MARABA DA WATAN RAMADAN •••••••••••••••• [20]

MARABA DA WATAN
RAMADAN
.
•••••••••••••••••••••
[20]•••••••••••••••••••
.
•••• LAILATUL QADR •••
.
•LAILATUL QADR: shine
Qaddararren dare, dare
mai daraja mai girma,
daren alkhayri, dare mai
albarka, dare ne wanda
misali bazai gama
rarrabe abunda wannan
dare ya qunsa ba face
ALLAH (SWT) shine
masani.
.
•••FALALAR DAREN
LAILATUL QADR•••
.
Falalar wannan dare mai
girma ce domin an
shedar da sauqar
al'qur'ani acikinsa, kuma
ALLAH (SWT) Ya
ambace sa acikin
LittafinSa a wurare
daban-daban, daga
cikinsu akwai fadar
ALLAH (SWT):
.
"lallai mu muka sauqar
da shi (Alqur'ani) acikin
daren Lailatul Qadr, me
ya sanar da kai abunda
ake qira Lailatul Qadr,
Daren Lailatul qadr yafi
daraja akan wata dubu,
saboda mala'iku suna
sauqa acikinsa tare da
ruhu (jibril) da izinin
Ubangijinsu ga kowane
al'amari, Amincin ALLAH
ne wannan daren (da
abinda ke cikinsa) har
6ullowar alfijir"
.
(Surah ta 97 aya ta 1
zuwa 5)
.
Haqiqa daukakar daraja
ta isa ga wannan dare
na Lailatul Qadr acikin
wadannan ayoyi cewa
yafi watanni dubu, Haka
kuma sauqar mala'iku
acikinsa har da Mala'ika
Jibrilu (AS) wata falala
ce ta wannan daren.
.
Kuma lalla akwai daga
falalar wannan dare
cewa acikinsa ne ake
rarrabe dukkanin
al'amura abin
hukuntawa.
.
ALLAH (SWT) Yace:
"Lallai ne mu mun
sauqar da alqur'ani a
cikin dare mai albarka,
lallai Mu masu gargadi
ne, acikinsa ne ake
rarraba dukkanin al0ura
abin hukuntawa"
.
(Surah ta 44 aya ta 3
zuwa 6)
.
•••LOKUTAN DA AKE
SAMUN DAREN
LAILATUL QADR•••
.
Annabi (SAW) yace: shi
wannan dare, ana
samunsa a daren 21, da
daren 23, da daren 25,
da daren 27 da daren 29
da daren qarshe na
watan Ramadan.
.
Dan Umar (RA) Yace:
wasu mutane daga
sahabban Annabi (SAW)
an nuna musu daren
Lailatul Qadar acikin
barci, acikin kwana
bakwai na qarshen
watan Ramadan, sai
Manzon ALLAH (SAW)
Yace: "Ina zaton cewa
mafarkinku ta dace da
kwana bakwan qarshe,
saboda haka wanda ya
kasance zai nemi ta to
ya neme ta acikin
kwana bakwai na
qarshen watan
Ramadan"
.
(Muttafaqun Alaihi)
.
Mu'awiyya Dan Abu-
sufyan (RA) Yace:
Manzon ALLAH (SAW)
Yace: acikin (Lokacin
ganin) Lailatul Qadari:
"Daren 27 ne" Abu-
Dawud ya ruwaito shi,
kuma zance mafi
rinjaye Hadith ne
mauqufi. Kuma lallai
(Malamai) sunyi sa6ani
acikin ayyana
takamammen daren a
bisa zantuka arba'in.
.
Aisha (RA) tace:
"Manzon ALLAH (SAW)
Ya kasance yana
maqwabtakar masallaci
a kwana goma na
qarshen Watan
Ramadan, Yana cewa ku
nemi daren Lailatul Qadr
a kwana Goma na
qarshen watan
Ramadan "
.
(Bukhari 4 /225, Muslim
1169)
.
Ibn Hajar Yace: Bayan
jeranta bayani akanta
(Lailatul Qadr) mafi
rinjayen zance shine
tana cikin marra ta
Goman qarshe, kuma ita
tana cancanjawa ne.
.
To wadannan sune
Lokutan da ake samun
Daren Lailatul Qadr.
.
••• ALAMAR DAREN
LAILATUL QADR •••
.
Manzon ALLAH (SAW)
Ya siffanta daren
Lailatul Qadr cikin
abunda Dan Abbas (RA)
Ya ruwaito cewa:
.
Manzon ALLAH (SAW)
Yace: "Daren Lailatul
Qadr dare ne mai sauqi
wanda yake a sake, ba
mai zafi bane kuma ba
mai sanyi ba ne, rana
tana wayuwar gari tana
mai rauni (Marar zafi)
mai launin ja"
.
(Ibn Khuzaimah 3/231).
.
•••NEMAN DACEWA DA
"DAREN LAILATUL
QADR"•••
.
Musulmi yana neman
dacewa da wannan
Dare mai albarka ta
hanyoyi kamar haka:
.
1• Tsayuwa da Da'a ga
ALLAH yana mai imani
da kuma kwadayin ladar
Ubangijinsa.
.
Manzon ALLAH (SAW)
Yace: "Wanda duk yayi
tsayuwar daren Lailatul
Qadr yana mai imani da
ALLAH da kuma neman
ladar Ubangiji to an
gafarta masa abunda
ya gabatar na zunubai"
.
(Bukhari 4/217, Muslim
759)
.
2• Musulmi kan iya
neman dacewa da
wannan dare ta hanyar
yawaita addu'a.
Aisha (RA) tace: "Ya
Manzon ALLAH shin ko
kana ganin idan na gane
wani dare ne Lailatu
Qadr me zance acikinsa?
Sai yace kice: .
ALLAHUMMA INNAKA
AFUWWUN TUHIBBUL
AFWA FA'AFU ANNIY"
.
Ma'ana: "Ya ALLAH Lallai
Kai mai yafewa ne
kuma kana son yafewa
to ina roqonka ka yafe
min"
.
(Tirmizi 3760, Ibn Majah
3850)
.
3• Raya kwana 10 na
qarshen Watan
Ramadan da ibada, da
kuma nisantar
abubuwan sha'awa da
yawaita ayyukan Da'a
zuwa ga ALLAH (SWT).
.
Aisha (RA) tace: Manzon
ALLAH (SAW) Ya
kasance yana yawaita
qoqarin ibada a kwana
10 na qarshen Watan
Ramadan, irin qoqarin da
baya yin irinsa a
kwanakin da ba
wadannan ba"
.
(Muslim 1174)
.
4• Yawaita ambaton
ALLAH irin wanda aka
samo daga Manzon
ALLAH (SAW) da kuma
yawaita karatun
Alqur'ani mai Girma da
Haddarsa, da kuma
qiran mutane zuwa ga
ayyukan alkhayri, dayi
musu hani akan
mummuna.
.
YA ALLAH KA BAMU
DACEWA DA DAREN
LAILATUL QADR KUMA
KA AMSA MANA
IBADUNMU. (Ameen)
.
-Faridah Bintu Salis.
(Bintu-sunnah)

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s