MARABA DA WATAN RAMADA N •••••••••••• •••••••• [18]

MARABA DA WATAN
RAMADAN
.
•••••••••••••••••••••
[18]•••••••••••••••••••
.
I'ITIKAFI DA HUKUNCE-
HUKUNCENSA …[2]
.
•••SHARUDAN
I'ITIKAFI•••
.
1• MASALLATAI: Yin
i'itikafi baya inganta sai
acikin masallatai.
Saboda ALLAH (SWT)
Yace: "Kada ku yi
mubashara da mata
alhali kuna masu i'itikafi
acikin masallatai"
.
(surah ta 2 aya ta 187)
.
Amma ba kowane
masallaci ake i'itikafi
acikinsa ba, domin yazo
acikin Hadith cewa:
"Babu i'itikafi (cikakke)
sai a masallatai uku"
wato Masallacin
Makkah, Masallacin
Qudus da Masallacin
Madina" (Hadith ne
ingantacce malamai sun
inganta shi)
.
Amma wannan Hadith
ba yana kore yin i'itikafi
bane acikin wanin
wadannan masallatai
bane, sai dai yana kore
cikar ladar i'itikafi a wani
masallacin na daban.
.
2• MUSULUNCI: sharadi
ne mai i'itikafi ya
kasance musulmi domin
ba'a kar6an i'itikafin
Kafiri.
.
3• HANKALI: Dole ne mai
i'itikafi ya zamo mai
hankali domin ba a
kar6ar ibadar Mahaukaci.
.
4• BALAGA: Wanda zai yi
i'itikafi ya zamanto
mutum ne wanda
hukunce-hukuncen
addinin musulunci ke
gudana akansa, kuma
masani akan addini
kuma masani akan
i'itikafi da mas'alolinsa.
.
5• NIYYA: Dole ne mai
i'itikafi zai tsarkake
Niyyarsa domin ALLAH
(SWT) Ya zamanto ba
domin Riya ba.
.
••• ABUBUWANDA SUKA
HALATTA GA MAI
I'ITIKAFI •••
.
1• Ya halatta ga mai
'i'itikafi ya fita daga
masallaci saboda wata
buqata ta shari'ah.
Saboda Aisha (RA) tace:
.
"Manzon ALLAH (SAW)
Ya kasance yana shigar
da kansa gare ni yana
i'itikafi a masallaci ina
cikin dakina, na taje
masa shi, a wata
Riwayar kuma "In
wanke masa kansa"
kuma ya kasance a
lokacin i'itikafi baya
shiga cikin gida sai
domin wata buqata ta
dan adam"
.
(Bukhari 1/342, Muslim
297)
.
2• Ya Halatta ga mai
i'itikafi yayi alwala a
masallaci amma alwala
sassauqa, amma yin
hakan ya zama baya
kawo qazanta a
masallaci ko cutarwa ga
jama'a. Hadith Yazo
cewa: "Manzon ALLAH
(SAW) Yayi alwala
sassauqa a masallaci"
.
(Ahmad 5/364)
.
3• Mai i'itikafi yana da
damar sanya
shimfidarsa a masallaci,
dominan samu daga
Hadith, Manzon ALLAH
(SAW) Ya kasance idan
zai shiga i'itikafi ana kai
masa shimfidarsa a
masallaci, a bayan wani
ginshiqi daga cikin
ginshiqan masallaci"
.
(Ibn Majah 642)
.
4• Fita daga cikin
Masallaci zuwa wurin
wanka amma idan babu
wurin wanka a
masallacin, to mai
i'itikafi yana da damar
zuwa duk yake domin
yin wanka saboda lalura
ce. Saboda Hadithin
Aisha (RA) tace:
"Manzon ALLAH (SAW)
Ya kasance baya zuwa
gida idan yana i'itikafi
sai domin wata buqatar
dan adam"
.
(Bukhari 1/342, Muslim
297)
.
ALLAH YA AMSA MANA
IBADUNMU (Ameen)
.
-Faridah Bintu Salis.
(Bintus-sunnah)

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s