyarwa a lokacin azumi
da lokacin da bana
azumi ba. Haka ma
Hadithan Manzon ALLAH
(SAW) sunzo da yawa
suna kwadaitarwa akan
haka, daga cikinsu
akwai wadanda suka zo
akan siffar ciyarwa
gaba daya, akwai kuma
wadanda suka ke6anta
ga watan Ramadan
kawai, wanda shine
muke magana a halin
yanzu.
.
Manzon ALLAH (SAW)
Yace:" Duk wanda ya
ciyar da mai azumi ga
budin baki, yana da
kwatankwacin ladarsa,
ba tare da an tauye
wani abu ba daga ladar
mai Azumin ba"
.
(Ahmad 4/114, Tirmizi,
Ibn Majah 1746)
.
•WASU DAGA CIKIN
ADDU'O'IN WANDA AKA
CIYAR GA WANDA YA
CIYAR DASHI !!!
.
Yana da kyau ga wanda
aka ciyar yayi Addu'a ga
wanda ya ciyar dashi
bayan qare cin abincin,
kamar yadda yazo daga
Manzon ALLAH (SAW)
Addu'o'in suna da yawa
amma ga kadan daga
ciki:
.
"ﺃﻓﻄﺮ ﻋﻨﺪﻛﻢ ﺍﻟﺼﺎﺋﻤﻮﻥ
ﻭﺃﻛﻞ ﻃﻌﻤﻜﻢ ﺍﻷﺑﺮﺍﺭ ﻭ
ﺻﻠﺖ ﻋﻠﻴﻜﻢ ﺍﻟﻤﻼﺋﻜﺔ "
.
Ma'ana: "ALLAH Yasa
masu azumi sunyi buda
baki a wajenku, kuma
ALLAH Yasa
nagartattun bayi sunci
abincinku, kuma ALLAH
yasa Mala'iku sunyi
muku addu'a"
.
(Abu-dawud 3/367 da
Ibn Majah 1/556, da
Nasa'i a cikin Amalul
Yaum wal Laila Hadith
na 296-298. Albani ya
inganta shi acikin Sahih
Abu-dawud 2/730.
.
"ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺍﻃﻌﻢ ﻣﻦ ﺃﻃﻌﻤﻨﻲ
ﻭﺳﻖ ﻣﻦ ﺳﻘﺎﻧﻲ"
.
Ma'ana: "Ya ALLAH! ka
ciyar da wanda ya ciyar
dani, ka shayar da
wanda ya shayar dani"
.
(Muslim 3/1626)
.
" ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺑﺎﺭﻙ ﻟﻬﻢ ﻓﻴﻤﺎ
ﺭﺯﻗﺘﻬﻢ ﻭﻏﻔﺮ ﻟﻬﻢ
ﻭﺭﺣﻤﻬﻢ "
.
Ma'ana: "Ya ALLAH! Ka
albarkace su acikin
abunda ka azurta su
dashi, kuma ka gafarta
musu, kaji qansu"
.
(Muslim 3/1615).
.
Annabi (Sallallahu alaihi
wasallam) Yace: "Aiki
wanda yafi falala shine
ka shigar da murna
acikin (zuciyar) dan
uwanka mumini ko ka
biya masa bashi ko
kaciyar dashi "
.
(Silsilatus sahiha 1494)
.
• A LURA CEWA:
.
Annabi (sallallahu alaihi
wasallam) Yace: "kada
ku ciyar da talakawa
daga abunda Ku Baku
cinsa"
.
(Sisilatus sahiha 2426)
.
Annabi (Sallallahu alaihi
wasallam) Yace: "lallai
Bawa ya ta6e kuma
yayi hasara idan ALLAH
(SWT) bai saka masa
tausayin yan Adam
acikin zuciyarsa ba"
.
(Silsilatus sahiha 456)
.
YA ALLAH DUK WANDA
YA TAIMAKI WANI YA
ALLAH KA TAIMAKE SHI
KA SANYA LADARSA
TA ZAMA SANADIN
SHIGARSA ALJANNAH.
.
ALLAH YA AMSA MANA
IBADUNMU (Ameen)
.
-Faridah Bintu Salis.
(Bintus-sunnah)
June 11 at 11:38am · Public

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s