FATAWOYIN LAYYA2(Sheikh Abdulwahhab Abdullah)

A wannan
darasi za mu
amsa
tambayoyi
kamar haka;
*Tambaya:
Mene ne
sharuddan
layya?
AMSA:
Yana daga cikin
sharuddan
layya:
abin da za a
yanka, lallai ya
kasance daga
cikin “bahimatul
anʿām” (dabbobin
ni’ima), irin su:
rakuma da
shanu da awaki
da
tumaki). Domin
haka, ba ya
cikin
sharuddan
layya, a yi ta da
namun
daji, kuma ba
za a yanka kaji
da
sauran
tsuntsaye ba,
kamar yadda
wasu daga
cikin ‘yan
Zahiriyyah
suka tafi a kai.
Dalili kuwa
fadin
Ubangiji
subhanahu wa
ta’ala
cewa:
ﻭﻟﻜﻞ ﺃﻣﺔ ﺟﻌﻠﻨﺎ
ﻣﻨﺴﻜﺎ ﻟﻴﺬﻛﺮﻭﺍ
ﺍﺳﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﻣﺎ
ﺭﺯﻗﻬﻢ ﻣﻦ ﺑﻬﻴﻤﺔ
ﺍﻟﺄﻧﻌﺎﻡ )34 ( …
ﺍﻟﺤﺞ: ٣٤
Ma’ana:
Kowacce
al’umma mun
sanya
musu ibadunsu,
domin su
ambaci
sunan Allah a
bisa abin da
(Allah)
ya arzuta su da
shi daga cikin
dabbobin
ni’ima…
Wannan aya ta
nuna cewa,
Ubangiji
subhanahu wa
ta’ala ya
ambaci
dabbobin ni’ima
ne, kuma
ya nuna cewa
lallai ne idan za
a
yanka su, a
ambaci
sunansa.
Amma ayar ba
ta ambaci
cewa ana
iya layya da
namun daji ba,
ko
tsuntsaye,
kamar kaji da
sauransu.
Kuma koda a
cikin dabbobin
ni’ima
din ba a
yankawa sai
wacce ta cika
wadannan
sharuddan:
1- Shanu: Sai
sun cika
shekara
biyu zuwa
sama.
2-Raquma: Sai
sun cika
shekara
biyar zuwa
sama.
3-Tumaki da
Awaki: Sai sun
cika
shekara daya
zuwa sama. Sai
dai
idan ya
ta’azzara ba a
samu
shekararriya
ba, to babu laifi
a
yanka wacce
ba ta shekara
ba
amma ta kusa
cika shekara a
cikin
raguna ko
awaki (watau
jaz’a),
saboda hadisin
da aka karbo
daga
Jabir Ibn
Abdullah
radhiyallahu
anhuma ya ce:
Manzon Allah
sallallahu alaihi
wa sallama ya
ce:
ﻟﺎ ﺗﺬﺑﺤﻮﺍ ﺇﻟﺎ
ﻣﺴﻨﺔ ﺇﻟﺎ ﺃﻥ
ﻳﻌﺴﺮ ﻋﻠﻴﻜﻢ
ﻓﺘﺬﺑﺤﻮﺍ
ﺟﺬﻋﺔ ﻣﻦ ﺍﻟﻀﺄﻥ.
Ma’ana:
Kada ku yanka
sai
shekararriya,
sai dai idan ya
gagareku , sai
ku
yanka wacce
ake kira jaz’a
daga
raguna.
Haka kuma,
ana so dabbar
da za a
yi layya da ita
ta kasance
kubutacciya
daga aibu.
Saboda
hadisin da aka
karbo daga
Bara’u
Ibn Azib
radhiyallahu
anhuma ya
ce: Manzon
Allah sallallahu
alaihi
wa sallama ya
ce:
ﻻ ﻳﻀﺤﻰ ﺑﺎﻟﻌﺮﺟﺎﺀ
ﺑﻴﻦ ﻇﻠﻌﻬﺎ ﻭﻻ
ﺑﺎﻟﻌﻮﺭﺍﺀ ﺑﻴﻦ
ﻋﻮﺭﻫﺎ ﻭﻻ
ﺑﺎﻟﻤﺮﻳﻀﺔ ﺑﻴﻦ
ﻣﺮﺿﻬﺎ ﻭﻻ
ﺑﺎﻟﻌﺠﻔﺎﺀ
ﺍﻟﺘﻲ ﻻ ﺗﻨﻘﻲ
Ma’ana:
Ba a yanka
ramammiya
wacce
ramarta ta
bayyana, ko
gurguwa
wacce
gurguntakarta
ta bayyana,
ko mara lafiyar
da rashin
lafiyarta
ta bayyana, Ko
me ido daya.
Banda
wadannan
siffofi na
dabbobi, akwai
wasu siffofin.
saidai
hadisan ba su
inganta ba, don
haka ba mu
kawo su a nan
ba.
Kuma lallai ne
abinda za a
yanka
na layya, ya
kasance
mallakarsa
aka yi ta
hanyar halal, ba
ta hanyar
haram ba.
Wato wajibi ne
ya
kasance ba na
sata ko kwace
ba
ne, kuma ba
dabbar da aka
bayar
jingina ko
amana ba ce.
Kuma ya
kamata mai yin
layya ya
sani cewa ba
cewa aka yi ya
yi
azumi ko rikon
baki ba. Domin
haka, ba a hana
shi ci ko shan
abin
sha ba
matukar yana
bukata.
*Tambaya:
Yaushe ya
kamata a
yanka abin
layya?
AMSA:
Jumhurun
malamai sun
tafi a kan
cewa, ana
yanka abin
layya ne,
bayan sallar idi
ko da liman bai
yanka ba.
Dalilinsu kuwa
shi ne
fadin Manzon
Allah sallallahu
alaihi
wa sallama
cewa:
ﻣﻦ ﻛﺎﻥ ﺫﺑﺢ
ﺃﺿﺤﻴﺘﻪ ﻗﺒﻞ ﺃﻥ
ﻳﺼﻠﻲ ﺃﻭ ﻧﺼﻠﻲ
ﻓﻠﻴﺬﺑﺢ ﻣﻜﺎﻧﻬﺎ
ﺃﺧﺮﻯ ﻭﻣﻦ ﻛﺎﻥ
ﻟﻢ ﻳﺬﺑﺢ ﻓﻠﻴﺬﺑﺢ
ﺑﺎﺳﻢ ﺍﻟﻠﻪ .
Ma’ana:
Wanda ya
yanka abin
layyarsa
kafin sallarmu,
to, ya sake
yanka
wata dabbar
maimakonta
bayan
sallar idi,
wanda kuma
bai yanka
ba (sai bayan
sallarmu), to,
ya
yanka da sunan
Allah.
Saidai kuma
Imam Mālik ya
tafi a
kan sabanin
abinda jamhur
suka
tafi akai inda
ya ke cewa:
Ba a yanka abin
layya sai bayan
liman ya yanka
nasa.
Dalilinsa kuwa
shi ne, hadisin
da
aka karbo daga
Jabir Ibn
Abdullah
radhiyallahu
anhu ya ce,
ﺻﻠﻰ ﺑﻨﺎ ﺍﻟﻨﺒﻲ
ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ
ﻭﺳﻠﻢ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻨﺤﺮ
ﺑﺎﻟﻤﺪﻳﻨﺔ ﻓﺘﻘﺪﻡ
ﺭﺟﺎﻝ ﻓﻨﺤﺮﻭﺍ
ﻭﻇﻨﻮﺍ ﺃﻥ ﺍﻟﻨﺒﻲ
ﺻﻠﻰ
ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻗﺪ
ﻧﺤﺮ ﻓﺄﻣﺮ ﺍﻟﻨﺒﻲ
ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ
ﻭﺳﻠﻢ ﻣﻦ ﻛﺎﻥ
ﻧﺤﺮ ﻗﺒﻠﻪ ﺃﻥ ﻳﻌﻴﺪ
ﺑﻨﺤﺮ ﺁﺧﺮ ﻭﻟﺎ
ﻳﻨﺤﺮﻭﺍ ﺣﺘﻰ ﻳﻨﺤﺮ
ﺍﻟﻨﺒﻲ. ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ
ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ
Ma’ana:
Mun yi salla
tare da Manzon
Allah
sallallahu alaihi
wa sallama a
Madina ranar
babbar salla,
sai
wasu mazaje
suka je suka yi
yanka, suna
tsammani
Manzon
Allah sallallahu
alaihi wa
sallama
ya yi yanka, sai
Manzon Allah
sallallahu alaihi
wa sallama ya
ce:
duk wanda ya
yi yanka kafin
na yi,
to ya sake
yankansa. Ya
kara da
cewa: Kada su
yanka har sai
Annabi
sallallahu alaihi
wa sallama
ya yanka.
Wannan shi ne
zance mafi
rinjaye
domin wannan
hadisin da
Imam
Malik ya kafa
hujja da shi ya
fada
karara cewar
ba’a yanka sai
bayan
liman yayi
yankan sa,
sabanin
dalilin jamhur.
Don haka sai
mutum ya
hakura har
liman ya
yanka. Idan
kuma mutum
yana
nesa da gari ne,
sai ya kintaci
lokacin da ya
kamata a ce
liman ya
yanka dabbar
layyarsa, sai ya
yanka tasa.
Wanda kuma
ya yanka
kafin salla, to
namansa ba na
layya
ba ne, ya zama
naman miya
kenan, ko ya
sani ko bai sani
ba.
Saboda haka
sai ya sake
yanka
wata
maimakonta.
Dalili kuwa shi
ne: wani sahabi
Uwaīmir Ibn
Ashkar
radhiyallahu
anhum ya taba
yanka dabbar
layyarsa kafin
sallar īdī, sai
Manzon Allah
sallallahu alaihi
wa
sallama ya ce:
ﺃﻋﺪ ﺃﺿﺤﻴﺘﻚ .
Ma’ana:
Ka sake yanka
wata a
maimakonta.
A nan Annabi
sallallahu alaihi
wa
sallam bai
tambaye shi ko
ya sani,
ko bai sani ba.
Wallahu a’alam!
*Tambaya:
A ina ya
kamata liman
ya yanka
abin layyarsa a
sunnance?
AMSA:
A bisa koyarwa
irin ta Manzon
Allah sallallahu
alaihi wa
sallama
liman zai yanka
abin layyarsa
ne a
filin idi, domin
al’umma su
shaida,
kuma su sami
damar yin ta su
layyar, ba tare
da wani
kokwanto
ba. Dalili kuwa
shi ne hadisin
Jabir
radhiyallahu
anhum ya ce:
ﺷﻬﺪﺕ ﻣﻊ ﺭﺳﻮﻝ
ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ
ﻭﺳﻠﻢ
ﺍﻷﺿﺤﻰ ﺑﺎﻟﻤﺼﻠﻰ
ﻓﻠﻤﺎ ﻗﻀﻰ ﺧﻄﺒﺘﻪ
ﻧﺰﻝ ﻣﻦ
ﻣﻨﺒﺮﻩ ﻭﺃﺗﻲ
ﺑﻜﺒﺶ ﻓﺬﺑﺤﻪ
ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ
ﺍﻟﻠﻪ
ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺑﻴﺪﻩ .
Ma’ana:
Na halarci idin
babbar salla
tare da
Manzon Allah
sallallahu alaihi
wa
sallama. Bayan
ya gama
hudubarsa, sai
ya sauka daga
kan
minbarinsa, aka
kawo masa
ragon
layyarsa, sai ya
yanka shi da
hannunsa (mai
albarka).
Haka kuma an
karbo wani
hadisin
daga Abdullahi
Ibn Umar
radhiyallahu
anhum ya ce:
ﺃﻥ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ
ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻛﺎﻥ
ﻳﺬﺑﺢ ﺃﺿﺤﻴﺘﻪ
ﺑﺎﻟﻤﺼﻠﻰ ﻭﻛﺎﻥ
ﺍﺑﻦ ﻋﻤﺮ ﻳﻔﻌﻠﻪ.
Ma’ana:
Hakika Manzon
Allah sallallahu
alaihi wa
sallama ya
kasance yana
yanka abin
layyarsa a filin
idi.
Saboda haka ni
ma na kasance
ina
aikata hakan.
Don haka sai
limamai su yi
koyi.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s