MARABA DA WATAN RAMADA N •••••••••••• •••••••• [15]

MARABA DA WATAN
RAMADAN
.
•••••••••••••••••••••
[15]•••••••••••••••••••
.
•••FIDIYA/FANSA
(CIYARWA) •••
.
•FIDIYA: Shine ciyar da
abincin mabuqaci
matalauci a kowani
wuni na Ramadan
saboda rashin samun
damar yin azumin ko
kasa yinsa saboda
girman shekaru da
sauran uzurorin shari'ah.
.
Asalin wannan mas'ala
shine fadar ALLAH
(SWT) da Yace: "Akan
wadanda basa iya yin
azumi, azumi yana basu
wahala, to sai suyi
Fidiya (ciyarwa) wato
fansar kai, ciyar da
abincin miskini daya a
kullum"
.
(Surah ta 2 aya ta 184)
.
Ma'abota ilimi sun samu
sa6ani a game da
wannan ayar, wasu
suna ganin shafaffiya
ce, wasu kuma suna
ganin ba shafaffiya
bace
.
Dan Abbas (RA) Yace:
"wannan ayah ba a
shafeta ba, ta sauqa ne
akan tsofaffi masu
shakaru da yawa
wadanda basa iya yin
azumi, sai su ciyar da
abincin miskini guda
daya a kullum"
.
(Bukhari 8/135)
.
Wadanda suka tafi akan
cewa ayar shafaffiya
ce sun kafa hujja da
cewa: akwai ayar da ta
shafe ta inda ALLAH
(SWT) Yace: "Duk
wanda ya kasance
mazaunin gida acikin
watan daga cikinku to
ya azumce shi"
.
(Surah ta 2 aya ta 185)
.
Imam Bukhari acikin
littafinsa, Sahih Al-
Bukhari a babin KITAB
ATTAFSIR yabi ra'ayin
Abdullahi Dan Abbas
(RA) ne wajen kawar da
cewa an shafe wannan
ayar.
.
Magana mafi rinjaye
wannan ayah an
shafeta ga ma'ana:
Hukuncinta dai ya
tabbata akan tsofaffi
masu manyan shekaru,
idan baza su iya yin
azumi ba, da kuma
mata masu ciki da
masu shayarwa, idan
suka ji tsoro akan
'ya'yansu sai suci abinci,
kuma su ciyar da abincin
miskini a kullum.
.
(Ibn Jarud 381, Baihaqi
4/230, Abu-dawud
2318)
.
••WADANDA CIYARWA
KO RAMAKON AZUMI YA
WAJABA AKANSU:
.
1• Matafiyi.
2• Marar lafiya.
3• Tsoffi.
4• Mace mai ciki ko mai
shayarwa.
.
Mu lura cewa matuqar
mutum zai iya rama
azumin to ramawar shi
yafi alkhayri agare sa.
Shi ciyarwa idan mutum
bazai iya yin azumi bane
aka masa rangwame da
ya ciyar. ALLAH shine
mafi sani.
.
ALLAH YA AMSA MANA
IBADUNMU (Ameen)
.
-Faridah Bintu Salis
(Bintus-sunnah)

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s