MARABA DA WATAN RAMADA N •••••••••••• •••••••• [16]

MARABA DA WATAN
RAMADAN
.
•••••••••••••••••••••
[16]•••••••••••••••••••
.
FALALAR KWANA GOMA
(10) NA QARSHEN
WATAN RAMADAN !!!
.
Kwanakin watan
Ramadan dukkansu
akwai falala acikinsu,
sai dai mafi falalarsu
sune kwanaki 10 na
qarshe. Saboda ayoyin
Alqur'ani da Hadithai
ingantattu sun zo da
bayanin falalarsu. Daga
cikin falalar wadannan
kwanaki akwai:-
.
1• Acikinsu ne ake
dacewa da daren
Lailatul Qadr, ba a
nemansa acikin sauran
kwanaki face acikin
kwana 10 na qarshen
Ramadan, saboda
Hadithin Aisha (RA)
tace:
.
Manzon ALLAH (SAW)
Yace: "Ku nemi Lailatul
Qadr acikin marar
kwanaki 10 na qarshen
watan Ramadan"
.
(Bukhari 4/225, Muslim
1169)
.
2• Lallai Manzon ALLAH
(SAW) Ya himmantu
kuma ya kula sosai da
wadannan kwanaki 10
na qarshen watan
Ramadan, saboda idan
suka zo Manzon ALLAH
(SAW) Yana daura
gyautonsa (damara) ya
dage da ibada ya nisanci
iyalansa, yayi ta
ayyukan alkhayri da
Da'a zuwa ga
Ubangijinsa a
Masallacinsa.
.
Aisha (RA) tace:
"Manzon ALLAH (SAW)
Ya kasance yana
yawaita qoqarin ibada a
kwanaki 10 na qarshen
Ramadan, irin qoqarin da
baya yin irinsa a
kwanakin da ba
wadannan ba"
.
(Muslim 1174)
.
3• Yana daga Falalarsa
cewa duk wanda ALLAH
(SWT) Ya azurta da
tsayuwa acikinsa, wato
sallolin dare da raya
daren ta hanyar bautar
ALLAH dayi masa Da'a,
to ALLAH Ya yafe masa
duk abunda ya gabatar
na zunubansa da ya
aikata, kamar yadda
yazo a Hadith:
.
Manzon ALLAH (SAW)
Yace: "Wanda duk yayi
tsayuwar daren Lailatul
Qadr yana mai imani da
ALLAH da kuma neman
ladar Ubangiji to an
gafarta masa abunda
ya gabatar na zunubai"
.
(Bukhari 4/217, Muslim
759)
.
4• Yana daga falalar
wadannan Kwanaki 10
cewa i'itikafi baya
kasancewa sai acikinsu,
kamar Yadda Hadithin
Aisha (RA) yazo, tace:
.
"Lallai Manzon ALLAH
(SAW) Ya kasance yana
yin i'itikafi a kwanaki 10
na qarshen watan
Ramadan, kuma haka
Manzon ALLAH (SAW)
Yake yi har ALLAH Ya
kar6i rayuwarsa"
.
(Bukhari 4/226, Muslim
1173)
.
Ya ALLAH ka bamu
dacewa ka sanya mu
daga cikin salihan
bayinka masu tsayuwa
akan bautarka da
addininka (Ameen)
.
YA ALLAH KA AMSA
IBADUNMU (Ameen).
.
-Faridah Bintu Salis.
(Bintus-sunnah)

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out / Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out / Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out / Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out / Change )

Connecting to %s