MARABA DA WATAN RAMADA N •••••••••••• •••••••• [19]

MARABA DA WATAN
RAMADAN
.
•••••••••••••••••••••
[19]•••••••••••••••••••
.
I'ITIKAFI DA HUKUNCE-
HUKUNCENSA …[3]
.
••• ABUBUWANDA BAYA
HALATTA GA MAI
I'ITIKAFI •••
.
1• JIMA'I: Yin jima'i da
sumbatar mace da
wasa da ita baya
halatta ga mai i'itikafi
da dare ko da rana, idan
kuma har hakan ya faru
to i'itikafin ya 6aci,
saboda hani akan
wannan yazo cikin
alqur'ani mai girma,
ALLAH (SWT) Yana
cewa: "kada kuyi
mubashara da mata
alhali kuna masu i'itikafi
acikin masallatai"
.
(Surah ta 2 aya ta 187)
.
2• FITA DOMIN GANIN
MARAR LAFIYA: Ba ya
halatta ga mai i'itikafi
ya fita zuwa ganin
marar lafiya a gida ko a
asibiti.
.
3• JANA'IZA: Ba ya
halatta ga mai i'itikafi
ya halarci sallar gawa
sai dai idan sallar gawar
ta kasance acikin
masallacin da yake
i'itikafi ne to zai iya yin
sallar gawar tare da
Liman. Kar ya fita sai
fitar da bata da
makawa, saboda Aisha
(RA) tace:
.
"Abunda yake sunnah
ga mai i'itikafi kar ya
gaida marar lafiya, kar
ya halarci jana'iza (sallar
gawa) kar yayi jima'i da
mace, kuma kar ya
shafeta shafar jin dadi"
.
(Abu-dawud ya fitar
dashi)
.
4• YASASHSHIYAR
MAGANA: Baya halatta
ga mai i'itikafi ya
shagaltu da wasa da
yasassun maganganu a
lokacin ibadarsa da ko
wane lokaci, saboda
Nassin AlQur'ani yayi
hani akan wadannan
abubuwa, kuma babu
fa'ida ta duniya ko ta
lahira acikinsu.
.
5• GIBA DA
ANNAMIMANCI: Yin giba
da yawo da
Annamimanci da
sauransu basa halatta
ga mai i'itikafi, saboda
Giba da Annamimanci
Dabi'u ne wadanda
ALLAH (SWT) da
Manzon ALLAH (SAW)
suka haramta, kamar
yadda yazo acikin
alqur'ani:
.
(Surah ta 49 aya ta 12
da kuma Surah ta 68
aya ta 10 zuwa ta 11).
.
•••LOKUTAN YIN
I'ITIKAFI•••
.
Malamai sunyi sa6ani
game da mafi qarancin
lokacin yin i'itikafi.
Amma Mafi Yawan
malamai sun tafi akan
cewa mafi qarancin
i'itikafi shine dare da
yini, dalilinsu shine
Hadithin Umar (RA)
wanda ya gabata.
.
•••JAN HANKALI•••
.
Mutanen mu na wannan
zamanin basa bawa
i'itikafi muhimmanci da
yawa daga cikinsu suna
tafiya masallatai da
sunan i'itikafi amma sai
suje suyita qiran
mutanen su a wayoyi
alhali suna ikirarin suna
i'itikafi wannan ba daidai
bane yin hakan
wulaqanta bautar
ALLAH (SWT) ne.
.
Da wannan nake jan
hankali al'ummar
musulmai idan zasu yi
i'itikafi su tsarkake
Niyyar su, su gabatar
dashi domin ALLAH ba
tare da sanya wasa
acikinsa ba.
.
ALLAH YASA MU DACE,
ALLAH YA AMSA MANA
IBADUNMU (Ameen)
.
-Faridah Bintu Salis.
(Bintus-sunnah)

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s