MARABA DA WATAN RAMADA N •••••••••••• •••••••• [13]

MARABA DA WATAN
RAMADAN
.
•••••••••••••••••••••
[13]•••••••••••••••••••
.
AZUMIN MATAFIYI !!!
.
MATAFIYI: shine wanda
zai tashi daga wani gari
zuwa wani gari, amma
a zamanin Annabi
(SAW) Matafiya suna
kama hanyar tafiya ne
da qafa ko akan wata
dabba, amma a wannan
Zamanin Matafiya suna
tafiya ne a Mota ko a
Jirgi wata motar ma
hada AC.
.
ALLAH (SWT) Yace: "duk
wanda ya kasance daga
cikinku a halin rashin
lafiya ko halin tafiya to
sai ya qirga kwanakin
da yasha Azumi domin
ya rama daga baya,
saboda ALLAH yana son
sauqi gareku baya son
ku da wahala ko
tsanani"
.
(Surah ta 2 aya ta 185)
.
•ZABI GA MATAFIYI:
.
Haqiqa Hadithai
ingantattu sunzo da
dama akan za6i ga
matafiyi, ko yayi azumi
ko yasha bayan
Ramadan ya biya.
.
•Hamza Dan Amr Al-
Aslamiyya (RA) ya
kasance mai yawan
azumi ne, sai ya
tambayi Manzon ALLAH
(SAW) Cewa: "Shin ko
ina iya yin azumi acikin
halin tafiya? Sai Manzon
ALLAH (SAW) Yace
masa: "Kayi Azumi idan
kaga dama; kuma ka
ajiye idan kaga dama"
.
(Bukhari 4/156, Muslim
1121)
.
•Anas Dan Maalik ya
ruwaito cewa: "Nayi
tafiya tare da Manzon
ALLAH (SAW) acikin
watan Ramadan, daga
cikinmu akwai masu
Azumi Akwai wadanda
basa azumi, kuma
Manzon ALLAH (SAW)
bai aibanta mai azumi
akan wanda baya azumi
ba, ko wanda baya
azumi akan wanda yake
yi ba"
.
(Bukhari 4/163-164,
Muslim 118)
.
Wadannan Hadithai duk
suna nuni ne akan za6i
ba fifiko ba, sai dai mafi
yawan Hadithai sun
nuna fifita ajiye azumi
alokacin tafiya, saboda
cewar da Manzon
ALLAH (SAW) Yayi:
"Lallai ALLAH (SWT)
yana son ayi aiki da
rangwamenSa kamar
yadda yake qyamar a
aikata
sa6onSa" (Ahmad
2/108, Ibn Hibban 2742
An kar6o daga Dan
Umar R.A)
.
Malaman Hadith sun
ruwaito cewa: Manzon
ALLAH (SAW) Yace: "Ba
ya daga cikin aiki mai
nagarta yin azumi a
lokacin tafiya"
.
(Bukhari 4/161, Muslim
1115 An kar6o daga
Jabir R.A)
.
•Abunda Malamai suka
rairaye daga Hadithan
da suka gabata shine,
cewa idan Azumi zai
wahalar lokacin tafiya
to yinsa baya cikin
nagarta, a wannan
lokacin barinsa shi yafi a
wurin ALLAH da
ManzonSa kamar yadda
yazo a Hadithin da ya
gabata.
.
Idan kuma Mutum Yana
iya yin Azumi ba tare da
wata wahala ba, kamar
yadda Hadithin Hamza
Dan Amr da Hadithin
Anas Dan Maleek suka
tabbatar to babu laifi
yayi azumi. ALLAH shine
mafi Sani.
.
ALLAH YA AMSA MANA
IBADUNMU (Ameen)
.
-Faridah Salis Umar.
(Bintu-sunnah)

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s