FARKON SHIGA ALJANNAH (SAWW).

FARKON SHIGA
ALJANNAH (SAWW).
*************
*************
******
Farkon wanda zai shiga
Aljannah aranar
Alqiyamah shine
Annabinmu
Muhammadu (saww)
kamar yadda Imamu
Muslim ya ruwaito daga
Sayyiduna Anas bn Malik
(rta) yace Manzon Allah
(saww) yace:
"ZAN ZO KOFAR
ALJANNAH ARANAR
ALQIYAMAH, SAI IN
KWANKWASA, SAI MAI
TSARONTA (WATO
MALA'IKA RIDHWAN)
YACE : "KAI WANENE?".
ZAN CE MASA
"MUHAMMADU NE". SAI
YACE : "SABODA KAI
AKA UMURCENI KAR IN
BUDE MA WANI KAFIN
KA".
Acikin wata ruwayar
kuma yace: "NINE NAFI
DUKKAN ANNABAWA
YAWAN MABIYA, KUMA
NINE FARKON WANDA
ZAI KWANKWASA
(KOFAR ALJANNAH)."
(Muslim ne ya
ruwaitoshi).
Acikin ruwayar Abu
Hurairah kuma Annabi
(saww) yace: "MUNE NA
KARSHE KUMA MUNE NA
FARKO ARANAR
ALKIYAMAH. KUMA
MUNE FARKON
WADANDA ZASU SHIGA
ALJANNAH".
(Bukhariy da Muslim ne
suka ruwaitoshi).
Akwai kuma hadisan da
suka nuna cewar
Talakawan wannan
al'ummar sai sun riga
mawadata (Masu kudi)
shiga Aljannah, kamar
yadda Imamu Ahmad
da Tirmidhiy suka
ruwaito Daga Sayyiduna
Abu Hurairah (ra) yace
Manzon Allah (saww)
yace:
"TALAKAWAN
MUSULMAI ZASU RIGA
SHIGA ALJANNAH KAFIN
MAWADATANSU DA
TSAWON RABIN WUNI
GUDA, WATO SHEKARU
DARI BIYAR KENAN (500
years).
Imamu Muslim kuma ya
ruwaito daga Sayyiduna
Abdullahi bn Amru bn
Al-Aas (ra) yace
Manzon Allah (saww)
yace:
"TALAKAWA DAGA
CIKIN SAHABBAN DA
SUKAYI HIJIRA, ZASU
RIGA MAWADATANSU
SHIGA ALJANNAH
ARANAR ALKIYAMAH
DA TSAWON SHEKARU
ARBA'IN".
(Muslim ne ya
ruwaitoshi).
Don haka ya kai 'dan
uwa, Kada wadata tasa
ka rika yin Girman kai ko
Alfahari. Domin girman
kai babu inda zai kaika
sai wuta. Kuma koda ka
tsaya ka bi Allah, sai
Talakawa sun rigaka
shiga Aljannah kamar
yadda Sahihan hadisan
nan suka tabbatar.
Ba wani abu ne zai
kawo maka wannan
jinkirin shiga Aljannar
ba, illa hisabin dukiyarka
da za'ayi ma. Domin ba
zaka gushe daga gaban
Zatin Allah ba, sai an
tambayeka akan
kowanne kwabo da Sisi
da Naira da dollars : Ta
ina ka sameta? Kuma ta
ina ka 'batar da ita?.
Acikin bin Allah, ko
kuma bin sha'awar son
zuciyarka?
Shi kuwa Talaka bashi
da komai sai ransa. Don
haka babu abin
tambaya sosai akansa.
Amma duk da haka ina
jan hankalin 'Yan uwana
Talakawa cewa mu
Zage damtse wajen
neman ilimi da bauta ma
Allah ta hanyoyin da
suka dace domin samun
babban rabo awajen
Allah. Kar mu sake
wasu sun fimu jin dadi
aduniya, kuma alahirar
ma su sha gabanmu.
Hakika mun gode ma
Allah da ya sanyamu
acikin wannan al'ummar
ta Annabi Muhammad
(saww). Allah yasa
muna daga cikin sahun
farkon wadanda zasu
shiga Aljannah aranar
Alqiyamah. Acikin
Makobtaka da
Masoyinmu (saww).
DAGA ZAUREN FIQHU
WHATSAPP
(15-09-1437)
20-06-2016.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out / Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out / Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out / Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out / Change )

Connecting to %s