MARABA DA WATAN RAMADA N •••••••••••• •••••••• [17]

MARABA DA WATAN
RAMADAN
.
•••••••••••••••••••••
[17]•••••••••••••••••••
.
I'ITIKAFI DA HUKUNCE-
HUKUNCENSA …[1]
.
•I'ITIKAFI: malamai
sunyi bayanin ma'anar
i'itikafi cewa shine
tsayuwa akan wani
abu, ta wannan ma'anar
ne ake cewa wanda ya
zauna masallaci yana
ibada acikinsa, wanda
ya ke6e domin bautar
ALLAH (SWT).
.
•••HIKIMAR YIN
I'ITIKAFI•••
.
Haqiqa ALLAH (SWT) Ya
shar'antawa bayinsa yin
i'itikafi, wanda manufar
hakan ita ce komawar
zuciya ga ALLAH (SWT)
domin neman kusanci
da neman yardarSa,
Kuma ALLAH ne ke
debewa mai i'itikafi
kewa a lokacin da ya
nisanci mutanen dake
debe masa kewa domin
zai ke6antu ne da
ambaton ALLAH, kuma
haqiqa ALLAH yana son
masu ambatonsa.
.
•••ZAMAN I'ITIKAFI•••
.
ALLAH (SWT) Yace:
"Kada ku yi mubashara
(hada jiki) da mata alhali
kuna masu yin i'itikafi a
masallatai"
.
(Surah ta 2 aya ta 187)
.
I'itikafi abun so ne,
wato (Mustahabbi ne) a
watan Ramadan da
wanin watan Ramadan.
Domin ya tabbata cewa:
.
Manzon ALLAH (SAW)
Yayi i'itikafin kwanaki 10
na qarshen watan
Shawwal"
.
(Bukhari 4/226, Muslim
1173)
.
Kuma Ya tabbata cewa
Umar Dan Khattab (RA)
yace wa Manzon ALLAH
(SAW): "Ya Manzon
ALLAH (SAW) lallai ni a
lokacin jahiliyya nayi
alwashin yin i'itikafin
dare daya acikin
masallacin makkah. Sai
Manzon ALLAH (SAW)
yace wa Umar (RA) to
sai ka cika alwashin da
kayi, domin haka sai
Umar (RA) yaje Makkah
yayi i'itikafin dare daya
a masallaci mai
alfarma" .
(Bukhari 4/237, Muslim
1656).
.
Amma mafificiyar
i'itikafi shine i'itikafin
watan Ramadan,
saboda Hadithin Abu-
Hurayrah (RA) da yace:
.
Manzon ALLAH (SAW)
Ya kasance yana yin
i'itikafi na kwanaki 10
acikin ko wane watan
Ramadan, amma yayi
i'itikafi na kwana 20 a
shekararsa ta qarshe
wanda ALLAH (SWT) Ya
kar6i rayuwarsa
acikinta"
.
(Bukhari 4/225)
.
Aisha (RA) tace: Manzon
ALLAH (SAW) Ya
kasance yana i'itikafi a
kwanaki 10 na qarshen
watan Ramadan har
ALLAH Ya kar6i
rayuwarsa"
.
(Bukhari 4/226, Muslim
1173).
.
ALLAH YA BAMU IKO,
YA KUMA AMSA MANA
IBADUNMU (Ameen)
.
-Faridah Bintu Salis.
(Bintus-sunnah)

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s