MARABA DA WATAN RAMADA N •••••••••••• •••••••• [14]

MARABA DA WATAN
RAMADAN
.
•••••••••••••••••••••
[14]•••••••••••••••••••
.
AZUMIN MARAR
LAFIYA, MATA MASU
HAILA DA MASU JININ
BIQI (NIFAS), TSOFFI,
MAI CIKI DA MAI
SHAYARWA A WATAN
RAMADAN !!!
.
••MARAR LAFIYA••
.
Marar lafiya shine
wanda ya kasance cikin
wani yanayi na rashin
lafiya wanda ya kai
bazai iya azumtar
azumi ba.
.
Haqiqa ALLAH (SWT) Ya
halatta wa marar lafiya
ya ajiye azumi domin
tausayawa da sauqaqa
ga lamarinsa, sai dai
rashin lafiyar dake sa
ajiye azumi shine
wanda yake cutar da
maras lafiya a jikinsa,
ko kuwa yin azumin
agare shi zai qara masa
wata rashin lafiya ta
daban ko jinqirin
warkewa.
.
•HUKUNCINSA: ALLAH
(SWT) Yace: "Duk
wanda ya kasance
maras lafiya daga
cikinku,ko a halin tafiya
to sai ya rama
kwanakin da yasha
azumin"
.
(Surah ta 2 aya ta 185)
.
Zai ajiye azumin ya
rinqa irga abunda yasha,
idan ALLAH Ya bashi
lafiya zai rama bayan
Ramadan, idan kuma
rashin lafiya ne wanda
bazai iya yin azumi ba
koda bayan Ramadan ne
to zai ciyar da miskini a
kowace rana. ALLAH
shine mafi sani.
.
••MACE MAI HAILA DA
JININ BIQI (NIFAS)••
.
Ma'abota ilimi akan
addini sun hadu akan
cewa mai Haila da Mai
Jinin Biqi (Nifas) baya
halatta agaresu su
dauki azumi, sai dai su
cigaba da cin abincinsu,
kuma zasu rama
azumin da suka sha
bayan Ramadan, sannan
idan jinin ya dauke zasu
yi wankan tsarki su
cigaba da sallah da
Azumi.
.
Domin qarin bayani a
koma ga littafan fiqhu
akan bayanin hukunce-
hukuncen Jinin Haila da
Jinin Biqi (Nifas).
.
•••TSOFFI•••
.
Tsoffi sune wadanda
shekarunsu yaja ma'ana
suka manyanta wanda
har yakai baza su iya
azumtar azumi ba.
.
Abdullahi Dan Abbas
(RA) Yana cewa: Tsoho
da Tsohuwa wadanda
basa iya yin azumi to
sai suci abincinsu a
lokacin azumi, amma su
rinqa ciyar da abincin
miskini kullum"
.
(Bukhari 4505, Fat-hul
Bari 8/180).
.
Anas Dan Maleek (RA)
yace: Wata shekara ya
kasa yin Azumi (domin
tsufa), domin haka sai
ya tanadi daro daya na
abinci, ya ciyar da
miskinai 30"
.
(Darul-quduni 2/207 ya
ruwaito shi da isnadi
ingantacce)
.
••MACE MAI CIKI DA
MACE MAI SHAYARWA••
.
Yana daga rahamar
ALLAH (SWT) babba
akan bayinsa masu
qarfi da raunana,
rangwamen da yayi na
cewa su ajiye azumi
lokacin Ramadan idan
akwai wani uzuri a tare
da bayinsa.
.
Daga cikinsu akwai
mace mai ciki da mai
shayarwa, kamar yadda
ma'abota ilimi suka
ambata.
.
Alka'abi ya ruwaito
Hadith cewa: "Dawakin
Manzon ALLAH (SAW)
sun kai farmaki (hari)
akan mu, sai nazo wurin
Manzon ALLAH (SAW)
na same shi yana cin
abincin rana, sai yace
mani matso kaci abinci,
sai nace masa azumi
nake yi, Yace to matso
na baka labari akan
Azumi, Lallai ALLAH
(SWT) Ya daukewa
matafiya rabin sallah,
ya daukewa mace mai
ciki da mai shayarwa
azumi"
.
(Tirmizi 715, Nasa'i
4/180)
.
•HUKUNCINSU: mace mai
ciki da mai shayarwa ya
halatta ta ajiye azumi
sai ta ciyar, ko kuma ta
rama azumin data sha
bayan gushewar
larurarta. ALLAH shine
mafi sani.
.
ALLAH YA AMSA MANA
IBADUNMU (AMEEN).
.
-Faridah Bintu Salis.
(Bintus-sunnah)

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s